An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar wasu da dama sakamakon turmutsutsu a yayin wani taron rabon kuɗaɗen tallafi a garin Bama da ke jihar Borno.

Wasu bayanai sun bayyana cewa ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da UNICEF suka shirya rabon tallafin.

Shaidun gani da ido sun ce, turmutsitsin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 8:00 na safe a makarantar firamare ta Kasugula, daya daga cikin cibiyoyin bayar da tallafi da aka kebe a garin Bama.

Rahoton na nuni da cewar waɗanda suka ci gajiyar shirin sun taru ne domin karɓar tallafin kuɗi na naira 28,500 kowannensu.

Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas

Turmutsitsin ya faru ne a daidai lokacin da jama’a suka yi cincirundo a bakin  kofar makarantar, lamarin da ya haifar da turereniya.

 

Wani dan shekara 60 mazaunin Mazaɓar Bukar Tela, wanda lamarin ya ritsa da shi ya rasu ne a lokacin da aka isa babban asibitin garin Bama. Daga baya wasu mutane biyu da suka jikkata sun mutu yayin da ake jinya a asibiti.

Majiyar ta ce, waɗanda suka samu raunukan sun hada da mata da maza, kuma an tura karin sojoji wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya tare da saukaka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.

Daga bisani aka bayar da gawarwakin mamatan ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kungiyar ta ICRC_Africa ta ce ba ta da hannu a aikin rarraba kudaden a Bama wanda ya haifar da wannan turmutsitsin da ya kai ga asarar rayuka, kamar yadda aka gabatar a cikin rahoton farko.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Yadda Sarki da Gwamnonin Kano da Jigawa suka sauka a Madina domin jana’izar Dantata

Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da  Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Magajin Garin Birnin Tehran Ya Karyata Da’awar ‘Yan Sahayoniyya
  • Ba Gaskiya Ba Ne: Ɓarayi Ba Su Sace Ɗan Uwan Gwamnan Zamfara Ba
  • Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno
  • Dalibai 29 Suka Rasu A Turmutsitsin Tserewa Ga Fashewar Taransifoma A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
  • Hare-haren Isra’ila sun kashe mana mutum 935 a yaƙin kwana 12 — Iran
  • HOTUNA: Yadda Sarki da Gwamnonin Kano da Jigawa suka sauka a Madina domin jana’izar Dantata
  • HOTUNA: Yadda Sarki da Gwamnan Kano suka sauka a Madina domin jana’izar Dantata
  • Babbar Mota Ta Afka Cikin Kasuwa A Taraba, Mutane Da Yawa Sun Mutu
  • An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina
  • Kasar Sin Ta Sake Ware Yuan Miliyan 100 Domin Tallafawa Lardin Guizhou Dake Fama Da Ambaliya