Iran : Hare-haren da Isra’ila ta kai kan Yemen babban laifin yaki ne
Published: 18th, May 2025 GMT
Iran ta yi kakkausan suka game da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasar Yemen tana mai danganta su da babban laifin yaki.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kai wa kan ababen more rayuwa na tattalin arzikin kasar Yemen da kuma cibiyoyin jama’a sun zama “laifi na yaki da cin zarafin bil’adama.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar, Esmail Baghai ya yi kakkausar suka kan hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kaiwa kan manyan tashoshin jiragen ruwa na kasar Yemen.
Ya kara da cewa hare-haren da aka kai a tashar jiragen ruwa ta Hudaydah, Ras Issa da kuma Salif na kasar Yemen, ya zama babban cin zarafi ga dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Mista Baghai Ya kara da cewa gwamnatin Isra’ila tana kai irin wadannan hare-hare ne a daidai lokacin da al’ummar kasar Yamen ke fama da matsanancin hali na jin kai.
Kakakin ya jaddada cewa Amurka da Birtaniya da wasu kasashen yammacin duniya suna da hannu a ci gaba da aikata laifukan da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma ta’addancin da take yi kan kasashen musulmi a yankin.
Ya jaddada cewa goyon bayan da kasashen yammacin duniya ke baiwa Isra’ila, ya kara bai wa gwamnatin Isra’ilar karfin gwiwa wajen aiwatar da hare-haren wuce gona da iri da kisan kiyashin da take yi wa mata da kananan yara na Falastinawa wadanda ba su da kariya, kuma a halin yanzu ga al’ummar Yemen da ake zalunta.
Jami’in na Iran ya kuma soki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da yin shiru a kan hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke yi, Ya kara da cewa: Dole ne al’ummar musulmi su tashi tsaye wajen yakar zaluncin da gwamnatin ke yi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da gwamnatin Isra ila ke hare haren da kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Ya Bukaci A Tsige Netanyahu Daga Kan Fira Ministan Isra’ila
Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Fira ministan Netanyahu ya yi sakaci da rayuwar yahudawa a cikin aikinsa don haka hambarar da gwamnatinsa ita ce mafita
Tsohon Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya yi kira da a hambarar da Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa, yana mai zarginsa da yin sakaci wajen kubutar da fursunonin yahudawa da suke hannu ‘yan gwagwarmaya a Zirin Gaza.
Barak ya ce: Netanyahu yana sakaci da rayuwar fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Gaza domin faranta wa masu tsattsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai.” Ya bayyana shi a matsayin mai sakaci wajen gudanar da ayyukansa, da kuma ci gaba da kisan kiyashi a Zirin Gaza domin karecmanufofin siyasa saboda neman ci gaba da mulki.
A wata hira da yayi da tashar talabijin mai zaman kanta ta Isra’ila ta 12, Barak ya bayyana cewa: Netanyahu “yana sakaci da rayukan mutanen da ake tsare da su a Gaza domin farantawa masu tsatsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai. Don haka ya jaddada yin kira ga ‘yan adawa da su dauki matakin ruguza gwamnatin Netanyahu maimakon ceto shi.