Aminiya:
2025-09-18@00:41:50 GMT

Yadda aka kashe dan fashi aka kama wasu 7 a Abuja

Published: 20th, May 2025 GMT

’Yan sanda sun bindiga wani wanda ake zargin dan fashi ne har lahira, sa’annan suka kwato bindigogi bakwai a unguwar Maitama da Abuja.

Kwamishinn ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajoa Adewale, ya sanar a safiyar Talata, cewa rundunar ta kama gungun wasu mutum bakwai da suka kware wajen aikata fashi d makami da kuma kwcen motoci.

Ajao ya ce ’yan fashin suna ganin ’yan sanda suka bude musu wuta, inda jami’an suka yi nasarar harbe wani wanda aka fi sani da Baballe, har lahira, suka kama wasu guda bakwai. Shugaban ’yan fashin, wanda ake kira Pastor Mogu da wani mutum daya sun tsere da raunin harbi a jikinsu.

Abubuwan da aka kwace a hannun ’yan fashin sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda hudu, pistol kirar gida guda biyu da wata babbar bindiga da harsasai. Sauran sun hada da mota kirar Toyota Corolla da kuma babur kirar Boxer.

Yadda DSS ta kama ɗan bindiga zai tafi aikin Hajji a Sakkwato An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin maniyyata a Saudiyya

Kwamsihinan ’yan sandan ya ce mutum biyu daga cikin ’yan fashin, tsoffin fursunoni da wani wanda ’yan sanda suke nema bayan ya tsere daga inda ake tsare da shi a Jihar Bauchi.

Ya ce, an samu nasarar ne a wani samame da jami’an runduna ta musamman masu aikin ya ki da miyagun laifuka suka kaddamar.

Rundunar a cewarsa, ta dade tana hakon gungun ’yan fashin da suka addabi mutane da kwacen motoci.

Bayan samun rahoto shirinsu na fara aiki a unguwar Maitama ne jami’an rundunar suka shammace su.

Ajao ya ce ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kuliya domin su fuskanci hukunci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan fashi kwacen motoci

এছাড়াও পড়ুন:

An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar

Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.

A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.

KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja

Ya bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.

Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.

Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.

TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.

Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”

Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.

Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.

Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • Sin Ta Gano Wani Dutse Mai Sassaka Na Daular Qin A Kan Tsaunin Qinghai-Tibet
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa