Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kashe Falasdinawa ‘Yan Gudun Hijira A Lokacin Da Suke Bacci
Published: 20th, May 2025 GMT
Da safiyar yau Talata mazauna yankin “al-Daraj’dake Gaza su ka farka daga cikin sanadiyyar harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa makarantar ” Musa Bin Nusair” dake karkashin hukumar agaji ta UNRWA” wacce take kunshe da daruruwan ‘yan hijira.
Dama dai wannan ba shi ne karon farko da wannan yankin yake fuskantar hare-hare daga HKI ba.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Harin na yau ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 44,mafi yawancinsu mata ne da kananan yara, baya ga wani adadi mai yawa na Falasdinawan da su ka jikkata.
Kananan yara da suke rayuwa a cikin wannan sansanin ‘yan hijira sun rika kai da komowa suna neman kayan wasanninsu daga karkashin baraguzai.
A kusa da asibitin “Ma’amadani” wanda sojojin sahayoniyar su ka kashe mutane 500 a cikinsa, tun farko-farkon yaki, an ga wasu mata suna bak kwana da dangi da ‘yan’uwansu da su ka yi shahada cikin kuka mai kuna.
Tuni dai aka yi jana’izar jam’i ta shahidan su 44.
Yakin Gaza dai ya shiga watanni na 18, ta yadda a halin yanzu babu wani wuri mai rufi idan ba hemomin da ‘yan hijira suke ciki ba. Bugu da kari sojojin na HKI sun lalata dukkanin muhimman cibiyoyin yankin na Gaza, da su ka hada na samar da ruwa, wutar lantarki, da kuma hana shigar da kayan abinci da magani cikin yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara
Akalla mutane uku ne aka ce an kashe tare da yin garkuwa da wasu 26 a wani sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara. Daily trust ta bankado cewa, hare-haren na tun ranakun Alhamis zuwa Asabar, sun shafi al’ummomi da dama a yankin. Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu Yanzu-Yanzu: Ana Zargin Makiyaya Sun Kashe Mutane 15 A Benuwe Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, lamarin ya fi kamari akauyen Sabon Gari, inda aka kashe mace guda tare da yin garkuwa da mazauna yankin kusan 20. Wani mazaunin Kauran Namoda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa, adadin ya zarta haka, inda ya ce an kashe mutane hudu – ciki har da mace guda, tare da sace wasu 26. Rahotanni sun ce daga cikin wadanda aka sacen har da wani mutum, da matansa biyu, da ‘ya’yansu uku. An kai hare-haren ne da sanyin safiyar ranar Asabar da misalin karfe 1:00 na dare zuwa 2:30 na daren, duk da kasancewar jami’an tsaro a garin Kaura Namoda. Majiyoyi sun yi zargin cewa, ‘yan bindigar yaran wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Bello Kaura ne, wanda aka fi sani da Dan Sade, wanda ake alakanta shi da kai hare-haren ta’addanci da dama a fadin kananan hukumomin Kaura Namoda, Bungudu, da Maradun.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp