Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta kai wa Marte ɗauki
Published: 19th, May 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba.
Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya.
Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5Kafin zuwansa, ’yan ta’adda sun sake karɓe iko da Marte bayan harin da suka kai a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka tsere zuwa garin Dikwa.
Gwamnan, ya ce mutane kimanin 20,000 ne suka tsere daga Marte, wanda hakan ka iya kawo matsala musamman ga matasa da za su iya shiga cikin harkokin ta’addanci.
Ya ce: “Muna da alhakin kare Marte. Idan muka rasa wannan gari, za mu iya rasa sauran ƙananan hukumominmu.
“Don haka ina roƙon Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya su haɗa hannu wajen kare wannan gari.”
Zulum, ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Borno.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Ɗauki Gwamnatin tarayya hari Marte
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno
Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa.
Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.”
Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara jajircewa.
Mutum 3 sun mutu, 21 sun jikkata a turmutsitsin karɓar kuɗin tallafi a Borno Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a TarabaSanata Ndume yace ce, “ina farin cikin sanar da ku cewa an kashe ’yan ta’adda biyar a ƙauyen Warambe. Ina kunjinjina wa mafarauta da kuma yadda aka yi saurin ɗaukar matakin tura sojojin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ zuwa wurin, wanda ya ƙara wa al’ummar yankin ƙwarin gwiwa.”
Makaman da aka ƙwato sun hada da bindiga ƙirar AK47 guda biyu da harsasai, kuma an damƙa su a hannun sojoji.