Kasar Sin Ta Cimma Burinta A Fannin Kulla Yarjejeniyoyin Fasaha Kafin Lokacin Da Ta Tsara
Published: 16th, May 2025 GMT
Kididdigar da ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun bana, adadin yarjejeniyoyin da suka shafi fasaha da aka kulla ya kai dubu 228 a kasar Sin, wadanda suka shafi Yuan triliyan 1 da biliyan 600, adadin da ya karu da kaso 13.
A matsayin daya daga cikin muhimman kasuwanni 5 na kasar Sin, bunkasuwar kasuwar fasaha tana da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sana’o’i. Kididdigar ta nuna cewa, a shekarar 2024, jimillar kudaden da aka samu daga kulla yarjejeniyoyin fasaha ta kai Yuan triliyan 6 da biliyan 800, adadin da ya karu da kaso 11.2 bisa dari. Lamarin da ya nuna cewa, adadin ya ci gaba da karuwa cikin shekaru 8 a jere, hakan ya sa, kasar Sin ta kai ga cimma burinta a fannin kulla yarjejeniyoyin fasaha, da darajarsu ta kai Yuan triliyan 5, bisa shirin raya kasuwar fasaha tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2025. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Sin ta a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI A Lokacinda Mayakan Ansarallah Suka Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kasar
An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada rahoton yawan barnan da makamai suka yi ba bayan shigowarsu haramtacciyar kasar.
Yahudawan sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi a yankunan Beersheba, Dimona da kuma garuruwan da suke kewaye da su a safiyar yau Asabar.
Majiyar sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun cilla makaman kan haramtacciyar kasar Isra’ila ne saboda ci gaba da kissan kiyashin da take a zirin gaza.