2025-11-05@23:12:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7585
«yajin aikin»:
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi. Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane. A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani. An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
Hukumar shirya gasar ƙwallon yashi ta ƙasa ta tabbatar da cewa za a gudanar da wasannin ƙarshe na bana a filin wasa na Jabi Lake Park, da ke babban birnin tarayya Abuja. Kodinetan hukumar a Najeriya, kuma shugaban hukumar a nahiyar Afirka, Mahmud Hadejia, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da Trust Radio a cikin shirin “Bakin Raga” da safiyar yau Laraba. An amince da hukuncin yi wa malamai ɗaurin shekara 14 kan lalata da ɗalibai Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano Shugaban ya bayyana cewa wannan ce gasa ta biyar da za a buga, kuma ta farko da za a fafata a Abuja. A cewarsa, za a fara buga wasannin ƙarshe daga...
A gaskiya wannan yanayi ya yi matukar burge ni, kuma sai na zaci ko don saboda ina bako ne, amma yayin da na ga wasu Sinawa suna daukar hotunan bishiyoyin, sai na ce to, babu makawa wannan yanayi ne mai burge kowa da kowa, bako da dan gari kuma ciki har da dattawa. Nan take ni ma na zaro wayata, muka ci gaba da kashe hotuna ni da abokin aikina. Na yi kokarin nuna kawaici a kan yadda yanayin ya shaukantar da ni, amma sai na ga abokin nawa ya fi ni “jazabancewa”, domin shi ya fi ni yawan yin “style” na daukar hoton da kuma yawan hotunan da muka dauka. Wani abu da na lura da shi...
Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu A cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu. Duk da ƙoƙarin jama’a na...
Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa. Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
Haka kuma, kaso 73.2 sun yi imanin cewa manyan kasashe ba sa sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu game da harkokin kasa da kasa, sannan kaso 81.9 sun yi kira ga MDD da ta kara mayar da hankali kan muradu da bukatun kasashe masu tasowa. (FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou November 5, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025
Wani jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a shataletalen Abbatuwar Phototake da ke birnin Jos a Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da mutuwar direban da wani fasinja guda ɗaya, tare da jikkatar wasu mata biyu. Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Laraba, bayan tasowar jirgin daga Bukuru zuwa Jos. Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan Tinubu Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe Wasu mazaunan yankin sun ɗora alhakin faruwar hatsarin kan rashin mutumin da ke kula da shingen tsallaka titin jirgin, wanda ya ratsa titin motoci a daidai shataletalen Abbatuwar Phototake. Sai dai mai magana da yawun...
Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025
Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko. A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa. Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana...
Ƙungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) tare da Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Gabas (NEDC), sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kan mata game da cutar sankara a Jihar Gombe, domin kare mata daga kamuwa da cutar. Dokta Halima Usman Faruk, ɗaya daga cikin likitoci mata da suka halarci wajen taron ta ce, cututtukan sankarar nono da bakin mahaifa na kashe mata da dama a duniya, musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya. Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri “A Gombe kawai, ana samun aƙalla sabbin mata bakwai masu fama da sankara a duk mako. “Don haka yana da muhimmanci mata su rika zuwa...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana numfashi a doron duniya. Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a. Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Yayin da yake hira da ’yan jarida a Kano a yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 70, Shekarau, inda ya ce gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da ɗabi’a. “Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce. Shiga cikin tsarin samar da shugabanni na gari masu gaskiya hidima ce ga jama’a kuma wannan ibada ce a Musulunci,” in ji shi. Tsohon...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri. Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya. Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka An raba motocin ne domin inganta sintiri da kai ɗaukin gaggawa, domin yaƙi da laifuka da barazanar tsaro irin su ’yan daba da sauran masu aikata laifi a Maiduguri da kewaye. Wannan na cikin irin tallafin da Gwamna Zulum ke bayarwa don inganta tsaro da kare...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro bisa daƙile hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka Mamdani ya zama Musulmi na farko da ya zama magajin garin New York na Amurka Abba ya yi wannan yabo ne, yayin da yake karɓar babban kwamandan rundunar soji ta 1, a Hedikwatar Kaduna, Manjo Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, a fadar gwamnati da ke Kano. Manjo Janar Wase, ya ziyarci Kano domin duba halin tsaro a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa. Ya bayyana yadda mahaifinsa,...
Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta Super Eagles, Eric Chelle, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Nigeria za ta lashe kofin nahiyar Afrika na 2026. Gasar da za a buga a kasar Maroko, Challe ya jadda kwarin gwiwarsa, bisa kafa hujja da zaratan yan wasan da Nigeria ta ke da su. Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025, karo na 35 daga ranar 21 ga watan Disamba da tawagogi 24 za su fafata, domin lashe babban kofin tamaulan na Afirka. Wannan shi ne karon farko tun 1988 da Maroko ta karɓi baƙuncin wasannin babbar gasar tamaula ta Afirka da take fatan gudanar da bikin da zai ƙayatar da duniya.
Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne “bisa umarnin alkali.” Ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar shari’a har sai an ci gaba da shari’a. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka tsare a Iran bisa zargin leken asiri. A halin yanzu suna Ofishin Jakadancin Faransa da ke Tehran. A ranar 21 ga Oktoba, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza. Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar da wadannan ayyuka, kuma dukkan bangarorin dole ne su mutunta sharuddan dake kunshe a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya.” “Muna aiki tukuru don kara taimakawa mutanen yankin Gaza; muna goyon bayan mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dawo da alaka tsakanin Gaza da Yammacin Kogin Jordan,” in ji Mista Guterres. Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, hare-haren Isra’ila a Gaza...
China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar da Amurka ta yi na janye tallafi da kuma daukar matakin soja kan kasar da ke Yammacin Afirka saboda zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci. A kwanan nan ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Kiristoci na fuskantar “barazana” a Najeriya, yana mai gargadin cewa Amurka za ta iya tura sojoji idan gwamnatin Najeriya ta gaza dakatar da abin da ya bayyana a matsayin ta’addacin masu kaifin kishin islama. Ya kuma sanar da cewa za a saka Najeriya cikin jerin “kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.” ke sa wa ido. Hukumomin Najeriya dai sun yi watsi da wadannan zarge-zargen, suna bayyana su a matsayin marasa tushe a...
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
Zohran Mamdani ya lashe zaben Magajin Garin birni mafi girma a Amurka wato New York, kuma zai zama Musulmi na farko a tarihi da ya taɓa shugabantar birnin. Mamdani, mai shekara 34 kuma dan jam’iyyar Democrat mai ra’ayin gurguzu, ya samu nasara bayan ya motsa masu ra’ayin sauyi a cikin birnin da ma fadin ƙasar, duk da suka daga Shugaba Donald Trump da ‘yan Republican, da wasu ‘yan Democrat masu matsakaicin ra’ayi. Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150 An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump A jawabin nasararsa bayan doke tsohon Gwamna Andrew Cuomo, Mamdani ya ce yana da cikakken goyon baya daga jama’a, kuma ya bayyana...
Daga Khadijah Aliyu An fara shirye-shirye gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano. An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025. Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, ya umarci kwamitin da ya gudanar da aikinsa da himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Kano. Ya bayyana cewa ana sa ran masana sama da 400 da sabbin mambobi daga ciki da wajen jihar za su halarta. Farfesa Pate ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan jajircewarta wurin...
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta musanta iƙirarin da Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya. A wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a ranar Talata, ƙungiyar ta ce kalaman Trump ba su da tushe kuma suna iya haddasa tashin hankali da rikice-rikicen addini a yankin da tuni ke fama da matsalar tsaro. Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma Shugaban Xi Ya Gana Da Firaministan Rasha ECOWAS ta ce hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a Afirka ta Yamma ba sa bambance tsakanin Musulmi ko Kirista, domin suna cutar da jama’a baki ɗaya. Ƙungiyar ta kuma roƙi ƙasashen duniya su tallafa wa gwamnatocin yankin...
Zohran Mamdani ɗan jam’iyyar Democrat ya lashe zaɓen magajin garin birnin New York. Mista Mamdani shi ne musulmi na farko da ya lashe zaɓen maganin garin a tarihin birnin. Ɗan asalin Asiyan shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya zama magajin garin birnin mai muhimmanci a Amurka. Hakan na zuwa ne a ranar da ake ganin jam’iyyarsu ta yi rawar gani a sauran zaɓukan da aka yi a wasu wurare a Amurka. Mista Mamdani ya yi nasara a kan Andrew Cuomo na jam’iyyar Indifenda da kuma Curtis Sliwa na jam’iyyar Republican wanda ake gani shi ne zai zo na uku a zaɓen. Waɗannan zaɓuka su ne na farko da ake gani kamar wani ƙalubale ne ga gwamnatin Trump. Tuni dai...
Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku. Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a hira da manema labarai a Gombe, a cikin shirin bikin Watan Wayar da Kan Jama’a game da Cutar Sankara. Ta ce an shirya gwajin ne domin inganta gano cutar tun da wuri da kuma bada magani cikin lokaci, kasancewar cancer na nono da na mahaifa su ne manyan cututtukan sankara da suka fi addabar mata. Dr. Hauwa Saurayi ta jaddada cewa gano cuta tun da...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kwara ta ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su ba tare da wata illa ba, a kauyen Igbonla. A cikin wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi, ta fitar, ta ce rundunar ta samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin wani gida, suna harbi a sama, sannan suka tafi da wasu daga cikin mazauna gidan. Daga nan ne rundunar ’yan sanda tare da ’yan banga da masu farauta suka isa yankin cikin gaggawa, lamarin da ya kai ga ceto sun hada da Fatima Wasiu da Kudus Wasiu da jaririya mai watanni shida, ba tare da jin rauni ba. Sai dai har yanzu ana ci gaba...
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin dan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Agwara/Borgu a Jihar Neja, Honarabul Jafaru Mohammed Ali. Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a jiya, a kauyen Kubul, kan hanyar Agwara zuwa Babana, a cikin Karamar Hukumar Borgu, yayin da dan majalisar ke hanyarsa ta zuwa ganawa da jama’arsa kan muhimmin shirin ci gaba. Bayan harin, Honarabul Jafaru da tawagarsa sun samu rauni, inda aka garzaya da su asibiti, kuma suna karbar kulawar likitoci a halin yanzu. A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun isa yankin domin fatattakar ‘yan bindigar da kuma kare rayukan jama’a. Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma a hukumance a yanzu game da...
Kwamishinan Habbaka kiyon Dabbobi na Jihar Kano, Dr. Aliyu Isa Aliyu, ya fara ziyarar wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a kananan hukumomin Ajingi da Dawakin Tofa. Ziyarar ta yi daidai da shirin gwamnati na kaucewa rikici, musamman sakamakon yuwuwar shigowar makiyaya daga Jamhuriyar Nijar cikin jihar. A Ajingi, Dr. Aliyu ya jagoranci tawaga ta jami’an tsaro, ma’aikatan ma’aikatar da shugabannin kungiyoyin manoma da makiyaya, inda ya bukaci tattaunawa, fahimtar juna da zaman lafiya, domin kauce wa sabani. Wakilin Hakimin yankin, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, da shugaban karamar hukumar Dr. Abdulhadi Chula, sun yaba da wannan yunkuri tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kafa ma’aikatar da naɗa kwamishina mai nagarta. A Dawakin...
Pars Today – Wakilin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kalaman shugaban Amurka game da gwajin makaman nukiliya a matsayin abin tsoro. A cewar Pars Today, Amir Saeed Iravani, jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya rubuta a ranar Talata ga Shugaban Majalisar Tsaro da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin martani ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da barazanar nukiliya, yana mai kiran su “abin damuwa ne kwarai da gaske.” Iravani ya yi gargadin cewa irin wadannan kalamai suna wakiltar babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya kuma suna nuna keta hakkokin Amurka a karkashin dokokin kasa da kasa. Shugaban Amurka ya sanar a ranar 29 ga Oktoba cewa...
Pars Today – Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa an gudanar da bincike mafi girma a tarihin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) a Iran, ba tare da an lura da wani karkata ba. Ya kara da cewa Washington da Tel Aviv suna kokarin dorawa duniya iko ta hanyar karya dokokin kasa da kasa. Saeed Khatibzadeh, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran kuma Shugaban Cibiyar Nazarin Siyasa da Kasa da Kasa ta Ma’aikatar Harkokin Waje, ya ce a wata hira da ya yi da CTV na gidan talabijin na Belarus a gefen taron “Tsarin Tsaron Yuropu” da aka yi a Minsk: “Tsaro babban batu ne ga Iran, domin kasar ta kasance abin hari ga hare-haren ta’addanci da kuma kai...
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, daliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba. Da yake magana da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun kasar nan. Kamar yadda na gaya muku, Shugaban Ƙasa ya umarce mu da cewa, ba ya son ASUU ta sake...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirinsa na ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.150, don cike gibin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025. Buƙatar na kunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata. An yi musayar yawu tsakanin Barau da Akpabio a majalisa kan barazanar Trump HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya ce za a samo bashin ne daga kasuwar bayar da lamuni ta cikin gida. Ya ce buƙatar karbo bashin ta zama dole ne sakamakon ƙarin girman kasafin kuɗin shekarar 2025. Shugaban ya kuma ce an gabatar da...
Sai dai Sanata Barau Jibrin ya ce, “Ni ɗan Nujeriya ne, kuma zan faɗi ra’ayina. Ba na jin tsoron Trump. Mu ƙasa ce mai cikakken ’yanci.” Maganarsa ta sa wasu Sanatoci dariya kafin Akpabio ya rufe tattaunawar, inda ya roƙi ’yan jarida su tabbatar da sahihancin labarai kafin su wallafa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno November 4, 2025 Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025
An yi musayar yawu a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin Shugaban Amurka, Donald Trump, na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Zaman majalisar ya biyo bayan sanarwar Trump da ke bayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa Mai Ƙalubale Na Musamman,” yana zargin Gwamnatin Tarayya da bari a ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar. DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Ba addini ne kaɗai ke haifar da rikici a Nijeriya ba — EU Batun ya taso ne a ƙarshen zaman majalisar na ranar Talata, lokacin da Akpabio ya shaida wa ’yan majalisar cewa ’yan Najeriya na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce hakan na karawa ‘yan ta’adda karfi, inda suke amfani da wannan dama wajen tara muggan makamai a yankin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar tsaro. ‘Yan bindigar sun yi ikirarin suna samun kimanin naira miliyan 300 duk mako daga haramtattun wuraren hakar ma’adinai. NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Shirin Daga Laraba na...
Dakta Bukar ya bayyana wannan hadin gwiwar a matsayin abu mai muhimmanci wanda yazo a kan gaba wajen karfafa wayar da kan jama’a game da rawar da sahihan bayanai suke takawa wajen tsara ci gaba da samar da manufofi masu tushe , da dorewar cigaban kasa. Dakta Bukar, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da kafafen yada labarai wajen isar da bayanan Hukumar ga al’umma. A cikin jawabinsa, Kwamishinan yada labarai Malam Ahmed Maiyaki, ya yaba da wannan shiri tare da tabbatar da cikakken goyon bayan Ma’aikatarsa ga manufofin Hukumar. Yace samar da sahihan da kafa gwamnati mai wacce da dogara da adalci yana daga cikin manifofi da kudirorin gwamnatin jihar Kaduna wanda hakan zai taiama wajen kawo...
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba. Jaridar Vanguwar ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar, yana cewa ƙungiyar EU na jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da su a Kudanci da Arewa maso Gabashin ƙasar. HOTUNA: Mun kori jami’ai fiye da 100 cikin shekara guda — DSS Barazanar Trump: Ba ma so a ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Nijeriya — Tuggar Jaridar Vanguard ta bayyana cewa matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira...
A halin yanzu, sashen saukar kumbuna da dukkan na’urori da tsare-tsaren da ke aikin tallafa wa saukar kumbo suna ci gaba da shirye-shiryen tarbar ‘yan sama jannatin, kamar yadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Kumbuna ta kasar Sin ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar November 4, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya November 4, 2025 Daga Birnin Sin Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya gargaɗi Shugaban Amurka Donald Trump, kan kada ya ƙirƙiri wata Sudan ɗin a Najeriya bayan zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar. Mista Tuggar, wanda ya yi jawabi a taron manema labarai a birnin Berlin tare da takwaransa na ƙasar Jamus, Johann wadephul, yana mai cewa Najeriya ƙasa ce mai bin doka da tsarin mulki, wadda ke tabbatar da cikakken ’yancin addini ga dukkan ’yan ƙasa. Dalilin da Trump ya yi iƙirarin ana kisan Kiristoci a Nijeriya — Ndume Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich “Kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ƙasa sun haramta cin zarafin addini, kuma suna tabbatar da damar...
Sanata Ali Ndume ya ce jahiltar halin da Najeriya ke ciki ne ya sa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ana kisan Kiristoci a ƙasar. Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Talata. Ousmane Dembele zai buga wasan PSG da Bayern Munich ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu Sanatan ya ce maganganun Trump sun nuna rashin cikakken fahimtar yadda matsalar tsaro take da sarƙaƙiya a Najeriya. Ya ce matsalar rashin tsaro a ƙasar ta shafi al’umma baki ɗaya ba tare da la’akari bambancin addini ba, yana mai cewa “mutane daban-daban ne ke...
Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Yarima Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa, jam’iyyarsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP bai dawo kan mulki ba a babban zaben 2027. A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ke yawo a Facebook, an ga Abbas yana jawabi ga magoya bayan APC a wani taro da ya yi da masu yada labaran jam’iyyar a karamar hukumar Gwale ta Jihar, inda ya yi wadannan kalamai. “Koma meye zai biyo baya, Abba ba zai koma kan kujerar gwamna ba. Ko Kano ta zauna lafiya ko ta hautsine, babu ruwanmu, amma dole ne Abba ya sauka a kujerar gwamnan Kano,” in ji Abbas ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
A yau Talata ne firaministan Sin Li Qiang, ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya isa birnin Shanghai don halartar baje kolin CIIE karo na takwas. Yayin zantawarsu, Li Qiang ya bayyana aniyar kasar Sin ta karfafa salon wanzar da ci gaba bisa manyan tsare-tsare tare da Najeriya, da zage damtse wajen aiwatar da wasu muhimman matakai goma na bunkasa kawance tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, da hada hannu wajen gina shawarar “Zira Daya Da Hanya Daya” mai inganci, da bunkasa matakin hadin gwiwa a sassan gargajiya, da fadada hadin gwiwa a sabbin masana’antu, da kara kyautata gina tattalin arziki da zamantakewar al’ummun sassan biyu. Li Qiang ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen...
Dan wasan gaban Paris Saint-Germain (PSG) ɗan asalin ƙasar Faransa, Ousmane Dembele, zai kasance cikin tawagar da za ta fafata da Bayern Munich a wasan Champions League da za a buga yau Talata. Dembele, wanda ya zura ƙwallo a wasan da PSG ta doke Bayern Munich da ci 2–0 a gasar Club World Cup zagaye na kwata-final a watan Yuli, bayan mako guda ya fice daga wasa sakamakon jin ciwo a cinyarsa ta dama a fafatawar da suka yi da Lorient. ’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Kocin PSG, Luis Enrique, ya tabbatar da cewa dan wasan ya murmure daga raunin kuma zai iya buga...
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su. China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a Ibadan Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran...
Ya ce, “Wannan ba yana nufin ba a kashe Kiristoci ba ne.” Abin da muke faɗa shi ne, ba Kiristoci kaɗai ake kashewa ba – ana kashe Musulmai ma,” “Addinan biyu sun tabbatar da hakan, akwai kashe-kashen rayuka da yawa da ke faruwa a Nijeriya tsawon shekaru 16 da suka gabata da kuma fiye da haka daga rikicin Boko Haram a 2009. Babu wanda zai iya musanta hakan. “Amma a ce kawai ana kai wa Kiristoci hari ya dogara ne da inda abin ya faru. Idan ya faru a yankin da Kiristoci suka mamaye, a zahiri Kiristoci ne za su kasance waɗanda abin ya shafa kamar yadda yake a yanzu a Benuwe da Filato. “Idan ya faru...
Yayin da yake gabatar da motocin, Gwamna Zulum ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na samar da tallafin kayayyaki ga jami’an tsaro a kowane lokaci. Ya jaddada cewa, tsaro wani bangare ne na muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba. Zulum ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya a Borno. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November...
Ƙasar China ta soki abin da ta kira yunƙurin Shugaban Amurka Donald Trump na yin katsalandan cikin harkokin cikin gida na Najeriya, inda ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Mao Ning, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata, a matsayin martani kan barazanar Shugaba Trump ta tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yaƙi da abin da ya kira kisan kiyashi ga Kiristoci. Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Trump, wanda ya yi ikirarin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya, ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da yin biris da zarge-zargen, yana...
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICEF
KADUNA TA ZAMA JIHAR FARKO A NIJERIYA DA TA AIWATAR DA SHIRIN SAMAR DA ABINCIN MAI GINA JIKI GA YARA – UNICE Daga Abdullahi Shettima. Hukumar Asusun kula da yara kananan yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna bisa zama jihar farko a Nijeriya da ta amince kuma fara aiwatar da shirin samar da abinci mai gina jiki da lafiya ga yara kanana (RUTF) wanda hakan ya zama wani muhimmin mataki wajen yakar karancin abinci mai gina jiki tsakanin yara. Da take jawabi yayin wani taron hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kaduna, wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Wafaa Saeed Abdelatef, ta bayyana yadda jihar Kaduna ta nuna gagarumar jajircewa a bangaren kiwon lafiya tare da samar da...
Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Dick Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Cheney shi ne mataimakin shugaban ƙasa na 46, wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa, George W. Bush a wa’adin mulki biyu daga shekarar 2001 zuwa 2009. An kama barawo da wayoyin sata 17 a taron sauya shekar Gwamnan Bayelsa Karuwanci da zubar da cikin ’yan mata ’yan gudun hijira ya karu a Maiduguri A cewar iyalansa, marigayin ya rasu bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita sakamakon ciwon huhu da na zuciya da jijiyoyin jini. Dick Cheney, wanda aka san shi da tsananin ra’ayin mazan jiya, yana daga cikin mataimakan shugabanni mafi tasiri a tarihin Amurka. Ya taka muhimmiyar rawa wajen...
Matsayar da China ta ɗauka na nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu a lokacin da ƙasashen Yammacin duniya, musamman Amurka, ke matsa lamba kan batutuwan haƙƙin ɗan adam da tsaron cikin gida a Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike November 4, 2025 Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington ya samo asali ne daga muradun jama’a, yana mai gargadin cewa duk wani hadin gwiwa da Amurka za a iya cimma shi ne kawai idan ta kawo karshen goyon bayan da take bai wa Isra’ila, ta kuma janye dukkan sansanonin sojinta daga yankin, sannan ta daina tsoma baki a harkokin Iran. Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana hakan yayin ganawa da wani rukunin dalibai na kasar a jajibirin Ranar Dalibai ta Kasa wacce kuma ta yi daidai da ranar kasa ta yaki da girman kai na duniya. Jagoran ya bayyana ranar a matsayin “ta tarihi” kuma wani muhimmin bangare...
Kasashen Musulmi bakwai, da suka yi taro a Istanbul a ranar Litinin don tattauna makomar Gaza, sun dage kan cewa Falasdinawa ne kawai ke da hakkin mulkin kansu, inda sukayi fatali da sabon tsarin kafa wata wani kwamitin gudanarwa na kasa da kasa a yankin bayan makonni biyu na tsagaita wutar da akayi wacce ke tangal-tangal. “Dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa, kuma Falasdinawa dole ne su tabbatar da tsaron kansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ga manema labarai bayan ganawa da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Pakistan, da Indonesia. “Akwai bukatar sake gina Gaza, kuma mutanenta suna bukatar komawa gida inji shi. Ya bayyana fatansa na “sulhu tsakanin Falasdinawa” cikin sauri tsakanin Hamas...
Ya ƙara da cewa yana cikin farin ciki ganin yadda Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar, inda ya ce, “Shi da Makinde sun taɓa cewa ba za su bari a lalata PDP ba ko a jawo ta ƙasa, amma ga su yanzu; su ne suka faɗi ƙasa.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi November 4, 2025 Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025
A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar. An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.% na kuri’un da aka kada. Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar. Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara. Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar. Gwamnati ta yi...
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.” “Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar. A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa. A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a...
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da wayoyin sata guda 17 da kuma kudi a wurin taron sauyin shkear Gwamna Douye Diri daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. A ranar taron, Gwamna Diri tare da yawancin ’yan majalisar dokokin jihar Bayelsa sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC, a gaban Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni da manyan jami’an siyasa na ƙasa. Shugaban sa-kai na jihar, Doubiye Alagba, wanda ya jagoranci kama wanda ake zargin, ya bayyana cewa an mika mutumin ga jami’an Operation Puff Adder na rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. A cewar Alagba, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya...
Ya kuma tunatar da cewa Nijeriya da Amurka na da kyakkyawar alaƙa tun da daɗewa, don haka bai kamata wannan sabuwar dambarwa ta lalata dangantakar ƙasashen biyu ba. Obi ya ce dole ne a yi amfani da diflomasiyya da tattaunawa wajen shawo kan matsalar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja November 4, 2025 Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump November 4, 2025
Sarakunan gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati sun koka bisa yawaitar kananan ’yan mata da ke daukar ciki da kuma zubar da ciki ba bisa ƙa’ida ba, a sansanonin ’yan gudun hijira da ke Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya fito fili ne a wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da ƙungiyar Grassroots Researchers Association (GRA) ta shirya tare da tallafin We Are Not Weapons of War (WWoW) a karshen makon da ya gabata a Maiduguri. Taron ya haɗa mutane fiye da 500, ciki har da waɗanda suka tsira daga fyade da cin zarafi a lokacin rikici, sarakunan gargajiya, lauyoyi, jami’an gwamnati da abokan ci gaban ƙasa, domin tattauna hanyoyin magance wannan matsala. “’Yan mata kanana na sayar da jikinsu, suna kuma zubar...
Rashin aikin yi na daya daga cikin manyan kalubalen da najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake cigaba da samun matasa dake da karfi a jika amma babu aikin yi. Hukumar kididdiga ta kasa ta fitar da bayanan dake baiyana cewa rashin aikin yi ya karu a najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar, kazalika binciken ya baiyana cewa wadanda basu yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi karatu mai zurfi samun aikin yi. NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Wadansu dalilai ne ke kara kawo rashin...
Bayan shafe lokaci, wani jami’in hukumar shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta. Duk da haka, Natasha ta ci gaba da nuna ɓacin ranta. “Da ban yi bidiyon kai-tsaye ba, da ba za su dawo da min fasfo ba.” A halin da ake ciki, ofishin Akpabio da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo November 4, 2025 Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025
Gwamnatin Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Nijeriya nan take, tana mai cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilan tsaro, bayan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai harin Soji a yankin Yammacin Afrika. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar damuwa a yankin Sahel. Majiyoyin Soji a N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya bayar da umarnin kulle iyakar kasar da Nijeriya, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda daga arewacin Nijeriya na shirin tserewa zuwa cikin Chadi. An ce umarnin ya shafi manyan hanyoyin shiga da fita, musamman ta yankin tafkin Chadi. Rahotanni sun ce an sanya rundunar Sojin...
Ya ce matsalolin Nijeriya suna buƙatar yin nazari, ba kalaman da za su ɓata lamarin ba. Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma a Kudu maso Gabas da su haɗa kai domin samun zaman lafiya da sulhu. A cewarsa, tattaunawa, adalci da kyakkyawan shugabanci su ne hanyoyin da za su kawo ƙarshen tashin hankali da dawo da amincewa tsakanin jama’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump November 4, 2025 Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
Prime ministan kasar sudan Kamil idris yayi gargadin cewa aikewa da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasashen waje a kasar Sudan zai kara ruruta wutar rikicin ne da kuma keta yancin kasar, kuma kalaman nasa suna cewa ne bayan rahoton da aka fitar game da cin zarafin dan Adam da aka yi a El-fasher dake arewacin Darfur. Sudan ta dade tana cikin rikci wanda ya haddasa yunkurin juyin mulki sau 20 a kasar da kuma yakin basasa guda biyu, lamarin ya kara taazzara ne bayan rikicin da ya barke a baya bayan nan, wanda ke barazanar ga zaman lafiya yankin , sai dai har yanzu kasashen duniya basu cimma matsaya ba kan yadda zaa samar da zaman lafiya mai...
rahotanni suna nuna cewa mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya da jagororin sassan tattara bayanan sirri kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump. Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ya ce yana so gwamnati ta dauki matakin gaggawa ko kuma ya turo sojoji domin su yaki maharan da ya bayyana da ƴanbindiga masu ikirarin jihadi. A sanarwar, ya ce, “na ba sashen yaki umarni su fara shirin daukar mataki. Idan har za mu kai hari, to za mu kai harin ne cikin sauri ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda ƴan ta’addan nan suke kai hari kan kiristoci,” in ji...
Ya jaddada cewa gwamnati tana tabbatar da tsaron kowa ba tare da bambanci ba. Kalaman Trump sun haifar da ruɗani da cece-ku-ce a tsakanin ‘yan Nijeriya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025 Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar a yau Litinin cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, sarkin Spaniya Felipe VI, zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, daga ranar 10 zuwa 13 ga watan nan na Nuwamba. (Mai fassara Bilkisu Xin) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce November 3, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025
Jami’ar ta kara da cewa, matakin gaggawa da ya dace Sin da Amurka su runguma, shi ne aiwatar da muhimmiyar matsaya da aka cimma, yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a Busan na kasar Koriya ta Kudu, da ingiza karin daidaito cikin harkokin raya tattalin arziki da hadin gwiwar cinikayyar Sin da Amurka, da ma tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau November 3, 2025 Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran...
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin dukkan ƙananan hukumomin jihar da su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin ƙarfafa zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma. A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayar su a tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance matsalolin da ke addabar yankuna. Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotannin hare-haren ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai November 3, 2025 Daga Birnin Sin Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka November 3, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan November 3, 2025
Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open. ’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian Open a Melbourne a ranar 18 ga Janairu. Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano Kafin hakan dai ’yan wasan biyu, wadanda suka hadu a wasanni uku daga cikin hudu na Grand Slam a shekarar 2025, sun lashe kofuna tara cikin manyan gasa 10 da suka...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025 Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 3, 2025 Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025
Tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Najeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi abin damuwa ne da ke da ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar. Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa na X. Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Obi ya bayyana cewa, barazanar turo sojojin Amurka su yaƙi ta’addanci da ma sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurkan take da damuwa da su, lamari ne da dole dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar ya ja masa hankali. “Babu shakka...
Ko da yake ƙungiyar ta yaba da sakin biliyan ₦10.6 ga asusun gidauniyar likitoci masu neman ƙwarewa (Medical Residency Training Fund) (MRTF) na 2025, ta ce biyan ya kamata ya zama na yau da kullum, a buɗe, kuma ya dace da hauhawar farashi. NARD ta kuma yi tir da dawo da wasu daga cikin likitocin da aka kora a Asibitin Koyarwa na Lokoja (FTH Lokoja), tana mai cewa dole ne a dawo da dukkan su ba tare da sharaɗi ba. Sauran matsalolin da ta jero sun haɗa da bashin albashi da ba a biya ba a BSUTH, da FMC Owo, da OAUTHC Ile-Ife, rashin aiwatar da tsarin one-for-one replacement, da kuma matsalar amfani da likitoci ƴan kwangila a asibitoci da...
Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi. An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Shugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na aikin al’umma da gidan rediyon ke yi, kuma suna da burin faɗaɗa shi zuwa dukkanin ƙananan hukumomin jihar 44. Ya ce, “Mu gidan rediyon al’umma ne da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya? November 2, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi November 3, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan. Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan motsinsu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse. ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya A sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar, sojojin sun gaggauta kai samame yankin bayan samun rahoto, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar. “A yayin arangamar, an hallaka ’yan bindiga 19, kuma...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sake fuskantar wani mummunan sakamako inda ta koma matsayi na 20, wato ƙarshen teburin gasar Firimiyar Nijeriya ta NPFL. Wannan koma baya na zuwa ne bayan ta sha kashi a hannun Enyimba United a wasan mako na 11, wanda aka buga a filin wasa na Enyimba International Stadium da ke birnin Aba a Jihar Abia. An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a Tanzaniya An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Ɗan wasan Enyimba, Bassey John, ne ya fara zura ƙwallo a ragar Pillars a minti na 27, kafin Edidiong ya ƙara ta biyu mintuna kaɗan kafin a tafi hutun rabin lokaci, lamarin da ya nuna...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai wa mutane da dama sun halarta ba. An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a Kano Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump Riƙe da Al-Qura’ni a hannu guda, Shugaba Hassan ta ce “na yi alƙawalin yi wa ’yan ƙasa aiki tuƙuru, zan yi biyayya ga dokoki na ƙasa da mutunta kundin tsarin mulki.” Baƙin da aka gayyata...
Sojojin haɗin gwuiwa ta Operation MESA ƙarƙashin Birgediya ta 3 sun kashe ƴan bindiga 19 a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, bayan wata musayar wuta mai tsanani da ta faru a yankunan Unguwan Tudu, Unguwan Tsamiya, da Goron Dutse da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Asabar. Wannan sumame ya biyo bayan sahihan bayanan leƙen asiri kan motsin wasu ƴan ta’adda da suka shiga yankin daga maƙwabtan dazuka. A cewar sanarwar Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan hulɗa da Jama’a na Birgediya ta 3, Sojojin tare da jami’an tsaro sun fatattaki ƴan ta’addan bayan musayar wuta, inda aka kashe ƴan bindiga 19, yayin da wasu suka gudu da raunin harbi. Ya ce an ƙwato babura da dama da kuma wayoyi...
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36. Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024. BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon...
Sojoji sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan. Bayanai sun ce sojojin sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na shirin ɗaukar matakan soja da ka iya haɗawa da hare-haren ƙasa da na sama a Nijeriya. Trump ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda yake amsa tambayar yanayin yadda hare-haren za su kasance ta sama ko ta ƙasa. NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Tsagin Damagum da Anyanwu sun shirya mamaye hedikwatar PDP a yau A cewarsa, “komai na iya faruwa, abubuwa da dama za su faru. Ina nufin abubuwa masu yawa,” in ji shi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito. Shugaban ya ƙara da cewa, “Suna kashe Kiristoci, kuma suna kashe su da yawa. Ba...
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, ya fitar da wata sanarwa mai karfi yana gargadin cewa kalaman Trump na iya kara ruruta wutar rikicin addini da kuma kara ta’azzara rashin tsaro a kasar. A shafinsa na X, tsohon gwamnan ya yi Allah-wadai da matakin Trump na ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da ke da matukar damuwa,” wanda kuma ya yi zargin ikirarin “kisan kare dangi ga Kiristoci.” Kwankwaso, ya yi kira ga Amurka da ta taimaka wa Nijeriya da tallafin fasaha da leƙen asiri maimakon barazana, sannan ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta zurfafa hulɗar diflomasiyya ta hanyar naɗa wakilai na musamman domin tattaunawa. “Ga ‘yan uwana ‘yan ƙasa,...
Shugaba Bola Tinubu ya ce “ya riga ya yi nisa da wasan da aka tsara a Amurka,” in ji fadar shugaban Najeriya a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci a Najeriya kwanan nan. A cewar Bayo Onanuga, mai ba Tinubu shawara kan bayanai da dabaru, shugaban ya riga ya dauki matakai na dabarun yaki da rashin tsaro a Najeriya tun kafin Trump ya bayyana damuwarsa. Onanuga ya kuma tabbatar da cewa zargin Trump na cewa gwamnatin Tinubu ba ta yi wani abu ba don kare Kiristoci daga hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai ba daidai ba ne. Mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana cewa Tinubu ya gana...
Daga Aliyu Muraki Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin. Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira. A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa, inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa. Haka zalika su ma likitocin ...
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi. NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar. A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin...
Ana ta ce-ce- ku-ce kan batun da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na kawo dakarun kasar sa Najeriya don taimakawa wajen yaki da matslar tsaro. Yayin da wasu ke ganin hakan abun san barka ne, wasu kuwa tofin Ala tsine suka yi ga wannan batu. Shin ko me zai faru idan aka kawo dakarun kasar Amurka Najeriya don shawo matsalar tsaro? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara. Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka. Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don...
Shugaba Donald Trump, ya jaddada cewa Amurka na iya tura sojoji ko ƙaddamar da hare-hare a kan Najeriya idan har kashe-kashen da ya ce ana yi wa Kiristoci suka ci gaba. A yayin tattaunawa da manema labarai da kuma saƙonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mista Trump ya ce ba zai zauna yana kallo ba. “Ana kashe Kiristoci da dama a Najeriya; ba zan bari a ci gaba ba,” in ji shi. A sakon da ya wallafa a dandamalin Truth a ranar Asabar, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji domin “kakkaɓe” abin da ya kira ƙungiyoyin ƴan ta’adda masu kishin addinin Islama. Haka kuma ya yi barazanar dakatar da duk wani taimakon Amurka...
Sabon rikici ya kunno kai a Jam’iyyar PDP yayin da ɓangarori biyu da ke taƙaddamar — na Umar Iliya Damagum, muƙaddashin shugaban jam’iyyar, da na Samuel Anyanwu, sakataren jam’iyyar na ƙasa — ke shirin mamaye hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja yau Litinin. A ranar Asabar, yayin da Damagum da wasu mambobin Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) suka gudanar da taro a Legacy House da ke unguwar Maitama, bangaren Anyanwu kuwa ya gudanar da wani taro daban a ofishinsa da ke Wuye, Abuja. Majiyoyi sun shaida mana cewa bangarorin biyu sun shirya komawa Wadata Plaza, wato hedikwatar jam’iyyar PDP, domin gudanar da ayyuka daga wurin — lamarin da ya tayar da hankalin ma’aikatan hedikwatar. Wani babban jami’in jam’iyyar ya ce, “Abin...
An kama wata matar aure a garin Kuta, hedikwatar Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bisa zargin yankar wuyan mijinta, Salisu Suleiman, da wukar girki. Majiyoyi sun ce matar ta kuma soka wa mijin wuka a idonsa na hagu, lamarin da ya lalata idon gaba ɗaya. Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana wa wakilinmu cewa ma’auratan sun samu saɓani ne, inda matar ta jira har sai da mijin ya kwanta barci kafin ta kai masa hari da wuƙa. Kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarinya auku ne da safiyar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025. A cewarsa, “A ranar 1 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 2:30 na asuba, wani Salisu Suleiman na garin...
Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita cewa dubban yara a falasdinu suna kwana da yunwa kusan kowanne dare, kuma akalla yara 650,000 ba su koma makaranta ba duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimamma a baya –bayan nan tsakanin bangarori biyu, Har ila yau ta bayyana batun dakatar da bude wuta a matsayin labari mai kyau, da ya kawo karshen ci gaba da lugudan wuta da israila ke...
Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun RSF sun kwace iko da El Fasher kuma sun yi kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa. A cikin sanarwar da ta fitar Salma Ishaq, Ishaq ta ce abin da ya faru a El Fasher “ya yi kama da abin da ya faru a El Jeneina a shekarar 2023, amma ba a bankado da kuma yada laifukan...
Daga Yusuf Zubairu Kauru Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu. A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa. Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin. Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda...
Kwankwaso ya kuma buƙaci gwamnatin Tarayya da ta ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da Amurka ta hanyar naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin kare muradun Nijeriya a matakin ƙasa da ƙasa. “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta naɗa jakadu na musamman da kuma jakadun dindindin domin wakiltar muradunmu yadda ya kamata a kasashen waje,” in ji shi. A ƙarshe, yayi kira ga ƴan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da juriya, yana mai cewa lokaci ne da ya kamata a fifita zumunci fiye da rarrabuwar kai. “Yan uwa ƴan Nijeriya, lokaci ne da muke buƙatar haɗin kai fiye da komai. Allah ya taimaki Nijeriya,” in ji Kwankwaso. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe. Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar. Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka A cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa. DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da...