2025-10-29@22:29:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10872
«ta kasar Sin»:
Zhai Kun, mataimakin shugaban kungiyar nazarin yankin kudu maso gabashin Asiya na Sin, kuma farfesa a jami’ar Peking, ya bayyana cewa, tun daga sigar 1.0 zuwa 2.0 har zuwa 3.0, an samu ci gaba mai zurfi ta hanyar sabbin ka’idoji na fasahar zamani da kare muhalli, da sabunta tsarin amince da ka’idojin juna, da kara karfin hadin gwiwar samar da kayayyaki, inda ya inganta yankin ciniki daga matsayin “kara adadi” zuwa “ingantacciyar bunkasa”. A yayin da ra’ayin bangaranci da babakere ke takura tsarin hadin gwiwa na duniya, wannan sabon tsarin ya samar da wata hanya iri ta Asiya don kiyaye tattalin arzikin duniya mai bude kofa. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tataunawa...
An sanya dokar hana zirga-zirgar jama’a a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania, bayan da ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsarin gudanar da zaɓen ƙasar. Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun riƙa yaga hotunan Shugaba Samia Suluhu Hassan tare da ƙona wani ofishin ’yan sanda, yayin da suke zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya na fifita jam’iyya mai mulki, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki. Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu Zanga-zangar dai ta ɓarke ne yayin da ake tattara sakamako bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen na...
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
An bayyana cewa mahalartan EIMC 18 sun fito ne daga hukumomin tsaron Nijeriya da kuma ƙasashen Afrika kamar Chadi, Ghana, Rwanda, Somalia, da Gambiya. A cikin laccarsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa salon Zamfara ta zama abin koyi ga sauran sassan Afrika wajen nazarin yadda ake ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci gaba. Ya ce, “A cikin shekaru 20 da suka wuce, tsarin tsaro a Afrika ya sauya sosai. Ra’ayin cewa gwamnati ita kaɗai ke da ikon amfani da ƙarfi yanzu ya fara fuskantar kalubale daga ƙungiyoyi marasa bin tsarin gwamnati – ciki har da ‘yan sa-kai, ƙungiyoyin kare kai, ‘yan ta’adda, barayin daji da kuma cibiyoyin aikata laifuka na ƙasa da ƙasa.” Gwamnan ya bayyana...
An yi taron musamman na Rasha bisa taken “Kirkire, bude kofa da more Ci Gaba” a ran 27 ga watan nan da muke ciki, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya shirya tare da gudanarwa a Moscow. A cikin jawabinsa ta bidiyo, shugaban CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, an kammala cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar dake jawo hankalin duniya cikin nasara a Beijing. Taron ya sake shelar wa duniya cewa Sin za ta fadada bude kofarta ga duniya, ta kuma bude sabon babi na samun wadata ta hanyar hadin gwiwa. CMG zai ci gaba da gina dandalin tattaunawa na duniya tare da abokan hulda,...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025 Labarai COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa October 29, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci October 29, 2025
Kakakin ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin Pei Xiaofei ya bayyana a yau cewa, yanayin ruwa da na iska a kasar ya ci gaba da ingantuwa a cikin watanni 9 na farkon bana. A cewarsa, matsakaicin nauyin burbushin abubuwan dake cikin iska na PM2.5, wanda shi ne muhimmin ma’aunin gurbatar iska, ya tsaya kan microgram 26 kan kowane cubic mita, a cikin birane ko garuruwan Sin 339, daga watan Janairu zuwa na Satumba, wannan ya nuna cewa an samu raguwar ma’aunin da kaso 5.1 kan mizanin shekara-shekara. Haka kuma, cikin watanni 9 na farkon bana, an samu ingantacciyar iska a kaso 87.6 na kwanakin, wanda ya karu da maki kaso 1.8 kan na bara. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa...
Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan.
Rahotanni sun bayyana cewa cewa kasar Pakistan ta bayyana cewa za ta dauki mataken da suka dace wajen kare tsaron alummarta da kasarta bayan kawo karshen yajejeniyar dakatar da bude wata ta kwanaki 4 tsakaninsu da kasar Afghanistan ba tare da wani ci gaba da aka samu ba, Yarjejeniyar ta waste ne kwana daya kafin cikarta bayan wani mummunan fada da aka tsakanin kasashen biyu da ya jawo dama suka mutu ciki har da fararen hula, Pakistan na zargin Afghanisatan da boye kungiyoyin yan ta’adda dake kai hare-haren ketare iyaka, sai da Kabul ta musanta wannan zargin kuma ta dage akan ikonta, A karshen mako ne minsitan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya yi barazanar barkewar yaki tsakani, idan dai mataken...
CIBIYAR yin nazarin yankuna dake islam abada ta gudanar da wani taron tattaunawa mai take takunkumin snapback kan iran da kuma faduwar yanki, ya kunshi jami’an diplomsiya , malamai da kwararru kan manufofi da siyasa da tsarin doka, sun bayyana damuwar da ake da ita na sake kakabawa iran takunkumi karkashin tattaunawar JCPOA. Kwararrun sun yi barazanar cewa sake kakabawa iran takunkumi zai iya haifar da mummunan sakamako ba wai ga tattalin arzikin kasar iran ba kawai, ga ma harkokin kasuwanci a yankin, tsaro da makamashi zai iya zarcewa zuwa inda ba’a yi tammani ba, Tattaunawar ta zo ne adaidai lokacin da kasashen turai ke kokarin rusa yarjejeniyar JCPOA wanda zai kai ga sake dawo da takunkumin kwamitin tsaro...
Ƴan sanda a kasar Tanzania sun saka dokar hana zirga-zirga a fadin kasar bayan zanga-zangar da ta barke yayin zaben shugaban kasa da ya rikide ya koma tashin hankali a wasu sassa daban-daban na kasar. Rahotanni sun nuna cewa, zanga-zangar ta barke ne musamman a birnin Dar es Salaam da wasu garuruwa yayin da jama’a ke nuna rashin jin daɗi kan yadda ake gudanar da zaben shugaban kasar. Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya a tsarin zaben, kuma sun nemi gwamnati ta gyara tsarin zabe da kuma ba kowa damar fadin albarkacin baki. A cewar jami’an tsaro, an sanya dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sai dai wasu kungiyoyin kare hakkin dan...
Majalisar dattijan Najeriya na aikin tantance manyan hafsoshin sojin kasar wadanda shugaban kasar Bola Tinubu ya nada domin jan ragamar bangaren tsaro a fadin Kasar. Da farko majalisar ta bayyana cewa za ta gudanar da tantancewar ne a mako mai zuwa, sai dai daga baya ta yanke shawarar matso da tantancewar zuwa yau Laraba A ranar 24 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya yi sauye-sauye a jagorancin bangaren tsaro na kasar, inda aka sauya hafsan hafsoshin kasar Christopher Musa da Laftanar-Janar Olufemi Olatubosun Oluyede. Haka nan shugaban ya naɗa Manjo-janar Waidi Shaibu a matsayin hafsan sojojin ƙasa, da Air Vice Marshall S.K. Anekea matsayin hafsan sojin sama sai kuma Rear Admiral Idi Abbas a matsayin hafsan sojojin ruwa. Bayan...
Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Turkiya Rajab dayyib ardogan da ma alummar kasar na farincikin zagayowar ranar da kasar ta samu yancin kai, kuma ya jaddada muhimmancin kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Iran da Turkiya suna da alaka mai zurfa ta tarihi aladu da kuma dabarun yaki, a daidai lokacin da ake samun sauyi a yankin , akwai bukatar kasashen biyu sun kara hadin guiwa a fannonin kasuwanci tsaro da kuma diplomasiya, sakon na pezeshkiyan ya nuna aniyar iranta fifita yin hulda tsakanin kasashen biyu Akwai abubuwa da dama da suka yi kama da juna tsakanin kasashen biyu masu abokantaka da yan uwantaka, pezeshekiyan, ya kara da cewa ta...
Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da ƙarar neman a kwace kuɗin, yana sanar da kotun cewa, ICPC ta bi umarnin wucin gadi na kwace dalolin da ta yi a baya. Ya ce, an buga sanarwa ta jama’a inda aka gayyaci duk wani mutum wanda yake ganin akwai dalilin da zai hana ko kuma bai kamata a kwace kudin ba har abada, amma babu wanda ya amsa. “Saboda haka, muna neman a ba da umarnin a kwace kudin har abada a mayar da su ga Gwamnatin Tarayya, saboda bin umarnin wucin gadi kuma babu wanda ya nuna adawa da hukuncin,” in ji Akponimisingha ga kotun. Hukuncin ya biyo bayan umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a ranar...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sassauci wa matar nan da kotu ta yankewa hukuncin kisa bayan samunta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda. Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kasar ya janye sunan Maryam Sanda daga cikin jerin waɗanda ya yi wa afuwa a kwanakin baya. Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a Taraba Ana iya tuna cewa, a farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da suka haɗa da matattu da masu rayayyu. Abin da ya fi daukar hankali a lokacin da aka sanar da afuwar shi ne ganin sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka, cikin wadanda...
Asalin tsarin shari’ar da ake amfani da shi game da kare muradun al’umma ya bai wa masu gabatar da kara damar yin aiki na neman hukunta masu laifi a madadin sauran al’umma a shari’o’in da suka shafi laifukan gurbata muhalli, da rashin kiyaye tsaftar abinci, da kuma rashin da’a ga gwamnati wadanda dukkansu idan aka bar su kara-zube, za su tauye hakkokin galibin jama’a. Amma a halin yanzu, sabon daftarin dokar da ake son kafawa ya fayyace nau’ikan dokoki 16, ciki har da karin wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka shafi al’adun gargajiya da kuma tsaron kasa, wanda ke nuna kara fadada tsarin dokar. Domin ganin ba a tauye hakkin kowane bangare tsakanin mahukunta da mabiya ba, a...
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump October 29, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu October 28, 2025
Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu laifukan da suka haɗa da kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu. Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin kashe mijinta, ba ta cikin sabon jerin sunayen wadanda aka yafe wa laifi. Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunayen mutane kimanin 50 daga tsohon jerin bayan ce-ce-ku-ce daga jama’a. “Bayan duba martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane daga jerin wadanda aka bai wa afuwa,” in ji Onanuga. Ya kara da cewa an dauki wannan...
Babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya Super Falcons ta samu tikitin buga gasar cin kofin nahiyyar Afrika ta mata ta 2026 da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci. Super Falcons ta samu nasarar ne bayan tashi kunnen doki 1 da 1 da takwararta ta jamhuriyyar Benin a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abeokuta a yammacin jiya Talata. Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra Kunnen doki ya bai wa Najeriya nasarar shiga cikin jerin ƙasashen da zasu buga kofin na Afrika, bayan Falcons ta doke Benin da ci 2 – 0 a makon jiya a birnin Cotonou. Hakan na nufin...
Rikici tsakanin bangarori biyu a garin Donga na Jihar Taraba, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a kan limancin masallacin Juma’a na garin. Bayanai sun nuna baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun jikkata kuma an lalata dukiyoyi. An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Rikicin, kamar yadda Aminiya ta gano, ya faru ne a ranar Talata kan limancin masallacin Juma’a na garin da ke gaban fadar Sarkin Donga. Wata majiya daga garin ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin kungiyoyi biyu na al’ummar Musulmi a garin kan wanda ya kamata ya zama...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin. Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin. An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Waɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara...
Wata gamayyar malaman addinin Musulmai ƙarƙashin inuwar Concerned Ulama of Sunnah ta aika da ƙorafi zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna tana zargin wasu malamai biyu da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Ana zargin malaman ne da yi batancin a cikin wa’azozinsu na kafafen sada zumunta. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Ƙorafin, wanda malamai goma sha shida (16) suka sanya wa hannu, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Umar Shehu Zaria da Malam Muhammad Sani Abubakar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Na’iya, ya bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki. A cewar masu ƙorafin, ayyukan waɗannan malamai biyu “na...
Mummunan cin zarafi a birnin El Fasher na kasar Sudan ya haifar da tofin Allah tsine da Allah wadai daga al’ummomin ƙasashen duniya da na cikin gida Kisan gilla da laifukan da ake aikatawa kan fararen hula a El Fasher, Arewacin Darfur, sun jawo Allah wadai daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam, yayin da gwamnati da hukumomin yankin ke musayar zarge-zarge game da musabbabin bala’in da kuma nauyin da ke kan al’ummar duniya. An ci gaba da Allah wadai da kasashen duniya da na cikin gida game da take hakkin da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta aikata kuma har yanzu take aikatawa kan fararen hula a El Fasher Arewacin Darfur. Kwamishinan...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa fararen hula a Sudan Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana damuwa game da rikicin makamai da ya barke a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Sudan, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula marasa laifi a birnin. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar a yammacin jiya Talata, Baqa’i ya nuna damuwa game da rikicin makamai da ya barke a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Sudan, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula marasa laifi a birnin. Baqa’i...
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da aka sanya wa Cuba nan take ba tare da wani sharaɗi ba. Ya bayyana cewa: Kawo ƙarshen waɗannan matakan ba wai kawai zai samar da sauƙi ga al’ummar Cuba ba ne, har ma zai aika da saƙo mai haske da yanke hukunci ga duniya cewa zamanin tilastawa, mulkin mallaka, da rashin adalci na tattalin arziki ya ƙare. Irawani ya jaddada a ranar Talata, a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da aka keɓe don tattauna ɗage takunkumin Amurka...
Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu ta soki shirin Trump kan Gaza tana mai jaddada cewa: “Yana daga mafi munin cin mutuncin da ta taɓa gani a rayuwarta Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Haƙƙin Dan Adam a Yankin Falasɗinu, Francesca Albanese, ta bayyana shirin zaman lafiya na Shugaban Amurka Donald Trump a Gaza a matsayin “mafi munin cin mutunci da na taɓa gani a rayuwarta,” tana mai tabbatar da cewa Shirin ba shi da haƙƙi na shari’a da na ɗabi’a. Albanese ta bayyana cewa: Ba ta da imani da tsarin siyasa na yanzu da ake Shirin aiwatarwa a Gaza ba, tana mai ƙarawa da cewa, “Ba za a iya gina...
Habiba Abubakar mai shekaru 35 da ’yarta Adama mai shekaru 9 sun rasa rayukansu bayan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno. Mai magana da yawun Rundunar ’San Sanda ta jihar, Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, yayin da suke komawa gida daga gona. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi Ya ce, “Sun fito daga gona ne kuma suna ƙoƙarin ketare wani kogi da ke kusa da kauyen Ghung. Amma...
Gwamnatin kasar Kamaru ta ce za ta dauki matakin shari’a kan babban jagoran adawar kasar, Issa Tchiroma Bakary, bisa zarginsa da tayar da tarzoma bayan zaben shugaban ƙasa. Ministan cikin gida na kasar, Paul Atanga Nji, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai suka nuna. Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Ya ce hukumomin kasar sun fara tattara saƙonnin kafafen sada zumunta da bidiyo da aka bayyana a matsayin “ƙarya” da kuma masu tayar da hankali domin a gurfanar da masu wallafa su a gaban...
Falasdinawa da dama ne suke ci gaba da yin shahada sakamakon ci gaba da kai hare-hare kan Zirin Gaza da Yahudawan Sahayoniyya ke yi An kashe fararen hula Falasdinawa da dama, wasu kuma sun jikkata yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren sama a yankin Gaza tun jiya da daddare, wanda hakan keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne. Majiyoyin lafiya sun ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 65 tun jiya da daddare har zuwa wayewar gari a yau Laraba, ciki har da 18 daga birnin Gaza da arewacin yankin Gaza, 40 daga tsakiyar yankin Gaza, da kuma 7 daga Khan Younis. Majiyoyin yankin sun ruwaito cewa jiragen yakin sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ɗan kasuwa mai taimakon al’umma, Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa shugaban na da kwarewa da hangen nesa wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar da inganta jin daɗin jama’a. Zaura ya yi wannan kiran ne lokacin da wata tawaga daga Tinubu/Shettima Campaign Group ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, inda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Nijeriya na da matuƙar muhimmanci domin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tabbatar da matsayi irin na ƙasashen da ke...
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu. Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.” A watan Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya umarci kwamiti na musamman na gwamnati da ya ɗauki matakan gaggawa don rage tsadar abinci a faɗin ƙasar nan. Duk da haka, wasu manoma na kukan cewa matakan sun jawo musu asara saboda tsadar kayan noman da suke amfani da su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October...
Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu. Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.” A watan Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya umarci kwamiti na musamman na gwamnati da ya ɗauki matakan gaggawa don rage tsadar abinci a faɗin ƙasar nan. Duk da haka, wasu manoma na kukan cewa matakan sun jawo musu asara saboda tsadar kayan noman da suke amfani da su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October...
“’Yan majalisa suna kuma fuskantar barazana daga wasu ‘yan yankunansu da ke samun damar shiga ofisoshinsu ba tare da izini ba.” Ya ƙara da cewa idan aka kasa magance waɗannan matsalolin tsaro, hakan na iya kawo cikas ga gudanar da ayyukan majalisar kamar wakilci, sa ido, tattaunawar kasafin kuɗi da zaman majalisar, wanda zai iya shafar tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya. A watan Mayun shekarar 2021 ma, an taɓa samun irin wannan gargaɗi lokacin da Boko Haram ta yi shirin kai hari Majalisar Dokoki da wasu muhimman gine-ginen gwamnati a Abuja. Bayan wannan gargaɗi, an taƙaita shiga majalisar, inda masana tsaro suka buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara tsaurara matakan tsaro a muhimman wuraren gwamnati. Garba, ya yi...
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Ali Larijani (SNSC) ya ce dangantakar da ke tsakanin Tehran da Islamabad tana habaka, kuma za ta iya kaiwa matsayin babban hadin gwiwa na din-din-din. Ali Larijani, a yayin da yake yin wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan Syed Mohsin Naqvi a wannan Talata a birnin Tehran, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar ƙasashen biyu a fannin tattalin arziki. Ya nuna yarjejeniyar dabarun da aka cimma a cikin kwanakin nan tsakanin Pakistan da Saudiyya, a matsayin mataki mai kyau kuma na hikima, wanda yake da tasiri matuka ga irin barazana da kasashen musulmi sue fuskata daga makiya. Larijani ya ce yanayin yankin a yau yana cike da ƙalubale daga maƙiya, wanda ke...
Firayim Ministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani ya jaddada cewa wajibi ne a kan al’ummar Iraki kare ‘yancin kundin tsarin mulkin kasarsu wanda hakan ba zai yiwuwa ba sai hanyar tsara makomar kasar ta hanyar sahihin zaben ‘yan majalisar dokoki da ke tafe. Al-Sudani ya jaddada cewa babu wani uzuri na kin kauracewa zabe da za a yarda da shi, yana mai bayyana cewa yin hakan “zai share fagen dawowar wadanda suka gaza da kuma wadanda suka ci hanci da rashawa.” Ya ce, “Muna dogaro da shiga cikin harkokin zabe cikin sani da himma a ranar 11 ga Nuwamba, ranar da za mu tsara sabuwar makomar siyasa ta Iraki.” Ya fayyace, “Muna son manufofin hikima da fifita muradun Iraki da al’ummar...
Firayim Ministan Habasha Abiy Ahmed ya yi kira da kasashen duniya su shiga Tsakani domin yin tsakanin kasarsa da Eritrea kan batun Tekun Ja, yana mai jaddada muhimmancin kawo karshen duk wata tashin tashina a yankin Kahon Afirka. Abiy, yayin da yake jawabi ga majalisar dokoki a Addis Ababa, ya yi watsi da batun yin amfani da karfin soja amma ya jaddada cewa dole ne a saurari bukatar Habasha, kuma a warware batun ta hanyar diflomasiyya. “Bukatar Habasha ita ce samun damar shiga teku, amma ba mu da niyyar shiga yaki da Eritrea. Akasin haka, mun gamsu cewa za a iya warware wannan batu ta hanyar lumana da fahimtar juna ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba,” in ji...
Sama da Falasdinawa 60, ciki har da yara 22 ne suka yi shahada a jerin hare-haren jiragen yakin Isra’ila suka kai a wurare da dama a yankin Gaza A cikin sa’oin da suka gabata, A cewar majiyoyin lafiya. Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a lokaci guda kan gidaje, masallatai, da sansanonin ‘yan gudun hijira. Wakilin Al-Mayadeen ya ruwaito cewa an kai wani harin bam a kan gidan iyalan Abu Dalal da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, inda aka kashe mutane 10, ciki har da yara uku. An kuma kai hari gidan iyalan Aql da ke sansanin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane uku da kuma jikkata da dama, yayin da Isra’ila take ci gaba da kai hari...
Masana kayan tarihi a Senegal sun gano sabbin shaidu na kisan gillar da aka yi a lokacin mukin mallakar Faransa a kasar a shekarar 1944, a matsayin wani bangare na kokarin da gwamnati ke jagoranta na gano gaskiya game da batun kisan da sojojin Faransa suka yi a kasar da ke yammacin Afirka a lokacin da ake cikin yakin duniya na biyu. Makabartar sojojin Thiaroye, wacce ke kusa da babban birnin Dakar, a halin yanzu ita ce wurin bincike da aka yi fafakeken rami domin tono kayan tarihi da nufin gano gawarwakin sojojin da ake zargin sojojin mulkin mallaka na Faransa sun kashe su a ranar 1 ga Disamba, 1944. Lamarin ya faru ne bayan da aka kawo kusan sojoji...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu October 28, 2025 Daga Birnin Sin Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona October 28, 2025 Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025
A zantawarsa da manema labarai, jagoran tafiyar Shelkh Umar Shehu Zaria wanda kuma shi ne, babban limamin Masallacin Mus’ab Ibn Umair, Sun jaddada cewa, su ba su da wani buri na daban face ganin an samu zaman lafiya, hadin kai, da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai da jama’ar Kaduna baki daya. “Wadannan malamai guda biyu suna fakewa da malunta suna cin mutunci Manzon Allah SAW. Da’awarsu a Kaduna barazana ce ga zaman lafiya, saboda fitina a jihar Kaduna ba za ta haifar da abu mai kyau ba,” inji shi Ofishin kula da harkokin addinai karkashin jagoranci Malam Tahir Umar Tahir, ya karɓi takardar korafin kuma ya tabbatar da cewa, zai gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar...
A nasa bangare kuwa, ministan kimiyya da kirkira na Afirka ta Kudu, Dr. Blade Nzimande, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, ya gamsu da babban nasarar da Sin ta samu a wa’adin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14. Ya ce, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba mai karfi ba tare da tangarda ba, kuma yana karawa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa. Ya ce Afirka ta Kudu tana fatan koyi daga sabon tsarin ci gaban Sin, don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka shafi sauyin yanayi, da tattalin arzikin dijital, da fasahar sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU...
Sanarwar ta ce, wannan horo mai taken ‘Computer Appreciation Training’ an shirya shi ne ta Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), a matsayin babban taron ƙarawa juna sani ga manyan jami’an gwamnati. A jawabinsa yayin buɗe shirin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan horo wata muhimmiyar hanya ce wajen cimma burin gwamnatinsa na ingantaccen aiki ta amfani da fasaha. Ya ce, “Burin mu shi ne tabbatar da cewa kowane bangare na gwamnati yana aiki cikin tsari, inganci da sauri, kamar yadda fasaha ke bai wa duniya damar gudanar da aiki cikin sauƙi. “Mun shiga wani zamani ne da fasaha ke sauya yadda ake gudanar da mulki – daga tsarin tsara manufofi, yanke shawara, zuwa yadda ake...
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025
Fitaccen marubucin nan ɗan Nijeriya wanda ya taɓa lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce gwamnatin Amurka ta soke bizarsa tana mai haramta masa shiga ƙasar. Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Legas a ranar Talatar nan. Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza Juventus ta kori kocinta Igor Tudor Ya bayyana cewa Ofishin Jakadancin Amurka ne ya sanar da shi batun ƙwace bizar a wata wasiƙa da ya aike masa. Sai dai ya sanar da cewa ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har zai sa Amurkan ta soke bizar da ta ba shi. “Ya zama dole ne na kira...
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, wasu manoma uku da makiyayi daya sun samu kananan raunuka. Ya kara da cewa an tura ‘yansanda da ‘yan banga na yankin don dawo da zaman lafiya. Kakakin rundunar ‘yansandan ya kuma ce, sun kama mutane 17 da ake zargi da hannu a rikicin, amma zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260 October 28, 2025 Labarai Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi October 28, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October...
Kuri’un na jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, sun tattaro ra’ayoyin jama’a daga manyan kasashen duniya masu tasowa, da ma na kasashe masu samun saurin ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 28, 2025
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci rundunar sojin ƙasar da ta kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, bayan ya zargi ƙungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma. Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar, ta ce: “Bayan tattaunawar tsaro, Firaminista Netanyahu ya umurci rundunar soji da ta gaggauta kai hare-hare masu ƙarfi a Zirin Gaza.” Juventus ta kori kocinta Igor Tudor An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Sanarwar na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas ta karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanakin baya domin ba da damar kai agaji ga fararen hula da ke yankin. Tun da farko dai Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka October 27, 2025
Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar. Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Labarai Tsohon Kwamishina...
An bude taron ministocin cikin gida na kasashen kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO a birnin Tehran. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Massoud Pezeshkian ne ya jagoranci bude taron wanda shi ne karo na hudu. Ministoci da manyan jami’ai daga Pakistan, Tajikistan, Turkmenistan, Jamhuriyar Azerbaijan, Afghanistan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Turkiyya, Uzbekistan, da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na halartar taron, tare da Sakatare Janar na ECO, Ministan Cikin Gida na Oman, da Mataimakin Ministan Cikin Gida na Iraki a matsayin baki. Mahalarta taron na tattauna batutuwan tsaro, sa ido kan iyakoki, tattalin arziki, da alaka tsakanin birane. Ya yi kira ga kasashen Tsakiyar Asiya, na Caucasus, Kudancin Asiya, Yammacin Asiya da Tekun Farisa, gami da kasashe membobin OCE, da su “yi...
Sojojin Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa uku yayin da suke fadada hare-haren da suke kai wa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA, wanda ya ambato majiyoyin yankin, ya ruwaito cewa sojojin mamayar sun mamaye kauyen Kafr Qud da karfin soja a ranar Talata. Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa ta bayyana shahidan da sunan Abdullah Muhammad Omar Jalmana, mai shekaru 27, Qais Ibrahim Muhammad al-Baytawi, mai shekaru 21, da Ahmed Azmi Arif Nashti, mai shekaru 29. Hamas ta yi Allah wadai da kisan na Isra’ila tana mai cewa kisan nasu “ya zama sabon laifi na laifukan da gwamnatin mamaya ta aikata kan mutanenmu a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Share 0 0 votes Article...
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta kori kocinta, Igor Tudor, bayan da ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki biyar kacal a wasanni biyar da ta buga a baya-bayan nan. A cewar wata sanarwar da kulob ɗin ya fitar a ranar Litinin, Massimiliano Brambilla, wanda shi ne kocin tawagar maza ta farko, zai jagoranci Juventus a wasan da za ta kara da Udinese a ranar Laraba. An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba “Juventus FC na sanar da cewa ta sallami Igor Tudor daga matsayin kocin tawagar maza ta farko, tare da sauran jami’ansa...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
Kasar Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji zuwa Ukraine don taimakawa Kyiv. Hukumar leken asiri ta Rasha (SVR) ta bankado cewa Faransa ta shirya aika Sojoji 2,000 zuwa Ukraine. Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira wannan yiwuwar “abin da ba za a yarda da shi ba,” tana mai gargadin hadarin dake tattare da shi. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta shawarci Paris da ta yi amfani da wadannan sojojin don kare gidajen tarihi na Faransa maimakon tura su a Ukraine. Dama a baya ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayyana cewa duk wani yanayi da ya shafi tura sojojin NATO a Ukraine ba abin yarda ba ne ga Rasha kuma yana iya fuskantar barazanar...
Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe mabukata. To mene ne dalilin nasarar Sin a wannan bangare? Gaggarumar nasarar da Sin ta samu a bangaren aikin gona, ba wani abu ba ne illa jajircewar gwamnatin kasar da dabaru da fasahohin aikin gona da kullum ake lalubowa. Misali, ko a cikin hamada, kasar Sin ta lalubo dabarun da suka dace, inda ake noman tsirrai masu juriya dake iya ciyar da mutane da...
Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004. Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
Rundunar ’yan sandan Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’ai 59 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin ɗawainiyar da rundunar ‘yan sandan ke yi wajen kula da jin daɗin jami’anta da iyalansu. Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jigawa, CP Dahiru Muhammad ne ya wakilci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, wajen raba tallafin a ƙarƙashin shirin nan na tallafa wa iyalan...
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun ci gaban al’adu da dabi’a a cikin al’umma a zahirance, da kara inganta jin dadin rayuwa, da samun manyan sabbin ci gaba wajen zurfafa shirin samar da kyakkyawar kasar Sin, da kuma kara samun ci gaba wajen karfafa garkuwar tsaron kasa. A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 (2021-2025), an kiyasta cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai zarce yuan...
Majalisar Dattawa za ta gudanar da zaman tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar a gobe Laraba waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwanan nan. Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin hafsoshin zuwa majalisar ne domin tantancewa da amincewa da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru ’Yan bindiga sun sa harajin N15m kan al’ummar Mazabar Sanata Tambuwal A wata wasiƙar fadar shugaban ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman da aka gudanar a wannan Talatar, ya ce kwamitin da ke kula da harkokin tsaro zai zauna gobe domin tantance waɗanda aka naɗa. A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya aiwatar...
Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, zai cika shekaru 39 a watan Yuni mai zuwa. Ya ce yana jin daɗin zama a Miami bayan shekaru masu yawa da ya shafe a Barcelona da kuma lokacin da ya yi a Paris Saint-Germain. Messi ya buga wasanni 195 tare da Argentina, inda ya zura ƙwallaye 114, kuma ya taimaka musu wajen lashe manyan kofuna kamar Copa América, Finalissima, da Kofin Duniya na 2022 a Qatar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni...
Rikici na kara bazuwa a Jamhuriyar Kamaru kwana guda bayan Kotun Kolin ta tabbatar da Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai cike da takaddama. Dan takarar jam’iyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ta sake bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben ba, yana mai cewa “zaben ba sahihi ba ne” yana mai yin fatali da nasarar Shugaba Biya. Sanarwar sakamkon ta janyo zanga-zanga, kone-kone da fada a tsakanin jama’a da jami’an tsaro a biranen Douala da Mbouda da Bertoua da Batouri, inda ake ci gaba da samun rikice-rikice lalata dukiyoyi. Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kona gine-gine da farfasa abubuwa, da satar kaya a wasu manyan birane ciki har da...
Ya ba da shawarar a mayar da wajen ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki ko ɗakin taro maimakon a sayar shi. Kiru, ya buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki alhakin kura-kuran da aka tafka a wajen wannan aikin, tare da tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai sake faruwa ba a nan gaba, musamman a harkokin ilimi da suka shafi jin daɗin dalibai da al’umma. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Labarai ’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi October 28, 2025 Labarai An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi October 28, 2025
Mazauna ƙauyukan Bazar da makwabtansu a Karamar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato, sun koka cewa ’yan bindiga sun kakaba musu harajin Naira miliyan 15 tare da barazanar kai sabbin hare-hare idan ba a biya ba. Wadannan ƙauyuka suna yankin Mazabar Sanatan Kudu ta Kudu, inda tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ke wakilta. Wani mazaunin yankin, Dauda Umar, ya shaida wa manema labarai, cewa “abin yana da matuƙar tsanani” kuma yana buƙatar gaggawar kulawar gwamnati. “Ina tabbatar muku cewa ’yan bindiga sun nemi Naira miliyan 15 daga gare mu, suka yi barazanar aikata mummunan abu idan ba mu biya ba. Ban san abin da za su yi ba kai tsaye, amma an riga an kakaba wannan haraji, wasu na...
Al’ummar Unguwar Filin Samji da ke garin Katsina sun buƙaci hukumomi su tabbatar da adalci, bisan zargin da ake wa jami’an Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma na gwamnatin jihar (C-Watch) da harbin mutane da kuma lakaɗa musu duka ba tare da dalili ba. Wata matar aure mai suna Khadija Hamisu Wada ta samu raunuka sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu mutane da dama suka ji raunuka bayan an kai musu hari da adduna, wuƙaƙe da sanduna. A cewar mazauna yankin, aƙalla mutane bakwai ne suka ji munanan raunuka a lokacin da abin ya faru. An ruwaito cewa Khadija na dauke da harsasai biyu a ƙugu, kuma likitoci sun gargadi cewa cire su da gaggawa na iya jawo mata matsalar...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Haɗin kai a tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ba zaɓi ba ne, amma dole ne Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Hadin kai da hadin gwiwar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya a cikin tsarin Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki (ECO) ba wani zaɓi ne na siyasa ba, a’a, wani muhimmin abu ne don cimma ci gaba, tsaro, da kwanciyar hankali a yankin. A lokacin jawabinsa a taron Ministocin harkokin cikin gida na kasashe membobin ECO na hudu, Pezeshkian ya lura cewa: Kiran wannan taron bayan dogon hutu yana nuna sha’awar kasashen membobinta na inganta hadin kai da hadin gwiwa a muhimman fannoni da ke shafar dangantakar yankuna. Ya bayyana cewa ma’aikatun...
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
Mataimakin Ministan Harkokin Waje Kan Harkokin Siyasa Na Iran Ya Ce: Iran Ba Ta Kula Da Matsin Lamba
Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan Harkokin Siyasa na Iran ya bayyana cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya amma ta yi watsi da duk wata tattaunawar dole da aka tilasta mata Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Harkokin Siyasa na Iran ya jaddada cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya, amma ta yi watsi da duk wata tattaunawa da aka tilasta mata bin duk wani ra’ayin wani bangare guda. Ya jaddada cewa: Warware takaddama cikin lumana zai yiwu ne kawai idan bangarorin biyu suna kan daidaito kuma babu wanda ke neman sanya sharuddansa. A lokacin taron kasa da kasa na hudu na nazarin Iran na zamani, a wani zama mai taken “Iran da Duniya Bayan Yakin Kwanaki 12,” Mataimakin Ministan Harkokin...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tushen haɗin gwiwar Iran da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya shine dokar da Majalisar Dokoki ta zartar Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Tushen hadin gwiwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) shine dokar da Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta zartar. A farkon taron, Baqa’i ya yi tsokaci kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin, yana mai cewa: Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta gudanar da zaman diflomasiyya na biyu a yankin Mashhad, tare da halartar wakilan hukumomin da abin ya shafa daga larduna uku na kan iyaka, tare da wakilan kasashe makwabta. Wannan taron yana da nufin tallafawa da karfafa hadin...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai da dama a gabashin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila sun yi rusa bama-bamai kan gidaje da dama a gabashin Zirin Gaza da safiyar yau Talata, tare da harba manyan bindigogi a yankuna daban-daban, a matsayin ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta. Cibiyar Bayanai ta Falasdinawa ta ruwaito cewa: Tun daga wayewar gari a yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila sun rusa gidaje da gine-gine akalla guda huɗu a gabashin birnin Gaza, Al-Bureij, da Khan Younis, inda aka ji ƙarar fashewar abubuwa masu karfi . Cibiyar ta ƙara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun buɗe wuta, ba tare da wani dalili ba a yankuna da dama na gabas da arewacin Zirin Gaza. Share 0...
Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin gujewa “kisan fararen hula” da dakarun kai daukin gaggawa ke yi Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: shugabannin sojoji sun yanke shawarar barin birnin El Fasher da ke Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan ne, domin kare birnin da ‘yan kasar daga afkawa cikin matsalar kisan kai a hannun Rundunar Rapid Support Forces ta dakarun Kai Daukin Gaggawa. A cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, al-Burhan, wanda ke jagorantar rundunar sojin Sudan, ya ce a wani jawabi da aka watsa ta talabijin a gidan talabijin na gwamnati:...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
Jami’an tsaron hadin gwiwar sun kashe fiye da ’yan bindiga 80 da suka yi yunƙurin kutsawa Jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara. Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin sama da na ƙasa sun gudanar da sumame a dajin Makuku, inda suka yi ruwan wuta kan sansanonin ’yan ta’adda, suka kuma kashe da dama daga cikinsu. Dakarun sun kuma ceto mutane biyu da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. A wata sanarwa da Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kebbi, Abdulrahman Zagga, ya fitar, an bayyana cewa dakarun sun yi nasarar daƙile wani mummunan hari da sama da ’yan bindiga 400 suka kai garin Ribah, inda aka yi musu mummunar ɓarna. An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Rikicin...
An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu. Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira. APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa Lokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci,...
Iran, a matsayinta na ƙasa mai wayewa da wayewa, ta kasance mai himma wajen haɓaka zaman lafiya da tsaro a duniya, in ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Esmail Baqaei a ranar Litinin a gefen wani biki na cika shekaru 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya a Tehran. A cewar Pars Today, Baqaei ya ƙara da cewa a cikin ‘yan shekarun nan, an sami manyan keta ƙa’idodi da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, waɗanda suka yaɗu a duk duniya. Ya yi gargaɗin cewa rashin kula da manufofin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya zaman lafiya da tsaro a duniya cikin haɗari mai girma. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake jaddada buƙatar...
Cibiyar dake kula da ilimin kasa ta kasar Jamus ( GFZ) ta sanar da cewa, girgizar kasar da ta faru a Turkiya ta kai daraja 6.1 a ma’aunin motsin karkashin kasa. Girgizar dai ta faru ne da misalin 10;48 na daren jiya a nisan kilo mita 10 karkashin kasa. An yi karar girgizar kasar a birnin Istanbul da sauran garuruwan da suke zagaye da shi. Ya zuwa yanzu dai babu wani rahoto akan asarar rayuka da girman asarar dukiyar da ta haddasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks...
Sakamakon da aka fitar a jiya Litinin ya bayyana cewa, Alassan Outara dan shekaru 83 ya lashe zaben a kaso 89.77 na jumillar shugaban. Mutum na biyu wanda yake bin Outara a baya shi ne tsohon ministan kasuwanci Jean-Lous Billon da kaso 3%, sai kuma mai dakin tsohon shugaban kasar Simone Gbango da ta sami kaso 2.4%. Tuni dai Billon ya taya Ouattara murnar cin zaben, bayan da ya yarda ya sha kaye. Tare da cewa a karkashin shugabancin Ouattara kasar ta Ivory Coast ta sami ci gaban tattalin arziki, sai dai masu bin diddigin siyasar kasar suna yin suka akan wasa da tsarin mulkin kasar domin bayar da damar ci gaba da tsayawa takarar Alassan Ouarrata. A zaben da...
Kungiyar Dakarun Kai Daukin Gaggawa ( RSF) ta kasar Sudan ta sanar da kwace iko da birnin El-Fashar, da nan ne tungarta ta karshe a yankin Darfur. Hakan dai ya haddasa matsalar dangane da ayyukan jin kai da ceto saboda yadda aka rutsa da dudun mutane a cikin birnin. A jiya Litinin ne dai rundunar ta (RSF) ta kame wani sansanin soja mai matukar muhimmanci a Arewacin babban birnin na yankin Darfur. Garin El-Fasha ne dai sansani mafi girma da sojojin kasar Sudan suke iko da shi a yankin Darfur. Wani rahoton MDD ya ambaci cewa da akwai fiye da mutane 26,000 da suke a tarwatse a cikin birnin na Darfur a tsawon shekara daya da aka dauka ana killace...
Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasar kasa da kasa Dr. Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai kasashe uku a cikin Asiya wadanda suke da ‘yanci da su ne Iran, China da Rasha, kuma suna taka rawa domin samar da sabon tsarin tafiyar da duniya. Dr. Wilayati ya bayyana hakan ne dai a yayin ganawarsa da jakadan China a Iran “Zong Bi Wuu” yana mai kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade da kuma zurfi. Har ila yau Wilayati ya ce alakar kasashen biyu ta ginu ne akan maslaha da kuma girmama juna da kuma cin gashin kai na siyasa, da hakan ya mayar da su, tare da kasar Rasha zama...
Rikicin Jam’iyyar ADC na Jihar Kaduna ya ɗauki sabon salo, bayan da uwar jam’iyyar ta nada tsohuwar Ministar Kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a jihar. Haka kuma jam’iyyar ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna, Bashir Sa’idu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i, a matsayin Mataimakin Shugaban Haɗakar. Da yake jawabi yayin taron manema labarai, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa maso Yamma), Ja’afaru Sani, ya bayyana cewa manufar ADC ita ce haɗa kan shugabannin jam’iyyun adawa a Kaduna domin ƙarfafa dimokuradiyya da shigar kowa cikin harkokin siyasa. Ya ce shugabannin Haɗakar sun ƙuduri aniyar sake farfaɗo da jam’iyyar da kuma haɗa kan jama’a don kawo ƙarshen abin da ya kira “mulkin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa October 27, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025
An kira wani taron musamman a Amurka na tattaunawa tsakanin kasa da kasa mai taken “Kirkire-kirkire da budadden kasuwanci, da more damammakin ci gaba” a birnin Washington na Amurka. Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da ofishin jakadancin Sin dake Amurka ne suka gabatar da taron cikin hadin gwiwa. Kusan baki 100 daga Amurka da Sin, ciki har da masana kan harkokin kasa da kasa, malamai, da wakilan matasan Amurka, sun tattauna batutuwa kamar yadda Sin ke amfani da karfin kimiyya da fasaha mai dorago da kai don karfafa kirkire-kirkire a duniya, da fadada budadden kasuwancinta mai zurfi, da more damammaki ga sauran kasashe. Da wannan taron ne aka fara gudanar da jerin tarurrukan tattaunawar...
Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara. Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar...
Wani rahoto da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, ribar da manyan masana’antun kasar Sin suka samu cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 da muke ciki, ta karu da kashi 3.2 cikin dari. A cewar hukumar ta NBS, masana’antun da ke samun kudaden shiga da suka kai akalla yuan miliyan 20 (kimanin dala miliyan 2.8) a shekara-shekara, sun samu jimillar ribar da ta kai yuan tiriliyan 5.37 a cikin watanni taran. A watan Satumba, ribar da manyan masana’antun ke samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 21.6 cikin dari a kan na makamancin lokacin a bara, kamar yadda hukumar ta NBS ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare...
Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung Zaar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin ko maudu’in wannan taron, wanda shi ne karo na farko bayan sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya da shugaban ƙasar ya yi. An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru Sai dai wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce taron ba zai nasaba da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin tsaro da inganta aikin rundunar sojoji a ƙasar nan ba. Tinubu yayin ganawa da sabbin hafsoshin tsaro Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Shugaba Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da...
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta
A yau Litinin 27 ga Oktoba, kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta ba da rahoton bayanan ayyukan jigilar kayayyakin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agustan bana. Bayanan na nuna cewa, a karkashin jagorar manufofi da bukatun kasuwa, aikin jigilar kayayyakin dake bukatar kankara ya nuna samun ci gaba mai karfi tare da fadada girman kasuwa. Bayanan sun nuna cewa, jimillar da aka samu a wannan bangare a wadannan watanni 3 ta kai tan miliyan 117.3, wadda ta karu da kashi 4.72% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cikin watanni 3 na farko na wannan shekara, jimillar jigilar abincin dake bukatar kankara ta kai tan miliyan 309.3, wadda ta karu da...
A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IEC) ta fitar dazu. Duk da cewa sakamakon zaben bai ƙare ba tukuna, amma Ouatara da ke jagorantar tun 2011 yana kan hanyarsa ta zuwa wa’adi na huɗu a kan karagar mulkin ƙasar, bayan sake zaɓensa a 2015 da 2020. A wannan Litinin, Hukumar zaɓe ta ƙasa da ƙasa (IEC) ta sanar da cewa Alassane Ouattara, mai shekaru 83, na...
Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin. An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru Bayanai sun ce mutuwar ɗan sa-kan ce ta jawo zargin cewa Fulani ne suka yi kisan, lamarin da ya sa wasu matasa suka dunguma suka kai farmaki a sansanin Fulani, inda suka kashe mutum goma a yayin harin. Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya ce, “kuskuren fahimta ce ta sa aka kai harin. “Sun...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki wajen kare tsarin cinikayya tsakanin mabanbantan sassa bisa matukar himma, tare da kasancewa cikin shirin aiki tare da dukkanin sassa, don kare martabar cudanyar mabanbantan sassa bisa gaskiya. Li, ya yi tsokacin ne cikin jawabinsa a yau Litinin, yayin taron shugabanni karo na biyar, na cikakkiyar yarjejeniyar kawance ta cinikayya cikin ‘yanci ta yankin Asiya da Fasifik ko RCEP, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Kazalika, a birnin na Kuala Lumpur, yayin da yake jawabi a dandalin taron kasashen gabashin Asiya karo na 20, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da mabanbantan sassa, wajen ingiza...
A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a babban gidan adana kayan tarihi na “Palace Museum”, albarkacin cika shekaru 100 da kafuwar gidan tarihin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kira da a kara babbar azama wajen kare gidan tarihin, a matsayinsa na wuri dake rike da matsayin kyakkyawar ma’adanar wayewar kai ta kasar Sin. Kazalika, a dai yau din, kamfanin dab’i na al’ummar kasar Sin, ya wallafa wani littafi na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mai kunshe da cikakkun bayanai, da fashin baki kan muhimman batutuwa da aka tattaunawa kan tsaron al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025
Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa Isra’ila a yayin wani rangadin jawabai da ya yi a Amurka. A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR ta ce an tsare Hamdi ne a filin jirgi sama na San Francisco. A ranar Lahadi CAIR ta yi kira da sake shi kuma ta zargi Trump da tsare shi saboda sukar da yake yi wa Isra’ila. Masu goyon baya da masu fafutukar kare hakkin jama’a sun ce tsare Hamdi wani lamari ne na ramuwar gayya ta siyasa ga masu sukar Isra’ila, wadanda ake hukunta su...
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifopa faransa, ta nuna cewa kasha 84 cikin dari na ‘yan kasar basu gamsu ba da Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa. A cewar kuma wannan binciken da aka yi aka kuma wallafa a jaridar le Journal du Dimanche, kashi 16% ne kawai na mutanen Faransa suka “gamsu” da aikinsa a Fadar Élysée, yayin da kashi 84% suka nuna rashin gamsuwa da shi. Kiyasin farin jinin shugaban bai taba raguwa haka ba. Emmanuel Macron, wanda kwarin gwiwarsa ke ci gaba da durkushewa, yanzu ya ba wa kashi 54% na masu jefa kuri’arsa kunya a zagaye na farko na 2022. Rikice-rikicen da aka samu sakamakon rusa Majalisar Dokoki ta kasa, murabus, sannan sake nada Lecornu...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar. Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta. Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata. Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga...
Majalisar tsarin mulki a jamhuriyar Kamaru ta sanar da Paul Biya mai shekara 92 a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 12 ga wata. Mista Biya ya lashe zaben da kashi 53.66% na kuri’un da aka kada, wanda hakan ya ba shi damar shugabancin kasar a wa’adin mulki na takwas. Saidai babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya yi ikirarin lashe zaben, ya samu kashi 35.19% na kuri’un, a cewar alkaluman da aka samu daga cibiyar. Madugun ‘yan adawar ya yi fatali da sakamakon zaben da ya danganta da abin dariya. Rahotanni sun ce tarzoma ta barke a wasu sassan kasar da suka hada da Douala da Garoua bayan sanar da nasarar ta...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025 Labarai Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote October 27, 2025 Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga October 27, 2025
Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wajen taron dandalin tattaunawa na Abuja karo na 6, da ya gudana a kwanakin baya, cewa “Sauyawar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya ta haifar da damammaki ga kasashen Afirka, ta fuskar janyo jari, da karfafa bangaren masana’antu.” Ban da haka, ta ce, “Huldar abota tsakanin Afirka da Sin wani misali ne na samun ci gaban da zai amfani kowa ta hanyar...
An kammala bikin bayar da Kyautar Jaruman Indomie karo na 17, inda aka karrama matasan da suka nuna hazaƙa da jarumtaka, kuma suka zama jakadun Najeriya a fannoni daban-daban. Wannan gagarumin biki ya gudana a birnin Legas a ranar 16 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin shirye-shiryen kamfanin Dufil Prima Foods, masu samar da Indomie Instant Noodles, a wani ɓangare na shirin kamfanin na kyautata dangantaka da al’umma (CSR). Kamfanin ya tabbatar da bayar da kyaututtuka ga Jaruman Indomie — wani girmamawa na musamman ga matasan da suka nuna jarumta da Ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin ƙasar. Taken bikin na bana shi ne “Jaruman da Ba a San Su ba”, inda fitattun matasa uku daga sassan Najeriya suka fito a matsayin zakaru, bayan sun...