2025-11-22@16:20:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4001

«makarantu»:

    Daga Aliyu Lawal  Gwamnatin Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da na masu zaman kansu a fadin jihar sakamakon sace dalibai da aka yi a Makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri a Karamar Hukumar Agwara. Gwamna Mohammed Umar Bago ne ya sanar da hakan a...
    Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko...
    Daga Isma’il Adamu  Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati,  da na masu zaman kansu a fadin jihar biyo bayan kalubalen tsaro da ya addabi makarantun kasar nan. Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu hare-haren sace ɗaliban makarantu da suka faru a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan. Wata sanarwa da...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin...
    Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.” Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da...
    Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja. Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro. Gwamnan Agbu...
    Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya  saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk...
    Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar...
    Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta...
    Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN). Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15....
    Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada...
    Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada...
    Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar. Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a. ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da...
    ’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
    Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu. Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
      Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwo na Gargajiya ta Afirka (CORET) tare da haɗin gwiwar ECOWAS sun hada matasan da aka horar da su da manyan abokan holda don bunkasa kiyo da bunkasa yawan madara a jihohin Kaduna da Jigawa.   A yayin zaman karawa juna sani a Kaduna, Koodinetan Aikin na CORET Dr. Umar...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga,...
    Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasiƙa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 1, irinsa na farko a tarihin jihar. Za a gabatar da kudurin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamban 2025. Wasiƙar, wadda Kakakin Majalisar, Alhaji Jibril...
    Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace dalibai ashirin da biyar daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu. Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe a lokacin da ƴan bindiga suka mamaye makarantar, inda suka kashe wani...
    Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu. Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar...
    Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a...
    Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas...
    a Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani. Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila...
    An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen...
    Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba....
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
    Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO)...
    Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya {IAEA} ya bayyana cewa: Suna tuntubar Tehran kuma masu binciken hukumar sun koma kasar ta Iran Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da komawar masu binciken Hukumarsa ta IAEA zuwa Iran da kuma ci gaba da duba wasu wurare da...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
    Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da...
    Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa...
    Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.   Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin...
    Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane...
    Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil. Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano. Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya...
    Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa...
    “Lokacin da Wike, Makinde, Ugwuanyi, Ikpeazu da Ortom suka kafa G5, bana are da su. Amma duk da haka, Wike abokina ne sosai. Lokacin da PDP ta samu matsala Wike ne ya yi ƙoƙarin tallafa mata,” in ji Anyanwu. Ya ƙara da cewa Wike bai fice daga PDP ba. Anyanwu ya kira taron gangamin PDP...
    “Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari...