Senegal ta karbi wani sansaninta na uku daga hannun Faransa
Published: 18th, May 2025 GMT
Kasar Faransa ta mika iko na sansanin soja na Contre-Amiral Protet ga kasar Senegel, wanda shi ne sansanin soja na 3 da aka mikawa kasar a bana.
An mika sauran sansanoni biyu da suka hada da Marechal da Sanit-Exupery ne a watan Maris din da ya gabata, Kuma dukkan sansanonin na da mazauni ne a Dakar, babban birnin Senegal.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Faransa ya fitar, ta ce an tsara mika dukkan wasu sansanonin dake karkarshin ikon Faransa a Senegal a bana, biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi.
A ranar 31 ga watan Disamban 2024, shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar a jawabinsa na sabuwar shekara cewa, za a bukaci dakarun Faransa su fara janyewa daga kasar a bana.
A shekarun baya bayan nan dai kasashen Afrika sun yi ta kira da janye dakarun Faransa daga kasashensu.
Shi ma a jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara, ya gabatar da shirin ficewar dakarun Faransa daga kasarsa.
Tun tuni daga kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suka raba gari da kasar ta Faransa tare da yanke alakar soji a tsakaninsu, sai kuma kasar Chadi wacce ta bi sahu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
IPOB A Najeriya Ta Jawo Asarar Rayuka Kimani 700 Da Kuma Kudade Kimani Naira Triliyon N7.5 Tun Shekara ta 2021
Mutane kimani 776 ne suka rasa rayukansu sannan kudade kimani naira Triliyon N7.6 ne aka yi a sararsu a cikin shekaru 4 da suka gabata a yankin kudu maso gabacin Najeriya sanadiyyar zaman gida wanda kungiyar IPOB ta tilasta masu.
Jaridar Premium time ta Najeriya ta bayyana cewa rahoton hukumar tsaro na SBM Intelligence ta fitar a watan Mayon da ya gabata ya nuna cewa, da farko Kungiyar ta IPOB ta tilastawa mutanen yankin zama gida na don ganin an saki shugaban kungiyar Namdi Kano, amma daya baya sai ta zarce zuwa yanzu.
Kuma hakan ya hana abubuwan ci gaba da kuma harkokin kasuwanci makarantu da kuma ayyukan gwamnati tafiya.
IPOB dai tana bukatar warewa daga tarayyar Najeriya don kafa kasa mai suna Biafra daga yankin kudu da kuma kudu maso kudu na tarayyar Najeriya.