Yeman ta yi barazanar killace tashar jiragen ruwan Haifa ta Isra’ila
Published: 20th, May 2025 GMT
Yemen ta yi barazanar killace babbar tashar jiragen ruwan Haifa ta Isra’ila, tare da gargadin cewa jiragen ruwa da ke tafiya a can.
“Dukkan kamfanonin da jiragensu ke nan ko kuma suka nufi wannan tashar, ana sanar da su cewa, ya zuwa wannan sanarwar, an saka tashar cikin jerin wuraren da muke son kaiwa hari,” in ji kakakin kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a Yemen Yehya Saree.
Rundunar sojin Yeman ta ce kakaba takunkumi na a matsayin mayar da martani ga yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.
Sanarwar ta ce sojojin Yemen ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar karin matakai na goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma tsayin daka.
Rundunar ta jaddada cewa matakan na Yemen za su zo karshe da zarar an kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Gaza tare da dage shingen da aka yi Zirin.
Tun da farko dama wani babban jami’in kasar Yemen ya gargadi kamfanonin jiragen sama na kasuwanci na kasa da kasa dake zirga-zirgar zuwa filin jirgin sama na Ben Gurion da ke yankunan da Isra’ila ta mamaye a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare na ramuwar gayya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zambiya Ta Kaddamar Da Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Mafi Girma
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp