HausaTv:
2025-05-16@14:51:27 GMT

Iran Tace Ranar Nakba Farawa Ce Na Musibu Ba Karshensu Ba

Published: 16th, May 2025 GMT

Jakadan JMI a MDD ya bayyana cewa ranar Nakba ko musiba ga Falasdinawa, abin bakinciki ba karshen musubar ba ce sai faraway ne, don a yau shekaru 77 da suka gabata kenen da musibar da ta faru da Falasdinawa tana ci gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Amir Sa’id Iravani yaana fadar haka a jiya Alhamis a MDD inda ake taron tunawa da ranar musiba ta falasdina.

Iravani ya kara da cewa taron tunawa da Nakba ta bana ta zo a dai-dai lokacinda Falasdinawa a Gaza suke cikin musiba wacce ba zata yi kasa da ranar Nakba ta shekara ta 1948 ba, ranar da aka kori Falasdinawa daga kasarsu, kuma ranar yahudawan suke bukukuwan kafa HKI shekaru 77 dasuka gabata.

Jakadan yace ranar Nakba ta bana ta zo a dai dai lokacinda HKI take kashe Yara da mata a gaza, tana rusa makarantu da asbitoci tana kashe ma’aikatan MDD da yan jaridu da duk wanda suka ga dama, sannan magoya bayanta suna hana kotuna hukunta wadanda suka aikata lafiya da sauransu.

Iranwa ya bayyana cewa hotunan bidyo da muka gani daya ce kacal daga hotuna masu girgiza zukata na yadda boma-boman HKI suke fadi kan gine0-gine a gaza suna jefa gabba falasdinawa da suka nika.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ranar Nakba

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai.

Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a kai, tare da mayar da hankali wajen habaka bukatu na cikin gida ta yadda ta kaucewa dogaro da kasashen waje, yayin neman ci gaba. Don haka duk wani matsi na Amurka, sai ya fi tasiri kanta maimakon kasar Sin. A ganina, wannan dalili ne ya sa Amurka neman sulhu ta hanyar neman tattaunawa da kasar Sin. Za mu iya cewa, ana maraba da tattaunawar duk da dama can Sin ta sha cewa, yaki ba zai samar da mafita ba, kuma kofarta a bude take a tattauna bisa adalci da sanin ya kamata.

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil Jami’ar Maryam Abacha Ta Rufe Ɗakunan Kwanan Ɗalibai Saboda Aikata Rashin Ɗa’a A Kano

Bisa la’akari da karfinsu na tattalin arziki, Sin da Amurka na taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin duniya da ma harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma tattaunawa ta baya bayan nan da kasashen biyu suka yi za ta taka rawa gaya wajen rage sabanin dake tsakaninsu da aza tubalin zurfafa hadin gwiwa.

Hakika yadda Sin ta tsaya kai da fata, ita ce kadai hanya ta nuna wa Amurka cewa fin karfi ba zai haifar da da mai ido ba, kuma tabbas hakan ya kwatar wa kasashen duniya musamman masu tasowa ’yanci, tare da ba su kwarin gwiwar bijirewa cin zali. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dubban Falasdinawa Sun Fito Kan Titunan NewYork Don Tunawa Da Ranar Musiba ko Nakba
  • HKI Ta Kashe Falasdinawa Akalla 143 A Ranar Tunawa Da Musibar Nakba
  • Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce Amurka Tana Da Hannu Dumu-Dumu A Kisan Kiyashin Gaza
  • Iran za ta gudanar da taro da kasashen Turai a Istanbul kan shirinta na nukiliya
  • Yoro Da De Light Da Heaven Ba Su Yi Atisaye A Man United Ba
  • Wata Kotu A Amurka Ta Bukaci A Saki Wani Malami Mai Goyon Bayan Palasdinawa A Jami’ar Georgetown academic
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Gaza
  • Gwamnati Kaduna Tace Zuba Jarin Da Ta Yi Na Euro Miliyan Dari Da Shadaya Zai Maganin Sufuri A Jihar
  • Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci