Aminiya:
2025-07-03@15:16:22 GMT

An kashe ’yan kasuwa 15 a wani sabon hari a Binuwai

Published: 19th, May 2025 GMT

Aƙalla ’yan kasuwa 15 ne aka kashe a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wasu garuruwa da ke Ƙaramar Hukumar Agatu a Jihar Binuwai.

’Yan kasuwar na kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Oweto da yammacin ranar Asabar lokacin da aka kai musu hari a kusa da garuruwan Ogwumogbo da Okpo’okpolo.

An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja ’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa

Tsohon mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce mutane da dama sun jikkata.

Ya ce mutum biyar aka kashe a kusa da wani ƙaramin rafin da ake kira Abekoko.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu na yanzu, Melvin James, yana wajen jana’izar waɗanda aka kashe lokacin da manema labarai suka kira shi.

Hadiminsa ne, ya ɗauki waya, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ɗora laifin kan makiyaya masu ɗauke da makamai.

Da aka tuntuɓi sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah na jihar, Ibrahim Galma, ya ce bai da masaniya game d harin ba amma zai bincika.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai yi wani ƙarin haske ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Catherine Anene, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton harin ba.

Wannan hari ya ƙara yawan mutanen da aka kashe a Jihar Binuwai daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 17 ga watan Mayu zuwa 174.

Sai dai mazauna yankin sun ce adadin na iya wuce haka, duba da yadda wasu hare-hare ba a kai rahotonsu ba ga hukumomin tsaro.

Yankuna da dama a jihar sun fuskanci hare-hare a baya-bayan nan, ciki har da Gwer ta Gabas, Guma, yankin Sankera (Katsina-Ala, Logo, Ukum), Otukpo, Gwer ta Yamma, Kwande, Apa, Agatu da Makurdi.

Yankin Sankera ne ya fi fuskantar hare-hare, inda aka kashe aƙalla mutum 83 tsakanin 17 zuwa 21 ga watan Afrilu kaɗai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan kasuwa Binuwai hari

এছাড়াও পড়ুন:

Sarayal Kuds Ta Kai Wa  Matsugunin ‘Yan Mamaya Na Sydriot Hari Da Makamai Masu Linzami

Rundunar Sarayar Kudus dake karkashin kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da kai wa matsugunin ‘yan share wuri zauna na Sydriot hari da makamai masu linzami da su ka yi sanadiyyar kashe da jikkata sojojin mamaya.

 Su kuwa kafafen watsa labarun HKI sun samar da cewa, an tsinkayo harba makamai masu linzami guda 3 daga Gaza zuwa Sydriot.

A gefe daya dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da cewa sun kai wasu hare-haren da makamai masu linzami zuwa yankin Q20 a sansanin ‘yan share wuri zauna na ” Nir-Ishaq” da “Miftahim.

Bugu da kari dakarun na “Sarayal-Kuds’ sun sanar da kai wa tankar yaki samfurin Mirkava hari ta hanyar wata nakiya mai karfi akan hanyar Zannah,dake gabashin unguwar Shuja’iyyah a birnin Gaza.

Abinda ya biyo baya shi ne kai wani harin da “Sarayal-Kuds’ ta yi akan sojojin mamaya da suke cikin wani gida, ta hanyar amfani da makamin TBG. Da dama daga cikin sojojin mamayar sun halaka da kuma jikkata.

A ranar Talatar da ta gabata ma dai dakarun “Sarayal-Kuds” sun kai wasu hare-haren na hadin gwiwa da ‘ Kassam’ akan  cincirindon sojojin mamaya a arewacin Khan-Yunus.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sarayal Kuds Ta Kai Wa  Matsugunin ‘Yan Mamaya Na Sydriot Hari Da Makamai Masu Linzami
  • Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya a Sakkwato
  • Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
  • Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya
  • Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
  • Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 
  • Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli
  • Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano
  • CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata
  • An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara