HausaTv:
2025-05-17@10:18:06 GMT

Adadin shahidai a yakin Gaza ya kai 53,119 tun daga Oktoba 2023

Published: 17th, May 2025 GMT

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai 53,119 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Adadin ya karu ne sakamakon wasu hare-haren Isra’ila na baya baya nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 93 wayewar safiyar Juma’a.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, ma’aikatar ta ce an kuma mika wasu mutane fiye da 200 da suka jikkata zuwa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da sojojin Isra’ila suka kai a yankuna da dama.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an sami rahoton mutuwar mutane 109 da jikkata 216, a cewar hukumomin lafiya.

Tun bayan da Isra’ila ta sake koma kai hare-haren a ranar 18 ga Maris, adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa shahidai 2,985 da kuma jikkata 8,137.

A dunkule, tun fara harin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023, adadin wadanda suka mutu a yanzu ya kai 53,119 da 120,214 da suka jikkata.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun rawaito cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa sama da 250 a fadin zirin Gaza musamman a yankin Beit Lahia da ke arewacin zirin Gaza cikin sa’o’i 36 kacal.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kwankwaso ya fice daga NNPP tun a 2023 — Shugaban jam’iyya

Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dokta Agbo Gilbert Major, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ba ya tare da jam’iyyar tun watan Yunin 2023.

Ya ce Kwankwaso ya fice daga NNPP tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.

Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — Atiku

A yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin ‘Daily Politics’ na Trust TV, Dokta Major ya ce:

“Kwankwaso ya zama tarihi a jam’iyyar NNPP. Ya zo a wani lokaci, sannan ya tafi da nasa mutanen.

“Bisa tsarinmu da kuma hukuncin kotu daga Abiya da Abuja, ba ya cikin jam’iyyar tun 2023.”

Shugaban jam’iyyar ya kuma yi bayani game da sauya sheƙa da wasu ‘yan siyasa ke yi daga jam’iyyar, inda ya bayyana cewa yawancin waɗanda suka fice ba su da matsala da NNPP, sai dai da tsagin Kwankwasiyya.

Ya ce waɗanda suka fice har yanzu suna da alaƙa da jam’iyyar.

“Suna ci gaba da faɗa mana cewa ba su da matsala da NNPP, matsalarsu dai ita ce tsarin tafiyar Kwankwasiyya. Wasu na cewa ta koma tafiyar mutum ɗaya, kuma sun gaji da haka,” in ji Major.

Ya ƙara da cewa waɗanda suka fice sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar NNPP, musamman a Jihar Kano, kuma ficewarsu babbar asara ce.

Amma ya ce jam’iyyar na nan da ƙarfinta – duk da ba ta tare da Kwankwasiyya.

Dokta Major ya kuma ƙi bayyana yadda dangantakar Kwankwaso ta ke da fadar shugaban ƙasa.

“Yana da ’yancin zuwa inda ya ga dama. Mu fa mun wuce wannan batun, mu yanzu muna duba gaba ne.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-hare A Kasar Yemen
  • Fiye Da Falasdinawa 300 Ne Su Ka Yi Shahada Da Jikkata Daga Safiyar Yau Juma’a
  • Kwankwaso ya fice daga NNPP tun a 2023 — Shugaban jam’iyya
  • Iran Tace Ranar Nakba Farawa Ce Na Musibu Ba Karshensu Ba
  • Sojojin Yemen Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Babban Filin Jirgin Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Human Rights Watch : Katange Gaza mataki ne na share al’umma
  • Qalibaf : Dole ne Iran da Aljeriya su hada kai don saukaka kai kayan agaji zuwa Gaza
  • Fiye Da Falasdinawa 80 Ne Su Ka Yi Shahada Daga Safiyar Yau Alhamis
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Aiwatar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Gaza