HausaTv:
2025-06-14@14:31:54 GMT

Sharhin Bayan Labarai: Dandalin Tattaunawa Na Tehran

Published: 19th, May 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran.

A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran, don tattauna batutuwan da suka shafi kasashen yankin yammacin Asiya.

Inda shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran suka gabatar da jawaban farko a taron.

An sami halattan baki daga kasashe 53 daga cikinsu akwai jami’an gwamnatoci wadanda suka hada da ministoci  masana da shuwagabannin cibiyoyin bincike da bada shawarori na kasashen duniya da dama.

Daga cikin bakin akwai ministan harkokin wajen kasar Oman Badr bin Hamad Al Busaidi wanda ya fadawa tashar talabijin ta Presstv kan cewa yankin yammacin Asiya a halin yanzu yana fuskantar matsaloli wadanda suke bukatar a tattaunasu tsakanin kasashen yankin. Ya kuma kara da cewa kasar Omman a shirye take ta shiga tattaunawa don fahintar juna ko da da wanda take da sabani sosai da ita ne kuwa. Ministan ya bada misali da rikicin kasar Falasdinu, wanda ya zarce dukka matsaloli yankin yammacin Asiya, har ya zama matsala ta kasashen duniya.

Ya ce: Abinda Falasdinawa suke fuskanta a hannun HKI a halin yanzu ya zama babban matsala da damuwa ga kasashen duniya da dama.

Albusaiti ya bayyana cewa abinda yake faruwa a kasar Falasdinu, bai kamata ya auku ba, ko kuma ba zai faru ba, da anbi hanyar tattaunawa tun lokaci bai kure ba. Ya kammala da cewa “Tattaunawar Tehran” wata dama ce ga wadanda suka yi Imani da tattaunawa a matsayin hanya tilo ta warware matsaloli tsakanin kasashe.

Sai kuma ministan harkokin wajen kasar Tajakisatn wanda ya bayyana cewa kasashen duniya suna bukatar tattaunawa mai zurfi don warware matsaloli masu yawa da take fama da su.

Sirajuddin Muhriddin ya kara da cewa kasashen duniya suna bukatar tattaunawa mai zurfi da kuma gudanar da bincike masu yawa don warware dimbin matsalolin da ake fuskanta da suka shafi tsaro da tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Ministan ya bayyana a cikin jawabinda ya gabatar kan cewa lalle kasashen duniya suna bukatar tattaunawa saboda ganin yadda al-amura suke sauyawa a cikinta da sauri.

Yace wuce gona da iri da tsatsauran ra’ayi wadanda suka kaiwa ga tashe-tashen hankula sun zama babban barazana ga dukkan mutanen a duniya. Ya yi kira ga kasashen duniya su gaggauta daukan bai-daya don magance da kuma kawo karshen kara fadadar wadannan matsaloli.

Ya bukaci a samar da shirin bai daya na samar da tsaro a wannan yankin don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikinsa.

Ministan harkokin wajen kasar Tajakistan ya kammala da cewa, wasu tsare-tsaren da ake da su a halin yanzu a yankin ba zasu iya tabbatar da zaman lafiya da kuma warware matsaloli tsakanin kasashen yankin ba, don haka akwia bukatar tattaunawa mai zurfi a tsakaninsu don cimma wannan manufar.

Sai kuma sakataren majalisar tsaro ta kasar Armenia wanda ya bayyana cewa kasarsa tana kokarin tabbatar da tsawo da zaman lafiya a kasar, da kuma makobta.

Armen Grigoryan ya bayyana cewa shirin gwamnatin kasar na (Drossroad For Peace) wanda aka kaddamar da shi a cikin watan Octoban shekara ta 2023 yana dauke da manufar bude hanyoyin bunkasa tattalin arzikin yankin wanda ya dade yana tseye baya motsawa, ya zama ya samar da cudayya da juna a yankin saboda ci gaban kowa. Ya ce munyi Imani kan cewa wannan shirin yana da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki wanda kuma zai kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Sannan tsohon firai ministan kasar Iraqi Adil Abdulmahdi, a jawabinda ya gabatar a dandalin tattaunawa na Tehran wato “Tehran Dialoque Furum”,  ya ce kasashen larabawa da sauran kasashen duniya duk, sun kasa warware rikicin Falasdinawa da HKI. Ya kuma kara da cewa kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza, wata babbar matsala ce wacce ta girgiza dukkan mai lamiri a cikin zuciyarsa.

Abdul Mahdi ya cewa hatta kotun kasa da kasa ta ICC ta kasa dakatar da kisan kiyashin da HKI take aikawa a Gaza wanda ya nuna irin lalacewra da al-amura suka yi a duniya a yau.

Tsohon firai ministan ya kara da cewa abinda yake faruwa a Gaza, Holocus ne a fili wanda al-amarin bai tsaya nan ba, birane a yankin yamma da kogin Jordan da Lebanon duk suna fauskantar wannan matsalar daga HKI.

Daga karse yayi kira ga kasashen duniya su tashi su nuna cewa sun damu da binda ke faruwa a Gaza, mai yuwa mu kawo karshen wannan kissan kare dangin.

Abdul Mahdi ya rufe da cewa tarihi zata riki wasu da dama da shirun da suka yi a ta’asar da HKI take aikawata a Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ministan harkokin wajen kasar kasashen duniya su bukatar tattaunawa da zaman lafiya ya bayyana cewa kara da cewa tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan man Fetur na Kasar Iran Yace Amurka Ta Kasa Hana Iran Saida Danyen Man Fetur Na Kasar

Ministan man fetur na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana cewa kasarsa zata ci gaba da saida danyen man fetur ga masu sayensa a kasashen waje duk tare da kokarin gwamnatin kasar Amurka na kara kuntatawa kasar a bangaren saida makamashin kasar ga kasashen waje.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya laraba bayan taron majalisar ministocin kasar a nan Tehran.

Ministan ta kara da cewa shirin Amurka na hana Iran saida danyen manta ga kasashen waje zai rugurguje kamar yadda ya rugurguje a baya. Y ace don mun rika mun gano kan zaren lalata duk wani shiri na hana mu saida danyin man ga masu sayan man kasar.

Ministan ya bayyana cewa labara ya zo masa kan cewa gwamnatin Amurka na kokarin kakabawa kasar takunkuman tattalin arziki kan sinadarin Methanol na kasar, shi ma suna aiki a kansa.

Gwamnatin Amurka ta Donal Trump tun watan Fabray run wannan shekarar ta fara wani sabin shiri na takurawa Iran, daga ciki har da maida sayar da danyen man fetur na kasar zuwa sifili.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran : Halin da ake ciki ba zai iya bada damar tattaunawa da Amurka ba
  • Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin
  • Iran ta caccaki kudurin IAEA wanda ta ce yana cike da siyasa
  • Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa: Sabon Tunani Don Wanzar Da Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya
  • Kasashen Iran Masar Da Kuma Omman Sun Gudanar Da Taro A Oslo
  • Ministan man Fetur na Kasar Iran Yace Amurka Ta Kasa Hana Iran Saida Danyen Man Fetur Na Kasar
  • An Gudanar Da Taron Ministoci Masu Daidaita Ayyukan Da Aka Amince Yayin Taron FOCAC
  • Jagora Ya Bambance Tsakanin Majalisun Dokokin Kasashe A Fagen Gudanar Da Ayyukan Kasa
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 8 A Jihar Filato
  • He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa