2025-07-04@18:58:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2619

«Uranium a cikin»:

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin ba ta goyon bayan wani bangare a rikicin Ukraine. Mao, wadda ta bayyana hakan yau Juma’a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, ta ce har kullum matsayar Sin ita ce karfafa gwiwar komawa ga tattaunawar wanzar da zaman lafiya. Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta yi rawar gani wajen ingiza bukatar tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki. Kazalika, a cewarta dukkanin sassan kasa da kasa sun kwana da sanin matsayar adalci, da hangen nesa ta kasar Sin, cewa tsawaitar rikicin Ukraine ba zai haifar da ‘da mai ido ga kowa ba. Har ila yau, a cewar jami’ar, Sin na goyon bayan gaggauta...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars. Ya naɗa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar. An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno “ADC za ta fuskanci matsala wajen zaɓen wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa” Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake gina ƙungiyar kafin tunkarar kakar wasa ta 2025-2026 a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL). A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an yanke hukuncin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon ƙafa. Gwamnatin ta rushe tawagar hukumar wasanni ta jihar tare...
    Ya yi nuni da cewa, jami’o’i na cikin tsaka mai wuya wajen samun sauye-sauye a duniya cikin sauri da kuma bukatu na cikin gida, wanda ke bukatar lallai sai sun sake yin nazari sosai kan tsarinsu, da dabi’unsu, domin samar da ingantaccen muradun al’ummarmu da nahiyarmu. Ya kuma jaddada mahimmancin hangen nesa inda jami’o’i za su zama matattarar kirkire-kirkire, masu inganci da kawo sauyi a zamantakewar al’umma. “Bari in yaba wa Makarantar Tattalin Arziki ta Afirka saboda himma da hangen nesa, ASE ta riga ta nuna kyakkyawar manufa wajen inganta karfin matasan Afirka da daidaita manyan makarantu tare da bukatun juyin-juya halin masana’antu na hudu,” in ji shi. A cikin laccarsa mai taken, “Jami’ar Nijeriya ta Karni na 21: Matsaloli...
    Bayan an rufe sararin samaniyar kasar Iran saboda yaki na kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa kasar a ranar 13 ga watan yunin da ya gabata, a yau Jumma’a a bude zirga-zirgan jiragen saman a duk fadin kasar daga karfe 5 na safe zuwa 6 na yamma daga ranar Jumma’a 4 ga watan July 4, 2025. Sake dawo da zirga zirgan jiragen sama yana daga cikin matakan da hukumomi a Iran suka dauka don dawo da nutswa a cikin kasar bayan yakin kwanaki 12 da HKI. Hukumar zirga zirgan jiragen sama na kasar ta dakatar da sauka da tashin jiragen samane jin kadan bayan da HKI ta awkawa Iran da ya ki a ranra 13 ga watan yuni don lafiyar...
    Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa JMI sabbin takunkuman tattalin arziki ta bangaren man fetur a jiya Alhamis, a dai-dai lokacinda take maganar sake farfado tattaunawa da ita. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto  Scott Bessent sakataren kudi na Amurka yana fadar haka ‘Amurka zata ci gaba da gurgunta tattalin arzikin JMI da dukkan hanyoyin samun kudadenta, har sai ta dawo kan muradunta. Wannan dai yana daga cikin shirin Amurka na takurawa tattalin arzikin kasar Iran har zuwa lokacinda mutanen kasar zasu kasa hakuri su kuma tashi su kifar da gwamnatin JMI daga cikin gida. Wannan ne takunkuman tattalin arziki na farko wanda gwamnatin Amurkan ta dorawa JMI bayan yakin kwanaki 12 da ita da HKI suka dorawa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi,  ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan. Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar...
    Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah. Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa. Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki...
    Kazalika, gazawar Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da kuma sauran hukumomin na jihohi na sauke nauyinsu, hakan ya nuna a zahiri, na irin kalubalen da ake fuskanta, na rashin sauke nauyinsu, na bayar da agajin na gaggawa. Misalii, an ruwaito cewa, a sansanin na ‘yan gudun hijira na Yelwata, musamman yadda suke kwana a kan tandarmin kasa, tare da kokawa da cizon Sauro, ‘ya’yansu ke ci gaba da zama a cikin yunwa, wanda hakan, ya kara harzuka su, fita yin zanga-zangar. Bisa wasu akaluma da aka samu daga Biniwe, sun nuna cewa, a sansanin na Yelwata, an samu haihuwa 15 da kuma mata da suka samu juna biyu, su 122, wadanda kuma suke ci gaba da rashin...
    Taron nay au dai an ba shi taken; Girmama Kwamandan Farmakin ” Wa’adussadiq” za kuma a yi shi ne da marecen yau a birnin Tehran a Husainiyyar ” Fatimatuzzahra ( a.s) dake karkashin rundunar soja ta ” Arrasulul-Muhammad ( a.s). Shi dai Birgediya Shahid Hussain Salami ya yi shahada ne a wani harin ta’addanci da HKI ta kawo wa Iran a ranar 13 ga watan Yuni tare da wasu kwamandoji da soja.
    Daga safiyar yau juma’a, Falasdinawa 17 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren da HKI ta kai wa Falasdinawa ‘yan hijira a yankin Mawasi dake Kudancin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a gabashin birnin Gaza, haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun yi amfani da jirgin sama maras matuki nau’in Code Copter ” wajen bude wuta akan wannan yankin. A cikin unguwar Shuja’iyya kuwa, sojojin sahayoniyar sun tarwatsa da rusa gidajen Falasdinawa. A sansanin ‘yan hijira na Jabaliya dake arewacin Gaza ma dai jiragen yakin HKI sun kai jerin hare-hare masu tsanani da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu. A daren jiya Alhamis ‘yan sahayoniyar sun yi kisan kiyashi akan Falasdinawan...
    Janar Ali Fadi wanda tashar talabijin din Iran ta yi hira da shi a jiya da dare, ya bayyana cewa; Iran tana da damar kera makamin Nukiliya da kuma rufe mashigar ruwan Hurzum. Janar Fadli ya ce; Dakarun na kare juyin musulunci sun lakanci yadda ake kera shi, tare da bayyana fatan cewa kar  makiya su tafka  babban kuskuren da zai tura Iran yin tunanin hakan.” Dangane da batun rufe mashigar ruwan Humuz kuwa, janar Faldi ya ce, suna da damar yin hakan,sai dai kuma ko kadan wannan ba ya cikin manufofin jamhuriyar musulunci. Janar Fadli shi ne mai kula da tafiyar da ayyyuka a tsakanin bangarori daban-daban na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran.
    Dantsoho wanda ya samu wakilicin Babban Manajan a Hukumar ta NPA Femi Oyewole, ya bayyana cewa, Shugaban Hukumar ta NPA, Hukumar ta mayar da hankali wajen ganin cewa, ana kare kimar Tekunan kasar. “Hadurran zuba baraguzan kusan a kurkusa suke, wanda kuma, suke ci gaba da karuwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai matukar bukatar a dakile yadda ake duba baragunzan, a cikin Tekunan, baki daya,” Inji Dantsoho. Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA bata yi kasa a guiwa ba, wajen daukar matakan da suka kamata, domin magance wannan matsalar. “Duba da cewa, muna gudanar da ayyukan NPA yadda ya kamata da kuma bin ka;idojin da ke tafiyar da Hukumar, musamman wajen bai wa kayan Hukumar da ke...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran cin amanar diflomasiyya ce Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana harin da sojojin Amurka suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya a matsayin cin amanar diflomasiyya da kuma cewa wani mataki ne da ba a taba ganin irinsa ba ga tsarin doka da hakkin kasa da kasa da kuma tsarin hana yaduwar makaman nukiliya. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da Ronald Lamola, ministan hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa na Jamhuriyar Afirka ta Kudu, sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya bayan dakatar da hare-haren soji da yahudawan sahayoniyya...
    Kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin Iran sun shirya tsaf don kare juyin juya halin Musulunci da kasarsu A yayin ziyarar da ya kai wa iyalan shahidi kwamandan tsaron cikin gida na kasar Iran Kanal Mohammad Alizadeh; Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Jajirtattun sojojin kasar Iran a shirye suke da dukkanin karfinsu wajen kare kyawawan manufofin juyin juya halin Musulunci da kuma dukkanin yankin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin kowane irin yanayi da kuma fuskantar duk wani mai neman wuce gona da iri. Manjo Janar Amir Hatami, babban kwamandan sojojin kasar Iran, tare da rakiyar Hujjatul-Islam Ahmad Jalili Safat, mataimakin shugaban bangaren rukunan siyasa ta sojojin kasar, Manjo Janar Muhammad...
    Dele Momodu, sanannen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa yawancin magoya bayan jam’iyyar sun fara ficewa daga cikinta, suna barin tsarin jam’iyyar a hannun ministan babban birnin tarayya. Dele ya bayyana hakan ne yayin wani shiri a Channels TV, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabon ƙawancen jam’iyyun adawa da suka rungumi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin fuskantar zaɓen 2027. Momodu ya ce, duk da Wike yana PDP, kasancewarsa a gwamnatin APC na nuna rashin amanna kuma ya janyo rikici cikin jam’iyyar. A cewarsa, “mutane suna barin gawar PDP ga Wike da ƙawayensa kawai.” Ya zargi APC da shirya makirci na tura mutanenta cikin jam’iyyun adawa don rage musu ƙarfi a 2027, yana mai...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai munanan hare-hare kan Falasdinawa da suka rasa gidajensu da fama da masifar yunwa, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan mutane da dama Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan ‘yan gudun hijira da kuma wadanda ke jiran agaji a zirin Gaza, inda a daren jiya zuwa safiyar Alhamis, hare-haren wuce gona da irinsu suka yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama, tare da jikkata wasu baya ga bacewar wai adadi mai yaw ana mutane a karkashin baraguzan gine-gine. Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan fararen hula 11 da suka hada da yara da mata a wani sabon kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata ta hanyar kai hare-haren bama-bamai...
    A yau Alhamis ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya halarci bikin bude dandalin tattaunawa kan zaman lafiya na duniya karo na 13, a jami’ar Tsinghua inda kuma ya gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa, Han Zheng ya bayyana cewa, a halin yanzu an samu babban sauyi a duniya, tare da fuskantar batutuwan kasa da kasa da yankuna da dama, don haka ana fuskantar kalubale a sha’anin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaban duniya. Ya ce, tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama, da kiran samun bunkasar duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kuma kiran kiyaye al’adun duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, sun samar da ra’ayoyin Sin kan daidaita manyan...
    Uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin ya rutsa da su a wasu yankunan Jihar Filato. Uwargidan shugaban ƙasar wacce ta bayyana bayar da tallafin a yayin ziyarar jaje da ta kai jihar a ranar Alhamis, ta ce kuɗaɗen da ta bayar ba na gwamnati ba ne, kuɗin ta ne da ta tara don taimakawa wasu. Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad ’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC “A yau na zo da gudunmawar Naira biliyan 1 don shirin sabuwar Najeriya (Renewed Hope Initiative), ba ni da maƙudan kuɗaɗe, amma abin da nake da shi shi ne in taimaki rayuwar wasu, ba wai in zuba...
    Bashir Ahmad, hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban yana cikin ƙoshin lafiya a birnin Landan. A cewarsa, labarin da ke yawo cewa Buhari na fama da mummunar rashin lafiya har yana kwance a ɗakin kulawa na musamman (ICU), ba gaskiya ba ne. Lakurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato ‘Yan Sanda Sun Hana Yunqurin Fasa Shago a Gombe, Tare da Kwato Babur Bashir ya tabbatar da cewa Buhari ya yi rashin lafiya a baya, amma yanzu yana samun kulawar likitoci kamar yadda ya kamata. “Lamarin ba kamar yadda wasu kafafen labarai ke yaɗa labari suka ruwaito ba, Buhari yana cikin yanayi mai kyau kuma magunguna na aiki a jikinsa,” in ji Bashir. Ya ƙara da cewa suna...
    Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota “Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi. Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki. “Yanzu mutane na so Buhari ya...
    Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota “Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi. Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki. “Yanzu mutane na so Buhari ya...
    Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci maida martani mafi tsanani. Janar Musawi ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta almayaden ta kasar Lebanon Ya kuma kara da cewa a yakin da ya gabata wato wa’adussadik na ukku na watan da ya gabata, sojojin Iran basu fitar da dukkan makamansu su. Ko kuma dukkan karfinsu ba. Don haka idan yahudawan sun  kukura sun sake farfado da yaki da JMI sai sun hadu da martani wanda ya fi na farko zafi, Janar Musavi ya kara da cewa HKI ta dauki shekaru tana tanajin ranar da...
    Dubabban falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan ne gwamnatin HKI ta kora daga gidajensu tun bayan ta fara wani shiri wanda ta kira Katangan karfe a farkon wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kungiyar Doctors without Borders wato MSF a takaice tana fadar haka a jiya Laraba. Rahoton ya kara da cewa HKI tana son korar dukkan falasdinawa da suke rayuwa a yankin yamma da kogin Jordan ne don samun damar kafa kasar Yahudawa zallah kamar yadda suke fata. Rahoton ka kara da cewa falasdinawa a garuruwan Tulkaram Jenin da kuma Nurushamne al-amarin ya fi shafa inda yahudawan suka kore falasdinawa akalla dubu 40,000 daga farkon wannan shekara ta 2025 sun kuma rusa gidajen...
    A jiya laraba ce aka gudanar da taron addu’a da kuma girmama shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka farwa kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron girmamawan ne a masallacin Imam Khomane (q) da ke nan Tehran. Labaran ya kara da cewa shahidan yakin kwanaki 12 dai sun hada da manya-manyan sojojin kasar kwamandan dakarun IRGC shahida Hussain salami, da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Shahid Muhammad Bakri da kwamandan rundunar sojojin Khatamul anbiya (s) da ke nan Tehran Ghulam ali Rashti. Da sauransu. Sai kuma masana fasahar makamashin nukliya guda 6 da kuma wasu fararen hula wadanda...
    Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof  ya bayyana cewa HKI zata gamu da maida martani mafi tsanani idan ta seke farfado da yaki da JMI, sannan sai sun yi nadamar fara yakin kamar yaki da kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibof yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake gabatar da jawabi a taron tunawa da kuma yin addu’a ga shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kawowa kasar. Ya ce HKI ba zata jurewa yaki mai tsawon lokaci ba, saboda Iran ta fi karfinsu, sannan wannan ne yasa gwamnatin Amurka ta shiga yakin, inda ta takaita da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar a fordo da Natanz...
    Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta Jota ya rasu yana da shekara 28 a duniha. Hatsarin ya faru ne a hanyar A-52, kusa da garin Palacios de Sanabria. Jota yana cikin motar tare da ɗan uwansa, André Silva, wanda shi ma ya rasu. Silva ɗan wasa ne da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon kafa ta Penafiel a ƙasar Portugal. Rahotanni sun...
    Aƙalla jami’an tsaro shida ne suka rasu bayan wata arangama da suka yi da ’yan bindiga a yankin Gada Woro a kan hanyar Patigi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a Jihar Kwara. Waɗanda suka rasu sun haɗa da ’yan banga guda biyar da ɗan sanda ɗaya. ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’ Lakurawa sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya a Sakkwato Wasu sojoji biyu, ’yan sanda biyu sun samu raunin harbin bindiga a fafatawar da ta faru a ranar Litinin. Waɗanda suka rasu sun haɗa da Mohammed Nma Dsuru daga Kokodo, Yanda daga Lafiagi, da Ndagi Saraka daga Edogi. Rahotanni sun ce ’yan bindigar da yawansu ya kai ɗaruruwa sun kai wa tawagar jami’an...
    Tsohon kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Muhsin Rizai ya bayyana cewa; Jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei ne ya jagoranci da kuma bayar da umarnin yakin “Wa’adussadiq 3” akan HKI. Dr. Muhsin Rizai wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama shahidai da aka yi a jiya Laraba a babban masallacin juma’a na Tehran ya kara da cewa; A karon farko jagoran juyin musulunci ne ya rika bayar da umarni da kuma jagorantar yadda yaki da HKI ya kasance. Dr. Muhsin Rizai wanda shi ne kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran a lokacin kallafaffen yaki da Iraki, ya kuma ce; An yi aiki tare a tsakanin babbar shalkwatar soja ta “Khatamul-Anbiya” da kuma babbar cibiyar...
    Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa. Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa akan yarjeniyar Nukilar iran shi ne kawo karshen Shirin makamashin Nukiliyar Iran, to kuwa Jallas ta jahilci abinda yake kunshe a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya. Ita dai babbar jami’ar harkokin wajen tarayyar turai Jallas ta rubuta sako a shafinta na X cewa; Ya zama wajibi a bude tattaunawa da sauri da Iran akan yadda za ta kawo karshen shirinta na makamashin Nukiliya, kuma...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Batun makamin kungiyar ta Hizbullah na cikin gida ne, don haka ba za su taba mika makamansu ga abokan gaba HKI ba.  Sheikh Na’im Kassim Wanda ya gabatar da jawabi a jiya Laraba da dare a yayin tarukan Ashura, ya bayyana cewa; Ba za mu taba lamunta da a sa mu cikin kaskanci ba, ba kuma za mu mika kasarmu ba, ko kuma mu aminta da barazana daga wani mahaluki akan mu ja da baya. Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Tattaunawar da ake yi akan makaman Hizbullah wani sha’ani ne na cikin gida, za kuma a warware batun ne a cikin gida, don ba shi da alaka da Isra’ila,...
    Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya. Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta   Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa Shirin Iran na Nukiliya bai iya kawo karshensa baki daya,maimakon haka ma sai ya jazawa Tel Aviv asarar mai yawa da kuma karfafa kishin kasa a tsakanin Iraniyawa.” Har ila yau, rahoton mujallar ta “”Foreign Policy” ya ci gaba da cewa; Asarar da aka yi a Isra’ila, tana firgitarwa”,amma a cikin Iran babu cikakken bayani akan girman barnar da aka yi- da hakan yake a...
    Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Kwalajiya da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum 15. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da mutum ke sallar Azahar. NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ramuwar gayya ne bayan da al’ummar ƙauyen suka daƙile wani hari da aka kai musu kwanakin baya, inda suka kashe ’yan ta’addan Lakurawa uku ciki har da wani jagoransu. A wannan sabon harin, ’yan bindigar sun dawo da yawa inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi. “Muna...
    Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su. Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta dakatar da duk wani tallafin makamai da take bai wa Ukraine din. Hamas ta karɓi tayin tsagaita wuta a Gaza Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada hare-harenta a kan kasar, yayin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza yaki tsakanin kasashen da...
    Ta ce, yayin ziyarar, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai zurfafa musayar ra’ayoyi tare da jagororin kasar Masar, game da ciyar da alakar sassan biyu gaba, da zurfafa hadin gwiwa mai samar da gajiya, da batutuwan dake jan hankulan sassan biyu.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun kuduri aniyar kare kan iyakokin Iran da tsaron kasar da kuma al’ummarta Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce: “Suna goyon bayan zaman lafiya, kuma ba su amince da yaki ba, amma a lokaci guda kuma, suna tabbatar da aniyarsu ta kare kan iyakokin Iran da tsaron kasarta da kuma al’ummarta.” A yau, Laraba ne, Shugaban kasar Iran Pezeshkian ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sadarwa, inda ya jaddada babban kudirin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na kare kan iyakokin kasar da tsaro da al’ummar kasar. Yana mai jaddada cewa: “A tushen al’adu da wayewar Iran, suna da gogewa da yawa wajen rage wahalhalun da mutane ke fuskanta.” Shugaban ya kara da...
    Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic. A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar. A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar...
    Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin. Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba,...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar ta Iran. Riyabkov ya shaidawa manema labarai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow cewa: “Za su karfafa hadin gwiwa a aikace tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa: Dole ne a karfafa karfin tsaron kasar Iran, saboda Rasha tana da gogewa mai kima a wannan fanni, kuma za ta ci gaba a kan hakan.” A ofishin jakadancin...
    Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a zirin Gaza tun da sanyin safiyar Laraba. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Akalla fararen hula 6 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai harin bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis. Sannan wasu Fararen hula 10 da suka hada da kananan yara suka...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum, mai shekaru 35 daga ƙauyen Kunji da ke Kwadon, bisa zargin mallakar jabun kuɗi. Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama Kawu ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025, a ofishin ’yan sanda na Lawanti, sannan aka kai shi ofishin Amada domin ci gaba da bincike. Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba Ya ce an samu dalar Amurka 1,000 da ake zargin na bogi ne (kimanin Naira miliyan 1.5), da kuma Naira 10,000 a cikin kayansa. A yayin bincike, Kawu ya amsa cewa kuɗin na wani mutum ne. ’Yan sanda sun ce suna ci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jajanta wa mutanen da ambaliya da guguwa suka shafa a ƙananan hukumomin Damboa da Askira-Uba. A cikin kwanakin da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haifar da ambaliya a ƙauyukan Wovi da Gumsuri na Damboa. Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu Wannan ambaliya ta yi sanadin mutuwar mata biyu, kuma ta lalata gidaje da raba mutane da muhallansu. A wani ɓangare kuma, guguwa mai ƙarfi ta afka wa garin Rumirgo da ke Askira-Uba, inda ta lalata gidaje da dukiyoyin jama’a. Dauda Iliya, mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar da...
    “Ba za su samu tayin da ya fi wannan ba abu zai ƙara muni idan suka ƙi.” Har yanzu babu martani daga jami’an Isra’ila kan iƙirarin Trump ba. Tattaunawar neman tsagaita wuta ta tsaya cak tun watanni da suka gabata saboda rashin jituwa kan matakin da za a ɗauka bayan an daina faɗa. Isra’ila tana son ta ci gaba da samun damar kai farmaki idan ta ga dama, amma Hamas tana so a daina faɗa gaba ɗaya. Ana sa ran Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai kai ziyara fadar White House a mako mai zuwa. Trump ya ce zai yi magana da Netanyahu domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin. A farkon shekarar nan, wani ƙoƙari na tsagaita wuta ya rushe a...
    Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da kammala dawo da dukkan  alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana gida Najeriya daga kasar Saudiyya. A cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Laraba, ta ce jirgin karshe dauke da alhazai 88 ya bar birnin Jiddah da misalin karfe 10:30 na safe dauke da alhazan jihar Kaduna da Katsina. Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta A cewar hukumar, hakan ya kawo karshen jigilar da aka shafe kwana 20 ana yi tun ranar 13 ga watan Yuni. A sakonsa na bankwana ga alhazan,...
    Babbar Kotun Jihar Filato da ke zamanta a Jos, ta yanke wa dalibin nan na makarantar GSTC Bukuru, Odey Emmanuel, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe malamin makarantarsu a kan abinci. Alkalin kotun, Mai Shari’a S.J. Bakfur, ya ce an sami Odey ne da laifin na kisan kai wanda kotun ta ce ya saba da tanade-tanaden sassa na 188 na 189 na kundin dokar manyan laifuffuka ta jihar Filato ta shekara ta 2017. Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu A cewar alkalin, masu shigar da kara sun gabatar da hujjojin da suka iya gamsar da kotun cewa wanda ake zargin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga mutanen kasar da daukaka. Don haka gwamnati mutanen kasar ba zasu taba yarda a barshi ba. Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da tashar talabijin ta CBS news na kasar Amurka dangane da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar a cikin watan yuni da ya gabata. Hare-haren  da aka kaiwa kasar a dai-dai lokacinda take tattaunawa da Amurka. A wani bangare a maganars Aragchi ya bayyana cewa baya ganin Iran zata farfado da tattaunawa da kasar Amurka nan kusa. Ya ce: Idan har zamu sake shiga tattaunawa da...
    Shugaban tawagar Iran a kungiyar hada kan majalisun dokokin kasashen duniya ya bukaci kungiyar ta yi tir da HKI saboda hare-haren da ta kai mata wanda ya keta dokokin kasa da kasa, ya kuma bukaci a koreta daga kungiyar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manoorchehr Mottaki yana fadar haka a wata wasikar da ya aikewa shugaban kungiyar majalisun dokokin ta duniya wato IPU, shugaban Tulia Ackson, ya ce abin  fata shi ne kungiyar zata yi tir da HKI kan sabawa doka ta 2(4) na MDD. Har’ila yau Mottaki ya bayyana cewa yana fatan Ackson zai sa a jingine samuwar HKI a kungiyar. Ya ce majalisar majalisun ta tattauna dangane da hare-haren Amurka da HKI kan kasar...
    Firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia assudani ya bayyana cewa kasarsa ta shigar da karar HKI a gaban kwamitin tsaro na MDD saboda keta hurumin sararin samaniyar kasar don kaiwa kasar Iran hare-hare. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sudani yana fadar haka, ya kuma kara da cewa HKI ba tare da neman izinin gwamnatin kasar ba a cikin yakin kwanaki 12 da JMI ta shiga sararin samaniyar kasar daga nan kuma ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin da kuma cibiyoyin fararen hula daga kasar ta Iraki. Duk ba tare da amincewar kasar ba. Firai ministan ya yi allawadai da hare-haren ya kuma bukaci a huklunta HKI kan hakan. Y ace kasar Iraki bata da garkuwan sararin...
    Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta. Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.
    Cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; a Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Hassan Abdullahi, Daraktan Tsaro na Cikin Gida a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), wanda ya wakilci NSA. Wasu fitattun malamai na addinin Musulunci da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jiddah sun haɗu da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Modibbo, tare da Ambasada Mu’azzam Ibrahim Nayaya, da Manjo Janar Adamu Hassan,...
    Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci a sake komawa teburin tattauna shirin nukiliyar Iran cikin gaggawa, inda take neman hadin kai a tsakanin Tehran da kuma Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya IAEA. Babbar jami’ar diflomasiyyar EU Kaja Kallas ta shaida wa Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Iran, Abbas Aragchi cewar Brussels a shirye take ta shige gaba don ganin an koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran bayan hare-haren Amurka a tashoshin makamashinsu. HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza Bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarho da jami’ar ta yi da Mista Argchi, ta wallafa a shafinta na X cewar ya kamata a koma tattaunawa...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CBS, Araqchi ya yi tsokaci kan ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana iya komawa tattaunawa da Iran a cikin wannan mako: Araqchi yana mai mayar da martini da cewa: “Ba ya jin za a dawo da tattaunawar cikin gaggawa.” Ya kara da cewa: “Kafin yanke shawarar komawa kan tattaunawar, dole ne Iran ta fara tabbatar da...
    Wakilan kasashen duniya a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna girmamawa ga wadanda suka yi shahada a harin wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Iran Masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka da wakilan kasashe daban-daban a Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da bayanai kan mutanen da suka yi shahada a hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran ta hanyar halartar hedkwatar wakilan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya. Daruruwan masu fafutukar neman zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka ne suka hallara a hedkwatar tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin New York a ranar Litinin din wannan mako don karrama shahidan...
    Magajin garin birnin Tehran ya bayyana cewa: Karyar ‘yan sahayoniyya ya tonu na cewa ba su kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran ba Magajin garin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ali-Ridha Zakani ya tabbatar da cewa: Karairayi da ‘yan sahayoniyya suke yadawa dangane da rashin kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran a fili yake karara. Yana mai nuni da cewa akwai kwarararn dalilai da ake da su wadanda suke fallasa karyar wadannan ikirari. A cikin bayanansa, Zakani ya ce: Dalilai kan wadannan karairayi su ne kaburbura gawawwaki da suka hada da fili mai lamba ta 42 a makabartar Al-Jannar – Zahra da ke babban birnin Tehran. Ya...
    Kotu a kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Ayatullah Baqir Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda Hukumar tsaron kasar Iraki ta sanar a ranar litinin cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan wadanda suka aiwatar da zaluncin kisa kan Ayatullahi Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa Alawiyya Bint al-Huda. Ofishin yada labarai na hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta yanke hukuncin kisa kan masu laifin Sa’adoun Sabri da Haitham Abdul Aziz, bayan da aka tabbatar da cewa suna da hannu wajen aiwatar da hukuncin kisa kan Shahadar Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr da ‘yar uwarsa, Alawiyya Bint al-Huda a...
    Mummunan kisan kiyashi kan ‘yan darikar Alawiyyan Siriya, kuma wadanda aka yi wa kisan gilla a kasar a watan Maris sun kai mutane 1,479 A cikin binciken da ya yi na baya-bayan nan, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cikakkun bayanai na kisan gillar da aka yi tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris din wannan shekara ta 2025, inda aka kai wa ‘yan darikar Alawiyya hare-hare a yankin gabar tekun Siriya. Binciken ya tabbatar da mutuwar Alawiyawa 1,479 da bacewar wasu da dama a wurare daban-daban guda 40, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen hankula da daukar fansa kan tsirarun mabiya mazhabobin Musulunci a kasar ta Siriya. Kamfanin dillancin labaran reuters ya wallafa binciken nasa ne bisa...
    Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da ƙaddamar bincike a game da harin da dakarunta suka kai kan wata cibiyar intanet da ke yankin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗimbin fararen hula a jiya Litinin. Hukumar kare lafiyar fararen hula ta Falasɗinu, ta ce wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta harba a jiya Litinin sun faɗa kan kasuwar kwamfuta ta ‘Al-baqa’ da ke gaɓar teku da ke birnin Gaza, kuma a wannan cibiyar kaɗai mutane 24 ne suka rasa raukansu. Ɗaya daga cikin masu magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, tabbatas sun kai hare-hare kan wurare da dama da dakarun Hamas ke fakewa don gudanar da ayyukansu a Gaza, to...
    Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi. “Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka...
    Bayanai daga makusantan fitaccen attajirin nan da ya riga mu gidan gaskiya, Alhaji Aminu Ɗantata sun nuna cewa an ɗage jana’izarsa da aka shirya gudanarwa bayan sallar La’asar a ranar Talata. Yanzu an mayar da jana’izar zuwa bayan Magariba a haramin birnin Madina. Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu A wata zantawa da ya yi da BBC, Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya bayyana cewa tuni gawar Alhaji Aminu ta isa birnin na Madina. “Alhamdu lilLah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya...
    Kakakin gwamnatin JMI ta bayyana cewa a dai-dai lokacinda Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar , babu wata tattaunawa da Amurka nan kusa, duk tare da cewa Amurkawan sun bayyana cewa za’a ci gaba da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin gwamnatin kasar Iran Malama Fatimah Muhajirani tana fadar haka a jiya Talata, ta kuma kara da cewa, babu wata rana da aka sanya na tattaunawa da Amurka kuma mai yuwa babu wata tattaunawa da ita nan kusa. Fatima tana maida martani ne ga wata sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayara na, na cewa nan kusa zasu sake farfado da tattaunawa da JMI.  Tehran dai ta bayyana cewa bata bukatar wani...
    Malaman addinin musulunci daga mazahabar sunna kima 1300 sun tabbatar da cewa gwagwarmaya da HKI wajibi ne a addinin musulunci kuma wajibi ne a Sharia. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanin da malaman suka fitar bayan taron da suka gudanar na cewa tallafawa falasdinawa wadanda HKI take kashewa wajibi ne a sharia. Kuma suna kira ga dukkan malaman sunnan su gane haka su kuma bayyanawa sauran musulmi musamman ahlussa kan cewa jihadi a kan yahudawa sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasar Falasdinu wajibi ne ga wanda yake da ikon  hakan. Bayanin ya kara da cewa abinda Falasdinwa suka yi a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023M da kuma fara yakin Tufanul Aksa yana dai...
    Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Major General Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a taron addu’a da kuma girmma marigayi Manji Janar Muhammad Baqiri babban hafsan hafsoshin kasar wanda yayi shahada a ranar Jumma’a 13 ga watan Yunin da ya gabata. Ya kuma kara da cewa babban shaitan da kuma karamin shaitan duk zasu halaka sun kasa kaiwa ga bukatunsu a yankin kwanaki 12 da suka...
    Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 22 ga watan Yulin wannan shekara domin sauraron bukatar ba da belin da Tukur Mamu, da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci Mai shari’a Mohammed Umar ya tsayar da ranar ne biyo bayan dage shari’ar da lauyan Manu, Johnson Usman, SAN, ya nema, domin ba shi damar yin nazari tare da ba da amsa da ya dace kan karar da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya shigar a kansa. A cikin bukatar da Mamu ya gabatar a jiya Litinin 30 ga watan Mayu, ya nemi a bayar da belinsa dsaboda yanayin rashin lafiyarsa. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan...
    Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya.  Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta taba amfani da Kalmar ‘dakatar da fada ba” a mastayin zabi.  Haka nan kuma ya ce; ‘Yan sahayoniya ba wadanda za a amince da su ba ne, balle gaskatawa, ba a cikin Iran ba, balle kuma a kowane wuri a duniya.”  Shikarci ya kuma yi ishara da cewa; sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwan fiye da kowane lokaci a baya, don haka duk...
    Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin dala biliyan 51.26. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar yin aiki tukuru wajen aiwatar da cikakkun manufofi, na ingiza managarcin jagorancin jam’iyyar bisa kyawawan akidu. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin tsokacin da ya yi, lokacin da yake jagorantar taron nazari na jami’an hukumar siyasar na kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Isra’ila ta bayyana shirin ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen Siriya da Lebanon da suka daɗe ba sa ga maciji da juna a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan na zuwa ne bayan samun lafawar rikici tsakanin Isra’ila da Iran. Kasar Isra’ila ta ce za ta ƙulla hulɗa da ƙasashen da suka daɗe suna zaman doya da man ja, amma ta ce babu batun tattauna makomar tuddan Golan da ta ƙwace daga hannun Siriya. Zan yi takara a Zaɓen 2027 — Peter Obi An sanya dokar hana fita a Kaduna Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar wanda ya bayyana hakan a wannan Litinin din ya ce ƙasarsa tana da yaƙini kan karya lagon ƙasar Iran lokacin fito na fito na tsawon...
    Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yi watsi da bangaren rahoton kwamitin SAGO, na masana kimiyya mai bayar da shawara game da asalin kwayar cutar da ta haddasa annobar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce a ranar 27 ga watan Yunin nan, kwamitin SAGO, ya wallafa wani rahoto game da tushen kwayar cutar SARS-CoV-2, wadda ta haddasa barkewar annobar COVID-19. Sanarwar ta ce, duk da yake bincike mai zaman kansa da kwamitin SAGO ya gudanar bai nuna wata sabuwar shaida game da asalin kwayar cutar ba, bai kuma bayyana wani abu da ya saba da sakamakon binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO na...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
    Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya. A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta...
    A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya. A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta mutunta haƙƙin kasashe da guje wa ɗabi’a nuna fuska biyu a fagen ayyukanta da...
    Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce gona da iri kan Iran, kuma har yanzu Amurka ba ta dauki wani mataki ba kan wannan batu. A wata hira da tashar BBC game da batun tattaunawar makamashin nukiliyar Iran da Amurka: Takht-e Ravanchi ya ce: “Sun ji daga Amurka cewa a shirye take ta ci gaba da tattaunawar, amma har yanzu ba a tsayar da ranar ba, kuma Iran ba ta amince da...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar ta dakatar da hadin gwiwa da hukumar IAEA dole ne aiki da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana a wani taron manema labarai cewa: Dole ne hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yi aiki nesa da batun siyasa, yana mai nuni da cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, dole ne yin aiki da ita. Ya ce wannan doka ta tana nuna damuwa da fushin al’ummar Iran ne dangane da hare-haren wuce gona da iri da aka kaiwa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran da kuma kisan gillar da aka yi...
    A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya. Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.” Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar. Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi...
    Iran ta bukaci gudanar da binciken gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai gidan kurkukun Evin A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar, jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike mai tsanani kan harin da ‘yan sahayoniyya suka kai gidan yarin Evin da ke birnin Tehran. A cikin wasikar, Irawani ya rubuta cewa: Wannan harin da aka kai a ranar Litinin, 23 ga watan Yunin wannan shekara ta 2025, an nufi wani gidan yarin farar hula da gangan, wanda hakan ya sabawa dokokin kare hakkin...
    Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da wasu larduna masu iyaka da shi da ke kudu maso yammacin kasar Sin sun fuskanci mamakon ruwan sama tun daga ranar 18 ga watan Yuni, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa, inda lamarin ya fi muni a yankin Rongjiang. Mahukuntan yankin sun raba yankin zuwa kashi bakwai a matsayin wadanda ambaliyar ta fi shafa tare da kwashe mazauna zuwa wasu manyan wurare masu...
    Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa. Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar. Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa. Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus...
    Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar. Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin, wacce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe HOTUNA: Sabon shugaban rikon APC APC ya jagoranci taron Majalisar Gudanarwa A baya, Ma’aikatar Lafiya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 606, sannan mutane 5,332 da suka jikkata. Jahangir ya ce hare-haren Isra’ila kan gidan yari na Evin da ke Arewa maso Yammacin...
    Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad.   Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini.   Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
    Sabon Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Ali Bukar Dalori, ya shiga ofis, inda a halin yanzu yake jagorantar taron Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar.
    Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran  yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da ministan tsaro na kasar Saudiya Yerima Khalid bin Salman, ya kuma kara da cewa HKI ba kasashe abin amincewa ba. Musawi ya ce sojojin JMI a shirye suka su dakile dukkan hare-haren da HKI zata kawo nan gaba. A wani bangare kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasa da kasa ta kuma MDD...
    JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI. Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan...
      Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus.   Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano.   Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan.   Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari.   Ya ce, kafafen yada labarai sun...
    A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94. Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano. Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina...
    ‘Yan sandan Tehran sun sanar da kama wani dan leken asirin kungiyar leken asirin Isra’ila ta “Mosad” a cikin daya daga tasoshin jiragen kasa na birnin Tehran. Dan leken asirin wanda aka watsa furucin da ya yi, ya bayyana cewa aikinsa shi ne kera jiragen sama marasa matuki da kuma ‘yan kananan jirage, a yammacin Tehran bisa umarnin wadanda su ka dauke shi aiki masu alaka da Mosad. Haka nan kuma ya ce, ya tattara bayanai akan wasu muhimman wurare da cibiyoyi,musamman wadanda su ka shafi yadda naurorin kariyar samaniyar saman Iran suke aiki, tare da aikewa da su zuwa kasashen waje. Majiyar ‘yan sandan ta ce, an kama mutumin ne bayan da aka dade ana bin diddiginsa da kuma...
     Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu ne sannu a hankali zurfinsa yake bayyana. A jiya Lahadi ne matatar man fetur ta Haifa ta sanar da cewa; Wani karamin sashe nata ne zai fara aiki, saboda hare-haren makamai masu linzami na Iran.  Matatar man fetur din wacce ake kira da sunan : “BAZAN” ta ce sai zuwa wata Oktoba ne ake sa ran cewa za ta koma aiki baki daya. A ranar...
    Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar  musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta da Pakistan din ta dauka akan harin da HKI ta kawo wa Iran, haka nan kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga Iran. Janar Musawi ya  kuma yi ishara da matsayar gwamnati da al’ummar Pakistan akan ta’addanci na HKI, kamar kuma yadda ya bayyawa kwamandan sojojin kasar ta Pakistan yadda Amurka ta taimakawa HKI a tsawon kwanaki 12 na yakin.  Har ila yau, janar Musawi ya ce; Tare da cewa mun rasa kwamandoji masu girma a farkon harin ta’addancin, sai dai kuma duk da haka, mun hana ‘yan sahayoniyar cimma manufofinsu. A farkon yakin dai,...
      Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.   Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar.   Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu. Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.” Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara...
    Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Seyyed Abdurrahim Mousawi ya bayyana cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan kasar Iran ya zo ne duk da kamewa da kai zuciya nesa da Iran take yi, kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa ba na...
    Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni. Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar. Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne...
    Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya Rahotonni sun bayyana cewa:  Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya.  Wannan ya zo daidai da wani sintiri da sojojin mamayar Isra’ila da ke ci gaba da yi a kauyen Kodna da ke cikin karkarar Quneitra, ba tare da wata arangama ko gargadi daga mahukuntan Siriya ba. Ana ci gaba da yin shiru a hukumance dangane da irin wadannan tsauraran matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a kan iyakar kasar da tuddan Golan na Siriya da ta mamaye, lamarin da ya sanya ayar...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
    Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin farashin abubuwa da dama da zai hau sama.  A cewar masana, Gabas ta Tsakiya da ke samar da akalla kashi 34 na mai a duniya da kashi 18 na gas, gumurzun kasashen biyu ya haddasa farashin danyen mai tashi da kashi 10, yayin da gas ya kara da kashi 7. Haka ma akwai fargabar Isra’ila na iya illata harkokin mai da jigilarsa a mashigar Hormuz...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki ya bayyana fatansa gare su, bayan da ya ziyarci kauyen cikin watan Yulin shekarar 2021. Ya ce, bayan fahimtar cewa kauyen ya samu sabbin sauye-sauye a shekarun baya-bayan nan, kuma mazaunansa sun samu karin kudaden shiga, ya yi matukar farin ciki. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan karkashin manufofin JKS, mazauna kauyen za su gina yankunan kan iyakoki, tare da kyautata rayuwar al’ummunsu...
    Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna. Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa mai daraja ta biyu a Ingila wato Championship. Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an cimma matsaya tsakaninta da Van Nistelroy ne bayan tattaunawar da suka yi. A ƙarshen watan Nuwamban da ya gabata, bayan da ta kori Steve Cooper a lokacin da suke matsayi na 16 a gasar Firimiyar bara, Liecester City ta ƙulla yarjejeniya da Van Nistelrooy, kwangilar da ba za...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya tsaya kanta, mutumtum ne wanda yake tupka da warwara a lokaci guda. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kakakin  majalisar dokokin yana fadar haka a zaman majalisar dokokin kasar a jiya Talata. Qalibof ya kara da da cewa kalaman da Trump yake fada na kaskanta shugabannin JMI yana daga cikin yakin kwakwale ne da mutanen kasar Iran. Kuma yakamata ya sani, kuma wadanda suke tare da shi su sani mutanen Iran zasu ci gaba da kare kansu su kuma yaki da wadanda suke shishigi a kan kasarsu. Daga karshen yan siyasan makiya...
    Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta ki ta rattaba hannu kan yarjeniyar da gwamnatin shugaba Trump yake so kan shirinta na makamashin Nukliya ba, abinda muke buklata kawai shi ne mu aika da wasika kan a dawoda takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, wadanda suka hada da na makamai, kudade, da kuma fasaha wadanda aka dagesu shekaru 10 da suka gabata. Bayanda Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA a shekara 2018...
     Kwamitin koli na  tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran.  Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar musulunci ta Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa; Karkataccen rahoton da hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya gabatar ne ya zama abinda HKI ta fake da shi wajen kawo wa Iran hari na ta’addanci. Azizi ya kara da cewa; Iran ta sha nanata cewa, shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne, kuma yana gudana ne a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya. Ibrahim...