Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da naɗin sabbin sakatarorin ƙananan hukumomi guda 21 a faɗin jihar.

 

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala ya sanya wa hannu, wacce aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.

 

Ya bukaci sabbin sakatarorin da aka naɗa da su yi aiki tukuru don ganin nasarar wannan gwamnati da kuma ci gaban jihar gaba ɗaya.

 

Daga Abdullahi Tukur

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

 

Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.

A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.

Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da  biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.

Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?