Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai
Published: 6th, February 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura.
Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara.
Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar AbujaGobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Ya buƙaci makarantu da su fifita tsaro da kula da lafiyar ɗalibai a kowane lokaci.
A yayin bincike, rundunar ‘yan sandan Zamfara ta ce tana ƙoƙarin gano musabbabin tashin gobarar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin.
Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata.
Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum.
Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran bukatun yau da kullum.
Yace ana samun ribar kimanin naira dubu goma zuwa ashirin a kowace rana daga siyar da kifin ga matafiya da kuma baki masu kai ziyara garin.
A don haka, Umar yayi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta yi yashen madatsar ruwan saboda a samu karin kifaye da kuma ruwa da za a iya amfani da shi domin noman rani.
Shi ma a yayin tattaunawa da Dagacin Warwade, Malam Musa Ado, ya ce madatsar ruwan tana samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da hana tafiya zuwa cirani a sauran yankunan kasar nan da sunan yin sana’o’i.
Ya ce matasan yankin suna gudanar da sana’ar kamun kifi da kuma nomar rani da ta damina.
Sai dai kuma, Malam Musa ya koka kan rashin samar da injinan noman rani da kuma Malaman gona kamar yadda ake yi a gwamnatocin baya.
Kazalika, yace a ‘yan kwanakin baya gwamnatin jihar Jigawa ta kai ziyara kauyen inda ta sanar da cewar Bankin duniya zai samar da wasu kudade ta hannun gwamnatin tarayya wanda za’a baiwa gwamnatocin jihohi domin yashewa tare da gina burtuloli da hanyoyin noman rani.
Bisa haka ne dagacin yayi kira ga gwamnatin jihar da ta fara yin garambawul a madatsar ruwan domin a baiwa mazauna yankunan damar amfani da shi.
A shekarun baya dai, gwamnatin jihar Jigawan ta samar da irin kifaye guda dubu Dari uku domin inganta samar da kifi a yankin.
Usman Mohammed Zaria