Mutane 7 Sun Mutu 11Sun Jikkata A Hadarin Mota A Niger.
Published: 19th, May 2025 GMT
Mutane 7 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu goma sha daya suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Essa dake kan titin Agaie Badeggi a karamar hukumar Katcha a jihar Neja.
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Minna.
A cewar Abdullahi Baba Arah, motar na dauke da hatsin gwamnatin tarayya, da kuma wata mota dake dauke da wasu fasinjoji 36, wadanda dukkansu maza ne zasu jihar Kano daga jihar Legas suka yi toho mu gama a lokacin da hatsarin ya afku.
Hatsarin ya afku ne da misalin karfe uku na safiyar yau, sakamakon rashin kyawun hanya a layin Lambata, Bida.
Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an tabbatar da mutuwar mutane 7, 11 da suka samu munanan raunuka, yayin da mutane 5 suka samu kananan yara.
Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an kai su cibiyoyin lafiya na Badeggi da Agaie, wasu kuma abokan aikinsu sun tafi da su yayin da ‘yan uwansu kuma suka tafi da wadanda suka mutu domin yi musu jana’iza.
A halin da ake ciki dai hukumar NSEMA ta gudanar da aikin bincike da ceto tare da matafiya da wasu mutanen kauyen da ke kusa da inda lamarin ya faru.
PR ALIYU LAWAL
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hadari
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon golan Super Eagles, Peter Rufai ya mutu
Tsohon mai tsaron ragar tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Peter Rufai, ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 61 a doron kasa.
Super Eagles ce ta bayyana rasuwar golan cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a wannan Alhamis din.
Harin Filato: Remi Tinubu ta ba da gudummawar Naira biliya 1 Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir AhmadFitaccen golan wanda yana cikin tawagar Super Eagles da ta lashe Kofin Nahiyyar Afirka na AFCON a shekarar 1994 ya rasu ne bayan fama da jinya.
Marigayi Peter Rufai wanda ake yi wa inkiyar Dodo Mayana, ya buga wa kungiyar Farense ta Kasar Portugal kusan wasanni 60.
A lokacin rayuwarsa, Peter Rufai ya mallaki makarantar koyon kwallon kafa da ake kira ‘Dodo Mayana’ a Jihar Legas, inda ake zakulo yara daga fadin Nijeriya a taimaka musu.
Peter Rufai ya yi makarantu da dama, yana kuma da takardu da shaidar karin ilmi na Diploma tare da Hukumar Kwallon Kafar Turai ta UEFA.
Tsohon golan ya karanci abubuwan da su ka shafi ladubba da kuma horaswa. Sannan ya yi kwas-kwasai da dama da Hukumar UEFA.
Peter Rufai yana da digiri na biyu) a fannin Harkar kasuwanci.