HausaTv:
2025-07-03@01:49:08 GMT

An yi zanga-zanga zagayowar ranar ‘’Nakba’’ a sassan duniya da dama

Published: 18th, May 2025 GMT

An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa.

A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar.

A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin su “Falasdinu za ta rayu!” » ko “Dakatar da kisan kiyashi a Gaza”.

“Nakba ba wani lamari ne da ya faru a baya ba, yana ci gaba da faruwa ta hanyar korar jama’a, da amfani da bama-bamai,” kan al’ummar Gaza.

Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza tun bayan barkewar yakin kisan kiyashi da Isra’ila ta kaddamar a watan Oktoban 2023 bayan harin ba-zata da Hamas ta kai.

Masu zanga zangar dake dauke da tutocin Falasdinu a Paris, sun zargi hukumomin Faransa, da yin hadin gwiwa da Isra’ila ta hanyar yin gum da bakinsu.”

A Zirin Gaza tun daga ranar 18 ga watan Maris din 2025, lokacin da gwamnatin Sahayoniya ta ci gaba da kai hare-hare, tare da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, an kashe Falasdinawa sama da 3,000, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu a Gaza tun farkon yakin zuwa akalla mutane 53,272, galibi mata da kananan yara, sannan Fiye da mutane 120,673 kuma sun jikkata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

JMI Ta Bukaci Kungiyar Majalisun Dokoki Ta Duniya Su Kori HKI Daga Cikinta

Shugaban tawagar Iran a kungiyar hada kan majalisun dokokin kasashen duniya ya bukaci kungiyar ta yi tir da HKI saboda hare-haren da ta kai mata wanda ya keta dokokin kasa da kasa, ya kuma bukaci a koreta daga kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manoorchehr Mottaki yana fadar haka a wata wasikar da ya aikewa shugaban kungiyar majalisun dokokin ta duniya wato IPU, shugaban Tulia Ackson, ya ce abin  fata shi ne kungiyar zata yi tir da HKI kan sabawa doka ta 2(4) na MDD.

Har’ila yau Mottaki ya bayyana cewa yana fatan Ackson zai sa a jingine samuwar HKI a kungiyar.

Ya ce majalisar majalisun ta tattauna dangane da hare-haren Amurka da HKI kan kasar Iran su kumka yi All..wadai da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar
  • Hamas ta karɓi tayin tsagaita wuta a Gaza
  • Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
  • Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Kwana 60 Da Hamas – Trump
  • JMI Ta Bukaci Kungiyar Majalisun Dokoki Ta Duniya Su Kori HKI Daga Cikinta
  • Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza
  • Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli
  • Togo: An Kashe Mutane 7 A Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
  • Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya