Leadership News Hausa:
2025-07-03@15:07:42 GMT

Ciwon Mara Lokacin Al’ada

Published: 19th, May 2025 GMT

Ciwon Mara Lokacin Al’ada

A gauraya kayan hadi cikin zumar, a rika sha cokali 3 da safe bayan karyawa da kuma da dare kafin kwanciya. A fara amfani da wannan hadi kafin zuwan al’ada, sannan a ci gaba har ciwon ya lafa, da izinin Allah.

Ciwin Ciki na mata mai  zafi

Hadi mai matukar karfi:

Garin hulba cokali 7, Garin habbatussauda (habbur rashad) cokali 7, Man zaitun cokali 10

Yadda ake amfani da shi:

A gauraya su wuri guda.

A rika diban cokali 2, a tafasa, sai a tace, sannan a zuba zuma kadan a ciki sai a sha. A fara amfani da wannan hadin kwana 5 kafin zuwan al’ada, a ci gaba har lokacin al’adar. Wannan zai kara lafiya da ni’ima a jiki.

Wani Hadin:

Tsamiya, Habbatussauda, Zuma:

Yadda ake amfani da shi:

A tafasa tsamiya da habbatussauda, a tace, sannan a zuba zuma a ciki. A rinka sha sau biyu a rana. Wannan shima yana da tasiri sosai wajen saukar da zafi da busar da radadin ciwo.

Wani Hadin:

Hadin Citta da Kanafari:

Citta (zanyen ko garinta), Kanunfari, Zuma

A tafasa citta da kanunfari, a tace ruwan, a zuba zuma a sha, yana saukaka ciwon mara musamman ga wadanda suke da matsalar kumburin mahaifa.

Ganyen gwanda da Lemo:

ganyen gwanda rabi, Ruwan lemon tsami

A markada ganyen gwanda da ruwan lemon tsami, a tace a sha. Yana taimakawa wajen tsaftace mahaifa da rage radadin mara. Ko kuma a dafa.

Tsarki da Ganyen Magarya:

A tafasa ganyen magarya, a zauna ciki (wankan dumi) na mintuna 15, musamman idan al’ada ta zo da zafi. Wannan na rage jin radadi da kwantar da mahaifa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Mara

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata 2 bayan ambaliya

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako.

Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin.

Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki watanni biyu bayan ibtila’in ambaliyar.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
  • Rasha Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba
  • Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
  • Arsenal Ta Sayi Kepa Daga Chelsea
  • Ba Gaskiya Ba Ne: Ɓarayi Ba Su Sace Ɗan Uwan Gwamnan Zamfara Ba
  • NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata 2 bayan ambaliya
  • Dalibai 29 Suka Rasu A Turmutsitsin Tserewa Ga Fashewar Taransifoma A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya