Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi
Published: 18th, May 2025 GMT
An yi wa ɗan wasan gaba na ƙungiyar Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi allurar barci mai nauyi domin taimaka masa murmurwa daga tiyatar da aka yi masa.
Bayanai sun tabbatar cewa an garzaya da ɗan wasan ɗan asalin Nijeriya asibiti ne domin yi masa tiyata a ranar Litinin, bayan ya samu mummunan rauni a cikinsa a wasan da suka tashi canjaras, 2-2 da Leicester a Gasar Premier ta Ingila.
Alamu sun nuna cewa rayuwar ɗan wasan mai shekara 27 ba ta cikin haɗari, kuma allurar barcin da aka yi masa za ta taimaka ne wajen tsagaita ayyukan zuciya da jikinsa wanda hakan zai taimaka wajen hanzarta samun sauƙi.
Awoniyi ya yi karo ne da ƙarfen raga sa’ilin da yake ƙoƙarin cin ƙwallo mintuna kaɗan gabanin tashi daga karawar tasu da Leicester.
Likitoci sun kwashe tsawon mintuna suna kula da shi kafin barin sa ya ci gaba da wasa, duk da raɗaɗin da yake ji, kamar yadda aka gani baro-baro, kasancewar a lokacin Forest ta ƙarar da yawan ’yan wasa da za ta iya canzawa.
A ranar Litinin aka kara tabbatar da munin raunin da ya samu bayan likitocin ƙungiyarsa sun kara duba shi, aka garzaya da shi asibiti domin yi masa tiyata.
Amma ranar Talata, Nottingham Forest ta fitar da sanarwa cewa “Awoniyi na samun sauki”.
A yayin wasan nasu an ga yadda aka samu wata ’yar rashin jituwa tsakanin mamallakin ƙungiyar Evangelos Marinakis da mai horas da ita Nuno Espirito Santo a cikin filin wasa jim kaɗan bayan kammala wasan a ranar Lahadi.
Bayan sukar abin da mamallakin ƙungiyar ya yi, Forest ta ce lamarin ya faru ne kasancewar Marinaki bai ji daɗin yadda Awoniyi ya ci gaba da wasa ba duk kuwa da raunin da ya samu.
Sanarwar ƙungiyar ta ce “Evangelo Marinakis bai ɗauki Nottingham a matsayin ƙungiyar ƙwallon ƙafa kawai ba, ya ɗauke ta a amatsayin wani ɓangare na iyalinsa — kuma yana ƙoƙarin ganin kowa ya yi amanna da hakan.
“Shi ya sanya bai ji daɗin abin da ya faru ba a filin wasa na Leicester City a ranar Lahadi.
“Matakin da ya ɗauka ya kasance na nuna tsantsar kulawa da tallafa wa daya daga cikin waɗanda ya ɗauka a matsayin nasa.”
Wane ne Taiwo Awoniyi?Awoniyi ɗan asalin Najeriya ne mai shekaru 27 da ke taka leda a ƙungiyar Nottingham Forest da ke Birtaniya.
Ya tafi ƙungiyar ne a watan Yunin 2022 daga ƙungiyar Union Berlin da ke Jamus, kuma ya fara wasan ƙwallon ƙafa ka’in da na’in ne a ƙungiyar Liverpool a shekara ta 2015 kafin ya tafi wasu ƙungiyoyi a Jamus da Holland da kuma Belgium a matsayin aro.
Ɗan wasan na gaba ya taka wa Nijeriya a gasanni daban-daban a matakai daban-daban kafin buga wa ƙasar a babbar ƙungiyarta ta Super Eagles.
Yana daga cikin tawagar Nijeriya da ta yi nasara kan Libya a wasan neman gurbin gasar Kofin nahiyar Afirka ta 2025. Dan wasan na da aure da ɗa ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya a ƙungiyar
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri.
Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai.
12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe“Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara) da kuma shawarwarin kwamitin bayar da shawara kan jinƙai, don haka na yi afuwa ga fursunoni 66 da ke babbar cibiyar gyaran hali da ke nan Maiduguri,” in ji Zulum.
Ya kuma ƙara da cewa “Na kuma mayar da hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai-da-rai tare da rage wa wasu fursunoni hukuncin zaman gidan yari a wani ɓangare na bukukuwan murnar zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya ta bana.”
“Bayan afuwar, Gwamna Zulum ya yi wani gagarumin tallafi ta hanyar ba da gudummawar tsabar kuɗi Naira dubu 20 ga kowanne fursunoni 1,280 da ke cikin wannan gidan gyaran.”
Don ci gaba da gudanar da bukukuwan ranar dimokraɗiyya a cibiyar, ya kuma sanar da bayar da gudummawar buhunan shinkafa 300, galan 50 na man girki, da shanu guda 5.
Da yake mayar da jawabi Kwanturolan gidan gyaran hali na jihar Borno, Ibrahim Bawa ya yaba da ziyarar da Gwamnan ya kai wanda ya ce ba a taɓa yin irinsa ba.
“Wannan shi ne irinsa na farko,” in ji shi.
Yana mai cewa, babu wani gwamnan da ya gabata da ya ziyarci wurin domin yin murna ga fursunonin, musamman waɗanda suka yi sa’ar shaƙar iskar ’yanci.
Bawa ya kuma tuno da irin karamcin da Gwamnan ya yi a baya da suka haɗa da kyaututtukan buhunan shinkafa 100, galan-gadan na man girki 25, da bijimai 10 a lokacin bikin Sallah na Eid-el-Kabir na baya, wanda ya ce duk fursunoni da ma’aikata sun ji daɗin su.
Mista Gambo Samuel, wanda aka fi sani da Sarkin Gida, kuma shugaban fursunonin, ya nuna matuƙar godiya ga Gwamna Zulum dangane da wannan alfarma da ya musu na afuwar da kuma kayan abincin da ya kawo musu tallafinsa.
Ya kuma yaba wa ƙoƙarin Gwamnan na kawo sauyi a faɗin jihar, wanda ya lura akai-akai ana jin labarin sa daga sabbin fursunonin da ke shigowa wannan cibiyar lokaci zuwa lokaci.
Baya ga ziyarar da ya kai gidan gyaran halin, Gwamna Zulum ya kuma ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da dama na tunawa da ranar dimokuraɗiyya a cikin birnin Maiduguri da suka shafi hanyoyin mota, ruwan sha, cibiyoyin kiwon lafiya da makamantansu.