Mutum 5 sun jikkata yayin da gidan mai ya ƙone ƙurmus a Ribas
Published: 17th, May 2025 GMT
Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas.
Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi.
Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaroMa’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar.
Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya.
Ya kuma ce shi da matarsa mai ɗauke da juna biyu sun kuɓuta da ƙyar daga gobarar.
“Na shirya domin ɗaukar fasinjoji zuwa Jihar Ebonyi. Ina buɗe but ɗin motata sai na ji ƙarar gobara.
“Nan take na kwanta a ƙasa, na tashi da sauri na gudu kafin fashewar. Motata ta ƙone, wasu mutane sun jikkata, ni ma na samu rauni.
“Amma cikin ikon Allah babu wanda ya rasa ransa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa motar asibiti ta Sojojin Sama ta zo, inda aka dinga kula da waɗanda suka jikkata, sannan aka ɗauki wasu zuwa asibiti.
A cewarsa jami’an kashe gobara sun isa wajen amma ruwansu ya ƙare, sai da Sojojin Sama suka kai ɗauki sannan suka iya kashe wutar gaba ɗaya.
Wani wanda abin ya shafa, Anthony Ofoke, wanda shi ne mai kula da ayyukan Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi a Jihar Ribas, ya ce gobarar ta lalata motocinsu guda biyu.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Jihar Ribas
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu.
’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — AmaechiBayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts.
Ya ce za a yi amfani da rahoton binciken asibitin a kotu.
Hakazalika, an kama wani mutum mai shekara 35 da ke unguwar Golkos a Ƙaramar Hukumar Billiri, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara shida fyaɗe a unguwar Awai.
Mahaifiyar yarinyar ce ta rahoton faruwar lamarin, inda ’yan sanda suka kama wanda ake zargin, sannan suka garzaya da da yarinyar Asibitin Kaltungo domin duba lafiyarta.
DSP Abdullahi ya ƙara da cewa rundunar ta kama wasu mutane 18 daban da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar.