Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 10 sun rasu kan rikicin gona da dabbobi a Filato

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.

Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa.

Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’  Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS

A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom.

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai harin ramuwar gayya ƙauyen Danchindo da yammacin a ranar 13 ga watan Mayu, inda suka kashe mutane huɗu.

A ranar 14 ga watan Mayu, an kashe shanu 26, wasu kuma sun jikkata a ƙauyen Darwat, lamarin da ake zargin ramuwar gayya ce saboda kashe mutane da aka yi.

Daga bisani wasu da ake zargin ‘yan bindigar Fulani ne sun kai hari wani ƙauye da ke kusa da al’ummar Wereng Kam, inda suka kashe mutane shida.

Bayan samun rahoton tashin hankali a Riyom, jami’an haɗin gwiwar tsaro sun shiga tsakani tare da ganawa da wakilan jama’a domin kwantar da tarzoma, da kuma gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu.

A bisa zargin sace shanu da kisa, an kama mutum ɗaya wanda ake ci gaba da bincike a kansa, tare da ƙwato shanu 130 a hannunsa.

Sanarwar ta kuma ce, tsayin dakan da sojoji suka yi ne ya hana maharan ƙone ƙauyen Wereng gaba ɗaya.

An fara sintiri domin kama waɗanda suka gudu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kasancewa a yankin domin wanzar da zaman lafiya.

Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven kuma shugaban runduna ta 3, ya kai ziyara yankin inda ya gana da shugabanni da wakilan al’umma.

Yanzu haka an fara samun zaman lafiya yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tabbatar da tsaro a yankin.

Wannan lamarin ya faru ne kwanaki huɗu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kasuwa a Ƙaramar Hukumar Wase, inda suka sace ’yan kasuwa biyar kuma suka kwashe kayayyaki.

Har ila yau, an ruwaito cewar maharan sun isa kasuwar ne a babura a ranar Litinin, lokacin da kasuwa ta cika da ’yan kasuwa da masu sayayya daga sassa daban-daban.

Sun fara harbe-harbe wanda ya sa mutane suka tsere domin tsira da rayukansu.

A baya-bayan nan, ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren da ake yawan kai wa wasu sassan Jihar Filato.

Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin yunƙurin kisan ƙare dangi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama wasu da haramtaccen buhunan takin zamani 20 a Borno
  • Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Karfin Tsaro Da Makamansu Masu Linzami Ne Suka Hana Makiya Kai Musu Hari
  • Mutum 10 sun rasu kan rikicin gona da dabbobi a Filato
  • Lassa: Mutane 138 Sun Rasu, 717 Sun Kamu A Jihohi 18 – NCDC
  • ’Yansanda Sun Cafke Mutane 9 Kan Kisan Jigon Jam’iyyar PDP A Adamawa
  • Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile
  • Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi