Yadda Ake Hada Danderun Kaza
Published: 18th, May 2025 GMT
Za ki samu kaza sai ki wanke ta, sannan ki tabbatar kin tsane mata ruwa ba’a barinta da ruwa ko kadan, sai ki zuba magi da gishiri da kori da kayan yaji da tafarnuwa idan kin so za ki dakata ko ki zuba ta haka, sai ki cakuda sosai ya shisshiga cikin kazar, sannan ki kawo albasa ki zuba wanda dama kin yankata a kwance ko a tsaye ba kanana ba saboda katta narke.
Sai ki kawo jajjagen tattasanki ki zuba, sai ki sake gaurayawa sosai, sannan ki ware ‘Foyil paper’ mai yawa yadda za ta dauki kazar sai ki zuba a ciki ki rufe ta gaba daya ba’a so kofa ko kadan saboda kada ruwa ya shiga sannan ki kara waro wata ki sake rurrufewa sosai.
Idan kuma kina da Steamer pot sai zuba ruwa a cikin ki dora akan steamer ki rufe ki dora a wuta ya yi kamar awa biyu za ki ga ya dahu.
Idan kuma baki da steamer za ki iya yi da tukunya da kwando, ki zuba ruwa a tukunya ki sa Kazar a kwando sai ki dora a tukunya ki dora a wuta kamar za ki yi dambo. A ci dadi lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya
Ga hotunan yadda ake gudanar da zaɓen cike gurbi a sassan Najeriya.