Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo
Published: 16th, May 2025 GMT
A ranar Asabar ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Rome na ƙasar Italiya bisa gayyatar da sabon Fafaroma Leo XIV ya aike masa.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya sanar da cewa, shugaba Tinubu zai yi bulaguron ne tare da manyan jagororin ɗariƙar Katolika na Najeriya domin halartar bikin rantsar da sabon fafaroman wanda shi ne na 267.
A cewar Onanuga, Cardinal Pietro Parolin ya aike da goron gayyata daga Fafaroma Leo XIV, wanda ya ce bikin ya nuna “wani lokaci mai muhimmanci ga mabiyan Cocin Katolika da kuma duniya da ke fama da tashe-tashen hankula da rikice-rikice da dama”.
Fadar shugaban ƙasar ta ce cikin takardar gayyatar sabon fafaroman ya bayyana alaƙar ƙashin kai da Najeriya, yana mai cewa ”ƙasarka mai girma na da mutuƙar muhimmanci a gareni, saboda na yi aiki a majami’ar Apostolic Nunciature da ke birnin Lagos a shekarun 1980”.
A cewar sanarwar, tawagar ta shugaba Tinubu za ta haɗa da Minista a harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu; Archbishop Lucius Ugorji na Owerri da kuma shugaban rukunin Bishop na Katolika na Najeriya; Archbishop Ignatius Kaigama na Abuja; da Alfred Martins na Legas; da kuma Bishop ɗin Katolika na Diocese na Sokoto, Mathew Hassan Kukah.
Fafaroma Leo XIV, tsohon Cardinal Robert Francis Prevost, za a rantsar da shi a matsayin Fafaroma a ranar Lahadi, 18 ga Mayu, a dandalin St Peter’s da ke Vatican.
Fafaroma Leo, wanda shi ne Fafaroma na farko daga Amurka an zaɓe shi ne kwanaki 17 bayan mutuwar magabacinsa, Fafaroma Francis, a ranar 21 ga Afrilu. Shi ne zai jagoranci Katolika biliyan 1.4 na duniya.
Ana sa ran shugaba Tinubu zai koma Abuja ranar Talata, 20 ga watan Mayu, in ji sanarwar
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Tinubu Cardinal Robert Francis Prevost Fafaroma Leo XIV sabon Fafaroma Fafaroma Leo
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe.
Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin.
Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar za ta sake shirya musu wata jarabawar.
NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A NajeriyaShirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB.
Domin sauke shirin, latsa nan