Kwara Ta Kafa Tutar Hadin Kai Mai Mita 70 A Ilorin
Published: 20th, May 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta kafa tutar hadin kai mai tsayin mita 70 a hukumance, wanda ke zama alamar “hadin kan kasa, tafiya tare da buri a matsayin al’umma”.
Da yake jawabi a wani takaitaccen biki a Ilorin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce jihar ba ta daga tuta kawai ba, a’a tana nuna kwarin guiwar wata alama ce ta hadin kai, alfahari, da kuma kishin kasa.
Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinan sadarwa na jihar Bola Olukoju, wanda wasu kwamishinoni uku suka taimaka masa: Aliyu Kora Sabi (sufuri); Nafisat Buge (Muhalli); da Nnafatima Imam (ci gaban al’umma) da sauran manyan baki.
A cewarsa, sandar tuta na kara karfafa martabar jihar a matsayin cibiyar kirkire-kirkire, al’adu, da jagoranci mai ma’ana.
Gwamna Abdulrazaq ya yi bayanin cewa, alamar za ta zama babban abin jan hankali, jawo masu ziyara, da samar da damammaki, da kuma baje kolin dabarun saka hannun jari na jihar kan ababen more rayuwa da ba wai kawai a yi amfani da su ba har ma da karfafa gwiwa.
Ya ce gwamnatinsa ta gina tituna, asibitoci na zamani, da karfafa samar da ruwan sha tare da bayar da tallafi ga manoma, ‘yan kasuwa, da kuma bangarori daban-daban na al’umma.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma October 30, 2025
Daga Birnin Sin Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC October 30, 2025
Daga Birnin Sin Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya October 30, 2025