HausaTv:
2025-11-27@22:37:48 GMT

Falasdinu : ‘Yan jarida 222 aka kashe tun fara yakin Gaza

Published: 19th, May 2025 GMT

Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe ‘yan jarida 5 na Falasdinawa a wasu hare-hare daban-daban da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, lamarin da ya kai adadin ma’aikatan yada labaran da aka kashe tun farkon yakin Isra’ila a zirin Gaza zuwa 222.

Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da dan jarida mai daukar hoto Aziz al-Hajjar, da matarsa, da ‘ya’yansu, wadanda aka kashe a ranar Lahadi, lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a gidansu da ke unguwar Saftawi a arewacin Gaza.

A gefe guda kuma, an kashe dan jarida Ahmad al-Zinati tare da matarsa, Nour al-Madhoun, da ‘ya’yansu, Mohammad da Khaled, a lokacin da aka kai wa tantin su hari a Khan Younis a yammacin ranar Asabar.

Shahadar wadannan ‘yan jarida na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan mutuwar Ahmed al-Halou, wani dan jarida da ke aiki da kafar yada labaran birnin Quds, wanda aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE

Daga Usman Muhammad Zaria 

Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin.

Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo.

Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na bukatar gyara.

Shirin AGILE, wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa mata ƙwarewar da za su dogara da kansu, inda ake sa ran mutum 50 za su amfana a horon da ke tafe.

 

A lokacin ƙaddamar da aikin, Mai kula da shirin AGILE a Birnin Kudu, Hajiya Maryam Hassan Jibrin, ta yaba da jajircewar Dr. Builder Uba ga ci gaban al’umma, tana jinjinawa kokarinsa tare da yi masa addu’ar ci gaba da jagoranci mai tasiri.

Da yake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ci gaban matasa, Muhammad Uba ya yi alƙawarin bayar da gagarumin tallafi ga mahalarta bayan kammala shirin cikin nasara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Isra’ila Tana Ci Gaba Da Rushe Gidaje A Yankin Gaza
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano