’Yan bindiga: Zamfara sun koma kwana a jeji
Published: 20th, May 2025 GMT
Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara.
Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu 26.
Wani mazaunin Ƙauran Namoda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce adadin mutanen zai iya cin haka, inda ya tabbatar cewa maharan sun kashe wata mata tare da sace wasu 26.
Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku.
An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin maniyyata a Saudiyya An kama ɗan bindiga a hanyar zuwa aikin Hajji a SakkwatoWani ganau ya ce lamarin ya fi muni a ƙauyen Sabon Gari inda ’yan bindiga suka kashe wata mata sannan kuma yi garkuwa da wasu mutane sama da 20.
’Yan ta’addan sun tsananta kai hare-hare a kan ƙauyuka inda a Asabar da misalin karfe 1:30 suka kai hare-haren, duk kuwa da cewa an girke jami’an tsaro a garin Ƙaura Namoda.
Wata majiya a yankin ta ce ana zargin ’yan ta’addan suna da alaƙa da jagoran ’yan bindiga, Bello Ƙaura, wanda aka fi sani da Ɗan Sade, wanda ya ya addabi ƙananan hukumomin Ƙaura Namoda da Bunguɗu da kuma Maradun.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ƙaura Namoda yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato
Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.
Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.
“Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen wannan ta’addancin.”
Dan Majalisar ya ce ya gabatar da bukata ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa domin tallafawa wadanda lamarin ya shafa kuma zai ci- gaba da bibiya domin ganin tallafin ya samu cikin lokaci.
Ya ce yana kokarin ganin rundunar sojoji ta kara tura wadatattun jami’ai tare da tallafa masu domin yakar ‘yan ta’addan da wanzar da zaman lafiya a yankunan.
Tallafin kayan abinci na gaggawa da dan majalisar ya bayar sun hada da buhuhuwan masara, gero, garin kwaki da kuma kuli- kuli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp