2025-12-13@12:12:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5847
«kwalliya»:
Wani kwalekwale da ke ɗauke da fasinjoji takwas ya kife yayin da yake ƙetare kogin da ke kan iyaka da garin Gamboru na Najeriya da Fotokol a ƙasar Kamaru, inda mutane uku suka mutu. Lamarin ya faru ne da misalin qarfe 6:30 na yamma lokacin da kwalekwalen, wanda wani Mamman Nur Abbagana na Kasuwan Katako,...
Amurka ta kama wani katafaren jirgin ruwan dakon man Najeriya kan zargin safarar ɗanyen mai na sata. Jami’an tsaron Amurka sun kama jirgin mai suna Super Tanker, mai lamba 9304667, ne, bayan sun gano cewa ya yi basaja, inda ya maƙala tutar wata kasa daban maimakon ta Najeriya yayin shigarsa ruwan Amurka. Wannan ya haifar...
Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa. Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna. Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar...
Tauraro kumafitaccen mai shirya fina-finan HausaAli Huhu, ya bayyana Iran a matsayin misali wajen haskaka Musulinci a matsayin adinin zaman lafiya ta hanyar fina-finai. A wata hira ta musamman da da kamfanin dillancin labarai na Iran Press, Ali Nuhu, wanda shi ne babban Manajan Kamfanin Fina-finai a arewacin Najeriya, ya yaba wa Iran saboda kokarin...
Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani daftarin kuduri da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agajin jin kai ba tare da wani sharadi ba zuwa Zirin Gaza. Kudurin da aka zartar a ranar Juma’a, ya yi kira ga Isra’ila da ta kare cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya tare da bin dokokin kasa da...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati...
Daga Usman Muhammad Zaria Aikin rigakafin watan Disamba a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar Jigawa ya samu gagarumar nasara, yayin da iyaye suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafi. Wasu daga cikin iyayen da suka kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 3 domin gudanar da aikace-aikacenta a lokacin aikin Hajjin 2026. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara a gaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin...
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya jaddada goyon bayansa ga wa’adin mulki ɗaya kacal ga gwamnonin, yana mai cewa hakan zai inganta aiki da kuma inganta harkokin mulki. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rantsar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin Ƙananan hukumomi, mataimakan shugabannin, Kwamishinoni da shugabannin hukumar a ɗakin taro na Hauwa...
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya jaddada game da mihummanci sanya hannun jari da kuma hadin guiwa a iyakoki, a matsayin abubuwan da ya fi mayar da hanakli akai a lokacin ganawarsa da shugaban kasar iraki Abdul latif rashid a gefen taron kasa da kasa na zaman lafiya a kasar Turkmenistan...
Dakarun Sojin Rundunar Operation Haɗin Kai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani samame da suka kai yankin Shettimari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga, a Jihar Borno. Majiyoyi sun shaida cewa rundunar ta kai harin ne ƙarƙashin Operation Desert Sanity V da safiyar ranar Alhamis. Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya...
Ɗan wasan gaban Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Galatasaray ɗan asalin Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na bana, a bikin bayar da kyaututtuka ta GQ Türkiye na maza na 2025. Ɗan wasan mai shekara 26 ya sami kyautar mafi girma a bikin da aka gudanar mai ban sha’awa. Matatar man Dangote ta...
Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba. A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin...
A ci gaba da al’adar fiye da shekaru 30, Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Afirka da dama a tsakanin 5-11 ga watan Janairun 2025 don sake tabbatar da dangantakar diflomasiyya da kuma binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Wannan ziyarar ta sake tabbatar da manufar ci gaba da cin moriyar juna a...
Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai. Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan...
Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu. A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar...
Wani dan sandan mai suna Ahmed Tukur ‘Yantumaki ya yi batan dabo yayin da yake a bakin aikinsa a Babban Ofisishin ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina. Bayanai sun nuna cewa, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2025 jami’in ya je bakin aiki inda ya ajiye jikkarsa da kular abincinsa a...
PDP wanda ke da gwamnonin 11 bayan zaben 2023, yanzu tana da biyar kawai tare da karin wasu suna nuna suna son barin jam’iyyar. Yawancin gwamnonin da suka sauya sheka a cikin wannan lokaci sun koma APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu guda daya. Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne Umoh...
A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000. Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar...
A nan za mu iya cewa, wannan zunzurutun kudaden da za su tara har Naira biliyan 19 a wata daya, ya zama wajibi alummar yankin su sauya, na dakile matsalar domin kuwa, ‘yan Nijeriya, sun gaji batun ana tara dimbin kudade, domin magance wata matsala a kasar, amma daga, a karkatar da su, zuwa wata...
Wani abun lura ma a nan shi ne yadda a matsayinta na kasa mai tasowa ta farko a tarihin duniya da ta cimma nasarar samun wadata cikin lumana, Sin ta samar da wata taswira mai inganci, wadda sauran kasashe masu tasowa za su iya bi domin raya kansu cikin lumana, kuma karkashin hakan ne take...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya zargi ‘yan siyasan Nijeriya da zagon kasa ga ci gaban kasar ta hanyar daukar mukaman gwamnati a matsayin gadon gidansu a maimakon amanar jama’a. Da yake jawabi a ranar Laraba a yayin taro karo na 15 mai taken, “ya Isa haka” da ya gudana a jihar Legas,...
Kamfanonin Sin Sun Kera Tare Da Sayar Da Motoci Sama Da Miliyan 31 Tsakanin Janairu Zuwa Nuwamban Bana
Masana’antun kirar motoci na kasar Sin, sun samar tare da sayar da motocin da suka haura miliyan 31 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, wanda hakan ke shaida irin ci gaban da suka samu ta fuskar fitar da hajoji. A cewar wasu alkaluma daga kungiyar kamfanonin kirar motoci na kasar Sin, tsakanin watan Janairu...
Hukumar kwallon kafa ta Nigeria (NFF) ta taya Osimhen murnar samun wannan babbar nasarar a kwallon kafa ta hanyar sanya hoton Osimhen a babban shafinsu na Facebook da yake da mabiya fiye da miliyan daya, Osimhen na daga cikin yan wasan da kocin tawagar ta Super Eagles Eric Chelle ya gayyata domin buga gasar kofin...
Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin...
Ministan Harkokin Waje na Jamhuriyar Benin, Olushegun Adjadi Bakari, ya ce kimanin sojoji 200 daga Najeriya da Ivory Coast yanzu haka na cikin kasar shi a matsayin wani ɓangare na aikin tsaro don tallafa wa gwamnati. Ƙaramar ƙasa ta Yammacin Afirka ta girgiza da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar Lahadi, wanda...
Jam’iyyar PDP a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo. Jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar ce a cikin wata sanarwa da sakatarenta yada labaranta na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar. Rahotanni sun ce Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar...
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Faidan ne ya bayyana cewa; kasarsa za ta iya daukar nauyin wararen matsalar Falasdinu, kuma a shirye take ta aike da sojoji zuwa yankin na Gaza idan bukatar hakan ta taso. Fidan ya fada wa kamfafen watsa labaru cewa; Tukriya a shirye take ta yi duk abinda za ta iya...
Kamfanin samar da siminti na BUA ya bayar da tallafin karatu Naira miliyan 40 ga ɗalibai 200 da ke manyan makarantu a jihohin tsohuwar Jihar Sakkwato. An bayar da tallafin domin ganin sun cimma burinsu a fannin ilmi. An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin...
Zuwa karfe 5:41 na daren ranar 7 ga watan Disamba, fim din Amurka “Zootopia 2” wanda aka fara nuna wa kwanaki 12 da suka wuce (tun daga ranar 26 ga Nuwamba), ya samu kudaden shiga a cikin kasar Sin da yawansa ya wuce yuan biliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 424.8, adadin da ya zarce...
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta lalata kayayyaki marasa inganci da suka kai sama da Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa. Kayayyakin da aka ƙwato daga jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Nasarawa, Benuwe da Kogi da Filato, an lalata su ne a wurin zuba shara a Angwan...
Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester United ta fara zawarcin tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 39,wanda ya bar Ƙungiyar Monterrey ta Mexico. Ramos wanda a shekarun baya, United ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa, yanzu haka yana da damar komawa ƙungiyyar a matsayin kyauta. Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen...
Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya, tare da haɗin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Kasar sun buɗe shafin neman aiki domin ɗaukar sabbin ’yan sanda na constables da kuma ma’aikata masu kwarewa ta musamman. A kwanan nan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ’yan sanda 50,000 a fadin ƙasar...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Farfesa Amina Salihi Bayero, a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar Northwest. Naɗin nata zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamban 2025, har zuwa tsawon shekaru biyar. EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara. Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na...
Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama tare da tsare Tsohon Ministan Ƙwadago kuma Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Chris Ngige. Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe ne, ya tabbatar da hakan da safiyar ranar Alhamis. bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewar an sace Ngige. An koro ’yan Najeriya...
Aƙalla ’yan Najeriya 32 ne aka koro su daga Indiya kan zargin su da hannu a kasuwancin miyagun ƙwayoyi. A ƙarshen watan da ya gabata, ’yan sandan Delhi da na Telangana, sun kama ’yan Najeriya 50 biyo bayan samamen da suma kai wa wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi mai alaƙa da ƙasashen waje. Ba ni...
Aƙalla ’yan Najeriya 32 ne aka koro su daga Indiya kan zargin su da hannu a kasuwancin miyagun ƙwayoyi. A ƙarshen watan da ya gabata, ’yan sandan Delhi da na Telangana, sun kama ’yan Najeriya 50 biyo bayan samamen da suma kai wa wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi mai alaƙa da ƙasashen waje. Ba ni...
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta nuna damuwa kan rudanin siyasa a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito. Shugaban Hukumar ECOWAS Omar Touray ya shaida wa taron ministoci a Abuja babban birnin Najeriya cewa, “Abubuwan da suka faru a ‘yan makonnin da suka gabata sun nuna bukatar yin tunani...
Ghana ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin ‘yan kasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion na Isra’ila, bayan da aka tsare wasu fasinjoji ko kuma aka yi musu korar kare, ta kuma ce tana tunanin daukar irin wannan matakin na ramuwar gayya. Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana...
Hukumar ICPC ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Najeriya na ɗaure a gidan yari. Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi. Kisan...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya...
Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya ce zai yi hisabi da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban Allah kan abin da ya faru a Zariya a 2015. Rikicin ya fara ne bayan da mambobin IMN sun tare wa tsohon Hafsan Soji, Tukur Buratai, hanya. Najeriya za ta buga wasan sada zumunta...
Daga Aliyu Lawal Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa,...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken...
Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu. A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar...
Zanga-zanga ta ɓarke a yankin Numan da ke Jihar Adamawa, kan zargin sojoji da kashe wasu mata a garin Lamurde. Mata sun fito zanga-zangar ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin kabilu Bachama da Chobo. An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara Sakkwatawa na murnar kisan da...