Leadership News Hausa:
2025-06-14@13:36:38 GMT

Tarihin Makarantar Katsina-kwalej Zuwa Ta Horon Malamai (1)

Published: 19th, May 2025 GMT

Tarihin Makarantar Katsina-kwalej Zuwa Ta Horon Malamai (1)

A wancan lokacin,Mrs. Bintu M.Sadik, cewa tayi  Sir S.M. Banaman shi ne Shugaban Kwalejin na farko duk kuma Malaman Turawa, daga baya ne aka dauke Hausawa ‘yan asalin wurin saboda su koyar da Hausa da kuma al’amarin daya shafi addinin musulunci.Ta ce mshahuran ‘yan Arewa sun halarci Kwalejin daga cikinsu akwai Firayim Minista na farko Abubakar Tafawa Balewa,Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan  Arewa, da kuma Sir Kashim Ibrahim,  da dai sauran wasu duk sun halarci Kwalejin ta Katsina

An samu labarin kasar Katsina ta taba kasancewa wata babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara.

Wannan  shi tun  lokacin da aka hade Arewa da Kudancin Nijeriya Katsina tana daya daga cikin wuraren da  hanyar jirgin kasa ta bi ko kuma Layin Dogo  a lokacin.Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shi ya bada wurin da aka gina Katsina Kwalejin ne a cikin gonarsa da ke Rafukka a lokacin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya

Ana zargin wata mata mai suna Khadija kan zargin kashe ’yarta mai shekaru 11, Fadila, saboda Naira 100 da ta samu a yawon Sallah a unguwar Tukur Tukur da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, inda lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a unguwar har maƙwabta suka ƙi yi wa gawar yarinyar sallah saboda tsoron abin da zai biyo baya.

Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3

Wasu maƙwabta sun bayyana cewa Khadija ta doke Fadila da taɓarya ne saboda ta zargi yarinyar da satar Naira 100.

Sun ce irin wannan ɗabi’a na duka da tsangwama ba sabon abu ba ne domin sau da dama idan ta tura Fadila talla aka samu matsala, sai ta lakaɗa mata dukan tsiya.

Wani mutum ya ce: “Dalilin da ya sa muka ƙi yi mata sallah shi ne, ba a ɗauki matakin da ya dace ba. An zubar da gaskiya. Saboda haka mu ma muka yanke shawarar ba za mu yi mata sallah ba.”

Amma mahaifiyar da ake zargi, wato Khadija, ta musanta zargin cewa ta yi wa ’yarta da duka da taɓarya.

Ta ce a lokacin da ta ke dukan yarinyar, ba kowa a gidan sai yara.

Mijin matar, Malam Mustapha Musa, ya shaida wa wakilinmu cewa lokacin da lamarin ya faru ba ya gida, don haka bai san yadda abin ya wakana ba.

Tuni mahaifin Fadila ya ɗauki gawar ’yarsa zuwa ƙauyensu da ke ji6har Kano domin yi mata sutura.

Ya ce: “Na bar komai da hannun Allah.”

Wani jami’in tsaron sa-kai wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce sun gayyaci Khadija da mijinta ofishinsu domin amsa tambayoyi, amma daga baya sai suka janye bayan sun ga ’yan sanda sun isa wajen.

Wakilinmu ya kai ziyara babban ofishin ’yan sanda da ke Ɗan Magaji, amma ya tarar babban jami’in ba ya nan.

Mataimakinsa ya ce ba su da masaniya game da lamarin.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya ce: “Ka jira, zan tuntuɓi ofishin yankin don jin yadda lamarin yake.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga ’yan sandan ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya
  • Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi
  • Matsin Rayuwa: ‘Yan Nijeriya Sun Rage Zuwa Kasashen Waje
  • Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina
  • Adadin Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Kashe A AfirkaTa Kudu Ya Karu Zuwa 49
  • Rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwanci a Arewa Maso Gabas
  • Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 8 A Jihar Filato
  • Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya
  • Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna