Hamas Ta Ce An Fara Tattaunawa Tare Da HKI Kan Tsakana Wuta A Doha A Yau Asabar
Published: 17th, May 2025 GMT
Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka.
Majiyar HKI ta nakalto firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa ya aika tawagar tattaunawarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa
Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa.
’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis ne suka samu kira daga Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Jigawa game da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawar zuwa Babban Asibitin Dutse, domin gudanar da bincike.