Malamai sun gindaya sharaɗi kafin janye yajin aiki a Abuja
Published: 20th, May 2025 GMT
Malaman makarantu da ma’aikatan ƙananan hukumomi a Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun bayyana cewa ba za su janye yajin aikin da suka shiga ba, har sai an biya malaman firamare bashin albashin da suke bi.
Yajin aikin ƙarƙashin jagorancin rassan ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) da ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), da na Abuja.
Wani mamba a ƙungiyar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana wannan matsaya ne a yayin wasu taruka guda biyu da suka gudanar a ranar Alhamis da kuma Juma’ar da ta gabata.
A cewarsa, shugabannin ƙananan hukumomi guda shida a Abuja, sun roƙi shugabannin ƙungiyoyin da su dakatar da yajin aikin domin ci gaba da tattaunawa, amma taron ya kare ba tare da an cimma matsaya ba.
Ƙungiyoyin sun nuna ɓacin ransu kan yadda shugabannin ƙananan hukumomi ke karya yarjejeniyar da aka cimma a baya-bayan nan, tare da rashin damuwa da walwalar malamai da sauran ma’aikatan ƙananan hukumomi.
Ko da yake ƙungiyoyin sun yaba da matakin shugabannin wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, sun ce har yanzu akwai sauran buƙatu da ba a biya ba.
Ƙungiyoyin sun kuma amince da shawarar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na amfani da kashi 10 na kuɗaɗen harajin da Abuja ke tattarawa daga ƙananan hukumomi domin biyan hakkokin ma’aikatan.
Sun buƙaci a fara biyan bashin watanni takwas na sabon mafi ƙarancin albashi da malamai da ma’aikatan ƙananan hukumomi ke bi, wanda adadinsa ya kai sama da Naira biliyan 16.
Sun jadadda cewar har sai an cika waɗannan sharuɗa, sannan za su janye yajin aikin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ma aikatan Ƙananan Hukumomi makarantu Sharadi Yajin aiki yajin aikin
এছাড়াও পড়ুন:
An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin maniyyata a Saudiyya
Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji.
An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji.
Ado Aliero shugaban ’yan bindiga ne da ya yi ƙaurin da yin garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda, musamman a Jihar Zamfara da maƙwabtanta.
Kafar yada labarai ta ABN News ta bayyana cewa matan biyu sun canza sunayensu domin kada a gane su.
An cimma matsaya kan dakatar da haska fina-finai 22 a Kano Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5Kamen nasu ya zama wani sabon a yadda gwamnatin Najeriya ke aiki tare da ƙasashen duniya wajen magance matsalar ta’addanci.
An bayyana cewa Gwamnatin Najeriya tana aiki tare da Saudiyya a yayin da ake zurfafa bincike kan matan da ake zargi.
Ba a bayyana sunayen matan a hukumance ba, amma majiyoyin tsaro sun bayyana cewa akwai yiwuwar a tatsi muhimman bayanai daga gare su.