Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Bunkasa Duk Da Matsaloli Da Dama
Published: 20th, May 2025 GMT
Bayan da mahukuntan kasar Sin suka kaddamar da yadda harkokin tattalin arzikin kasar suka gudana a watan Afrilun bana a ranar 19 ga wata, mataimakin shugaban zartaswa na kamfanin Novonesis na kasar Denmark, Morten Enggaard Rasmussen ya tattauna da wakilin CMG, inda a cewarsa, alkaluma sun nuna karfin tattalin arzikin kasar Sin.
A watanni 4 na farkon bana, saurin karuwar muhimman alkaluma masu alaka da samar da kaya a kasar Sin ya fi na shekarar bara baki daya. A watan Afrilu, wasu 36 daga cikin manyan sana’o’i 41 sun samu ci gaba bisa na makamancin lokacin a bara, adadin da ya wuce 80%. Alkaluma sun kuma nuna cewa, duk da matsalolin da take fuskanta, kasar Sin ta raya tattalin arzikinta ba tare da tangarda ba cikin watanni 4 na farkon bana, kuma ci gabanta bai tsaya ba, lamarin da ya nuna juriya mai karfi na tattalin arzikin kasar da kuma yadda take tinkarar kalubale.
Ban da haka kuma, cinikayyar waje ta kasar Sin ta samu karuwa ba tare da matsala ba, yayin da Amurka ta dora wa kayan kasar Sin karin haraji, lamarin da ya nuna karfin kasar Sin na yin takara a duniya. A watanni 4 na farkon bana, saurin karuwar jimillar kayayyakin shige da fice a kasar Sin ya fi na watanni 3 na karshen shekarar 2024 sauri har da 1.1%, jimillar kayayyakin da aka fitar ta karu da 7.5%. Har ila yau, yawan motoci da kasar Sin ta kera da kuma sayar da su duk sun wuce miliyan 10 a karon farko.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ake cewa, yin tafiya tare da kasar Sin, yin tafiya ne tare da damammaki. Kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada cikin amsar wasikar da ya aike ga jagoran majalisar bunkasa cinikayya ta Denmark dake kasar Sin, yadda ake nuna wa kasar Sin karfin zuciya, ya yi kama da yadda ake nuna karfin zuciya kan kyakkyawar makoma. Kana zuba wa kasar Sin jari, zuba jari ne a kan makoma. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tattalin arzikin kasar Sin kasar Sin ya a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hizbullah Ta ce Marigayi Shahid Ra’isi Ya Kasance Mai Taimakawa Kasar Lebanon Da Kuma Falasdinawa Ne
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa.
Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike makamai da dama a rayuwarsa a JMI amma wannan bai canza shi ba, ya kasance yana tambaya ta dangane da gwagwarmaya da HKI a yankin Hizbullah da kuma sauran mujahidai a yankin.
A lokacin shugabancinsa ya taimakawa kungiyar Hizbullah, sosai kamar yanda wadanda suka gabaceshi suka yi. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ce. Sayyid Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran yayi hatsari da jirgin sama mai saukar ungulu a kan hanyar dawowarsa daga makobciyar kasar Azerbai jan inda da shi da ministansa na harkokin waje da kuma limamin masallacin jumma’a na birnin Tabriz duk suka rasa rayukansu a hatsarin.