Gaza: Falasdinawa 150 Ne Su Ka Yi Shahada A Yau Lahadi
Published: 18th, May 2025 GMT
Mai Magana da yawun masu ayyukan ceto a yankin Gaza, ya sanar da cewa; Daga safiyar yau Lahadi zuwa marece adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 150.
Mahmud al-Basal ya fadawa tashar talabijin din ‘almayadin’ cewa; hare-haren na HKI sun fi tsanani ne a arewacin zirin Gaza, kuma kai tsaye suke kai wa sansanonin ‘yan hijira hari.
Da yake Magana akan kayan aikin da suke amfani da su domin ceto, al-Basal ya ce, kaso 75% na kayan aikinsu sun lalace, musamman motoci, kuma rashin makamashi ya sa ba za su iya amfani da su ne.
Haka nan kuma ya yi ishara da amfani da yunwa da HKI take yi akan falasdinawa,sannan ya kara da cewa; Da akwai dubban Falasdinawa da suke yi bacci ba tare sun sami burodin da za su ci ba.
A wurare uku da sojojin mamayar su ka yi wa mutane kisan kiyashi, adadin shahidai ya kai 150,kamar yadda jami’in aikin ceton ya shaidawa tashar almayadin. Daga cikin yankunan da akwai Beit-Lahiya, da Faluja, a arewacin Jabaliya.
Su kuwa Asibitocin yankin na Gaza suna cikin wuraren da sojojin mamayar su ka kai wa hare-hare. Asibiti na karshe da harin sojojin mamayar ya shafa shi ne; Asibitin Indonesia, wanda daga shi, ya zamana babu wani asibiti guda daya da ya saura mai aiki a Arewacin Gaza.
Dama dai sojojin mamayar sun baje asibitin Beit Hanun da kasa, su ka kuma ragargaza asibitin Kamal Adwan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin mamayar
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025