Ayatullah Khamenei : “Ba inda Rundunar Amurka ta taba shinfida zaman lafiya “
Published: 18th, May 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya caccaki kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan a ziyarar da ya kai a kasashen yankin Gulf na Farisa, yana mai cewa kalaman abin kunya ne a gare shi da dukkan Amurkawa, kuma bai cancanci amsa ba.
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar masu bayar da ilimi daga sassan kasar.
Ya kara da cewa wasu kalaman na Trump ba su ma isa a mayar da martani ba, yana mai kiransu da cewa abin kunya ne ga shi kansa shugaban Amurka da kuma wulakanci ga al’ummar Amurka.
‘’Ikirarinsa na cewa yana son samar da zaman lafiya da tsaro, zencen banza ne’’ inda ya kara da cewa Amurka na baiwa gwamnatin sahyoniya tan-tan na bama-bamai tana jefa su kan yara, asibitoci da gidajen jama’a a Gaza, Lebanon da kuma duk inda ta ga dama.
A yayin rangadin da ya ke a kasashen yankin Gulf, shugaban na Amurka ya yi jawabai da dama na sukar Iran.
A ziyarar da ya kai kasar Saudiyya, Donald Trump ya bayyana cewa “shugabannin Iran sun mayar da hankali wajen sace dukiyar al’ummarsu domin tallafawa ayyukan ta’addanci da zubar da jini a kasashen waje.”
Bayan hakan kuma, ya bayyana a Qatar cewa Amurka da Iran na daf da kulla yarjejeniyar nukiliya, kafin ya bukaci Iraniyawa da su “tashi” kan wannan batu “in ba haka ba wani mummunan abu zai faru.”, kallaman da jagoran juyin juya hali da shugaban kasar ta Iran sukayi fatali dasu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano.
Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro suna aikin tabbatar da zaman lafiya domin a gudanar da zaɓen cikin lafiya.
HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna“Dukkanin mutanen da muka gani suna kawo matsala an kama su, kuma zaɓen yana tafiya lafiya.
“Na gamsu sosai da yadda komai ke tafiya. Kayan zaɓe sun isa a kan lokaci, kuma yawancin rumfunan zaɓe sun fara aiki tun ƙarfe 8:30 na safe,” in ji shi.
Zango, ya ƙara da cewa an ɗan samu jinkiri a wasu wurare saboda matsalar sufuri da kuma yunƙurin wasu ƙungiyoyi na kawo cikas.
Amma ya ce jami’an tsaro sun shiga tsakani tare da tabbatar da doka da oda.
Ya ce ko da yake ba zai iya gane mutanen da aka kama ba, rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar masa cewa ta kama aƙalla ’yan daba 100 kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.