Yajin aiki: Jami’ar KASU ta shiga rudani
Published: 16th, May 2025 GMT
Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta shiga rudani a ranar Alhamis bayan da aka samu rahotanni masu karo da juna game da matsayin yajin aikin da reshenta na Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke yi.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya gudanar da taron manema labarai inda ya sanar da cewa ASUU-KASU ta dakatar da yajin aikin nata, kuma za a ci gaba da karatun nan take.
Ya danganta matakin janye yajin aikin da shiga tsakani da Gwamna Uba Sani ya yi, wanda ya amince da biyan Naira miliyan 50 miliyan don walwalar ma’aikata, tare da fitar da N146 miliyan don biyan wasu albashin da aka rike da kuma alawus-alawus na shirin koyon makamar aiki na dalibai (SIWES).
Farfesa Musa ya yaba wa wadannan matakan a matsayin “jaruntaka da ba a taba gani ba,” kuma ya jinjinawa gwamnan saboda “halinsa na ban mamaki game da halin da dalibai ke ciki, yanayin ilimi, da walwalar ma’aikatan ilimi da wadanda ba na ilimi ba.”
Layya: Farashin raguna na iya tashin gwauron zabo Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin SambisaYa kuma bayyana cewa an kafa kwamitin sasantawa karkashin jagorancin Mataimakiyar Gwamna Dokta Hadiza Balarabe, don tattaunawa da dukkan kungiyoyin jami’ar domin warware matsalolin da suka dade suna ci mata tuwo a kwarya.
Sai dai jim kadan kuma, ckin kakkausan harshe, ASUU-KASU ta musanta sanarwar Shugaban Jami’ar, inda ta bayyana ta a matsayin katsalandan kuma kuma mara izini.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Shugaban kungiyar Kwamared Abubakar Abdullahi da Sakatare Kwamared Peter M. Waziri suka sanya wa hannu, kungiyar ta shawarci jama’a da su yi watsi da ikirarin da hukumar gudanarwar jami’ar ta yi.
Kungiyar ta bayyana cewa, “Ba hukumar gudanarwar Jami’ar ce ta kaddamar da yajin aikin ba, don haka ba ta da ikon dakatar da shi.”
Kungiyar ta nanata cewa har yanzu tana jiran shawarar Majalisar Zartarwarta ta Kasa (NEC) bayan taron majalisar da aka gudanar a ranar 15 ga Mayu, 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yajin aiki yajin aikin
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse
Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19.
Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya.
Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a GombeAikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma.
Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba.
“Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan su ɓace bayan sun yi nasara,” in ji Yakubu Ayuba, mazaunin Talasse.
Ya ce rashin wuta ya jawo durƙushewar kasuwanci da tattalin arziƙi a yankin, kuma hakan zai yi tasiri a zaɓen 2027.
Wani mai sana’ar ɗinki, Musa Adamu Galadima, ya ce: “Janerata ya fi ƙarfinmu. Na kori yaran da ke koyon sana’a saboda ba zan iya ɗaukar nauyinsu ba.”
Shi ma Sulaiman Idris, mai sayar da lemun kwalba, ya ce yana kashe kusan Naira 10,000 a rana wajen siyan ƙanƙara.
“Lokacin da aka kawo kayan aiki mun yi farin ciki, amma yanzu komai ya tsaya,” in ji shi.
Da aka tuntuɓi ɗan majalisar don jin ta bakinsa, Ali Isa JC, ya ce matsalar ta samo asali ne daga jinkirin sakin kuɗaɗen aikin daga Gwamnatin Tarayya, amma suna ƙoƙarin ganin aikin ya ci gaba.
A halin yanzu, gwamnatin Jihar Gombe ta fara aikin samar da wuta ta hanyar samar da ƙaramar madatsar ruwa da hasken rana a Dam ɗin Balanga, wanda zai iya samar da 620KW.
Duk da haka, jama’ar Talasse sun ce rashin wutar zai sa su ƙauracewa kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.