Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma
Published: 17th, May 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Rome na Ƙasar Italiya domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo na XIV.
Za a gudanar da bikin ne a wajen wani taron addu’a da ake kira “solemn mass” a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu.
Crystal Palace ta lashe kofin FA na farko a tarihinta Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — KwankwasoAn tarbi Shugaba Tinubu a filin jirgin sojin Mario De Bernardo, inda jakadiyar Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da jami’an diflomasiyya daga Vatican da ofishin jakadancin Najeriya suka tarbe shi.
Tinubu ya samu gayyata ta musamman daga Sakatare Janar na Vatican, Cardinal Pietro Parolin.
A cikin wasiƙar gayyatar, Fafaroma Leo XIV ya bayyana cewa ya ga dacewar Shugaba Tinubu ya halarci bikin rantsar da shi.
Fafaaroma ya ƙara da cewa Najeriya tana da muhimmanci a gare shi domin ya taɓa aiki a ofishin jakadancin Vatican da ke Legas a shekarun 1980.
Shugaba Tinubu na tare da wasu manyan shugabannin cocin Katolika daga Najeriya ciki har da Archbishop Lucius Ugorji na Owerri, Archbishop Ignatius Kaigama na Abuja, Archbishop Alfred Martins na Legas, da Bishop Mathew Hassan Kukah daga Sakkwato.
Sun tafi Rome ne, domin nuna goyon baya da wakiltar Najeriya a bikin rantsar da sabon Fafaroma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bikin Rantsuwa Fafaroma Leo Sabon Fafaroma
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun kasar Kanada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci
Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun.
Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar.
A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita ba.”
Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba gwamnatin Najeriya za ta fitar da sanarwa kan matsayinta a hukumance, kamar yadda wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar mana, yana mai bayyana hukuncin a matsayin abin takaici.
Ita kuwa jam’iyyar PDP, ta bakin mamba a kwamitinta na zartarwa, Timothy Osadolor, ta ce kotun na da ’yancin fadin albarkacin bakinta, amma hukuncin nata ba yak an gaskiya.
“Amma babu wata hujja a cikin ra’ayin nasu da zai sa dukkan abin da suka fada a cikin hukuncin nasu ya zama gaskiya,” in ji Timothy.
Ya ce a maimakon ayyana jam’iyya gaba dayanta a matsayin kungiyar ta’addanci, kamata ya yi kotun ta fadi sunan masu alaka da ta’addancin kai tsaye, musamman a cikin jam’aiyyar APC.
Ya kuma bayyana hukuncin a matsayin na yanke kauna da salon shugabancin gwamnatin Najeriya a karkashin Shugaba Bola Tinubu, inda ya bukaci gwamnatin da kada ta dauki lamarin da wasa.
Sai dai duk kokarinmu na jin ta bakin jam’iyyar APC da gwamnatin tarayya ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Masu magana da yawun APC na kasa, Felix Morka da Bala Ibrahim ba su amsa kira rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura musu ba, yayin da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, shi ma bai amsa sakon da wakilinmu ya tura masa ba.
To said ai wani jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta fitar da sanarwa a kan hukuncin a hukumance da zarar ta tabbatar da sahihancin hukuncin.