An cimma matsaya kan dakatar da haska fina-finai 22 a Kano
Published: 20th, May 2025 GMT
Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da masu shirya fina-finai sun cimma matsaya bayan dakatar da wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Labarina da Dadin Kowa, Manyan Maga da Garwashi.
An bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda daga Litinin 19 zuwa Lahadi 25 ga watan Mayu 2025 domin miƙa fina-finansu don tantancewa da sahalewa.
Wannan na zuwa ne bayan wani taro da aka gudanar tsakanin hukumar da shugabannin masana’antar Kannywood a ranar Litinin.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ce za a duba fina-finan cikin gaskiya da adalci.
Shugaban MOPPAN reshen Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, ya buƙaci mambobin ƙungiyar da su gaggauta miƙa fina-finansu.
A baya, masu shirya fina-finai sun koka cewa ba a basu damar tantance fina-finan kafin dakatarwa.
Hukumar tace fina-finai ta ce matakin na da nufin tsaftace harkar fina-finai a Jihar Kano.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne hukumar da dakatar da haska wasu fina-finai gidajen talabijin da YouTube har sai an tantance su.
Fina-finan da hukumar da ta dakatar tun da farko, sun haɗa da Labarina, Dadin Kowa, Manyan Mata, Garwashi, Jamilun Jidda, da Gidan Sarauta.
Sauran sun haɗa da Dakin Amarya, Mashahuri, Wasiyya, Tawakkaltu, Mijina, Wani Zamani, Mallaka, Kudin Ruwa, Boka Ko Malam, Wayasan Gobe, Rana Dubu, Fatake, Shahadar Nabila, Kishiyata da kuma Rigar Aro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dadin Kowa Garwashi kannywood Labarina Manyan Mata
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar KNARDA Ta Ƙudiri Aniyar Yashe Madatsun Ruwa A Kano
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp