’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 26 a ƙauyukan Zamfara
Published: 19th, May 2025 GMT
Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara.
Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki.
Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200Wani mazaunin yankin ya ce: “Mutane sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa ne da safe.
Ana zargin yaran wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Bello Kaura wanda aka fi sani da Dan Sade ne da kai wannan harin.
Wata majiya ta ce yana da sansani kusa da Sabon Gari.
Wani mazaunin ya ƙara da cewa: “Muna roƙon gwamnati ta kafa sansanin soja a Kungurki.
“Waɗannan ’yan bindiga na kai mana hari duk lokacin da suka ga dama, rayuwarmu tana cikin firgici.”
A wani harin da suka kai, mutum huɗu suka kashe, tare da sace wani mutum ɗaya.
Daga baya, ’yan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa amma suka ƙi barin kowa ya ji muryar wanda suka sace.
Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar da ƙarin goyon bayansa ga hukumomin tsaro tare da ƙaddamar da dakarun sa-kai na Community Protection Guard domin taimakawa wajen kare al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari Sacewa Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
Wakilan kasashen duniya a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna girmamawa ga wadanda suka yi shahada a harin wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Iran
Masu fafutukar wanzar da zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka da wakilan kasashe daban-daban a Majalisar Dinkin Duniya sun gabatar da bayanai kan mutanen da suka yi shahada a hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar kan kasar Iran ta hanyar halartar hedkwatar wakilan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya.
Daruruwan masu fafutukar neman zaman lafiya da masu kiyayya da yaki na Amurka ne suka hallara a hedkwatar tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke birnin New York a ranar Litinin din wannan mako don karrama shahidan harin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta kai kan kasar Iran, inda suka rattaba hannu kan littafin tunawa da nuna juyayi ga gwamnatin Iran da al’ummar kasarta.
Mambobin kungiyar Yahudawa ta kasa da kasa Neturei Karta, kungiyar Yahudawa masu adawa da ‘yan sahayoniyya, su ma sun halarci gangamin tare da nuna girmamawa ga wadanda harin ya rutsa da su.