Iran: Aiwatarda Yarjeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Armenia Da Arzerbaijan Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Kasashen Biyu
Published: 17th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Armenia, Armen Grigoryan wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a yau Asabar.
Ministan ya kara da cewa JMI zata tabbatar da cewa an aiwatar da sulhu tsakanin kasashen biyu da gaggawa saboda tana dasawa da kasashen biyu makobta gareta.
A cikin watan Maris da ya gabata ne kasashen Armenia da Arzerbaijan suka amince a rubuta yarjeniyar sulhu a tsakaninsu a tsakaninsu don kawo karshen rikici a tsakaninsu wanda ya kusan shekaru 40 suna fafatawa a tsakaninsu.
Kasashen biyu sun yi yaki na karshe a tsakaninsu kan mallakar yankin Karabakh a shekara ta 2020 haka ma sun tabka yake-yake a kan malakar yankin a shekaru 1990 da bayansa, har zuwa lokacinda Azerbaijan ta kwace yankin a cikin sa,o,ii a yankin 2020. Sannan Armenia ta sallama mata yankin. Kasashen duniya dai sun amince da cewa yankin na Azerbaijan ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Imanin Iran Da Tattaunawan Zaman Lafiya Amma Ba Za Ta Amince Da Barazana Ba
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba
A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan shirin makamashin nukiliyar Iran cikin karfin gwiwa da mutunta juna, yana mai jaddada wajabcin rashin mika wuya ko mika kai ga duk wata barazana.
Shugaba Pezeshkiyon ya jaddada cewa yin shawarwari ɗaya ne daga cikin ka’idodin hankali da zurfin tunani, amma ba a kan kowane farashi ba. Dole ne a gudanar da shawarwari cikin aminci da mutuntawa tare da bin ka’idojin kasa da kare kima. Iran ta yi imani da tattaunawa da zaman lafiya, amma ba za ta taba mika wuya ga barazana da umarni ba.
Sugaban kasar ya kara da cewa: Ci gaba da kuma cimma manyan buruka na bukatar azama, karfin gwiwa, da kuma sauya yanayin tafiyar da harkokin gudanarwa. Idan wani ya yi niyya don ya cimma manufa amma ya yi kasa a gwiwa a farkon mataki, to ba zai taba cimma burinsa ba.