Me Ya Sa Manchester United Ta Fi Yin Kokari A Europa League?
Published: 17th, May 2025 GMT
A Premier League, kungiyoyi sun gama sanin Man United ciki da waje. “Dalili shi ne su kan hadu sau biyu duk shekara. Sun san abin da za su tarar game da ‘yanwasan United din da kuma filin wasanta, a gasar zakarun Turai kuma, akasari wannan ne karon farko da suke zuwa filin wasa na Old Trafford da kuma karawa da United.
Sai dai ya ce Manchester United dole sai ta yi da gaske a kan kungiyarTottenham saboda duka daga Ingila suka fito kuma sun hadu da su sau uku a wannan kakar duka Tottenham tana samun nasara kuma Tottenham din ta san lagon Manchester United sosai saboda haka komai zai iya faruwa a wasan da za su buga a wannan satin da za mu shiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa.
Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025.
Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a MadinaSP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari.
Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a yanzu haka an soma gudanar da bincike a kan lamarin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin rashin imani na kololuwa.
Ya bai wa al’umma tabbacin cewa za su bi diddigin lamarin domin matashin ya girbi hukunci daidai da abin da ya aikata.
Rundunar ’yan sandan ta bukaci jama’a da su rika gaggauta mika rahoton duk wata alama ta tabin hankali ko cin zarafi domin kaucewa faruwar makamancin wannan lamarin.