HausaTv:
2025-05-18@09:51:40 GMT

Yemen ta sake harba makami mai linzami kan Isra’ila

Published: 18th, May 2025 GMT

Wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yeman ya fada a yankuna Falasdinawa da aka mamaye.

Yemen ta jima da take kai hare-hare kan Isra’ila a matsayin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza dake fuskantar mamaya da ukuba da kisan kare dangi daga Isra’ila.

A cikin bayanin da ya yi bayan harin, babban jami’in gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen Nasr al-Din Amer, ya yi ishara da yadda gwamnatin Isra’ila ta yi watsi da kiran da kasashen Larabawa suka yi na neman zaman lafiya, ya kuma jaddada cewa hare-haren da ke faruwa a yankunan da aka mamaye, shi ne yare daya tilo da gwamnatin Isra’ila ke fahimta.

Hare-haren na Yemen sun yi matukar tasiri wajen durkusar da tattalin arzikin Isra’ila baya ga haifar da tsada sosai ga wasu kayayaki a Isra’ila, yayin da a daya bangaren kuma wasu hare-haren kan tsayar da al’amura a filin jirgin sama na Ben Gurion, mafi mahimmancin ga Isra’ila.

A martanin da ta mayar, Tel Aviv ta kara zafafa hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen.

Sai dai kuma dakarun na Yemen din sun lashi takobin ci gaba da kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, muddin gwamnatin kasar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kisan kiyashi da kuma kara tsananta hare-haren da take kai wa a zirin Gaza.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Fira Ministan Spain: Ba Za Mu Yi Mu’amala Da Isra’ila  Mai Kisan Kiyash

Shugaban hukumar Spain Pedro Sanchez ya bayyana ” Isra’ila” da cewa; “Mai Kisan Kiyashi Ce,” wacce kasarsa ba za yi mu’amala da ita ba.

Fira ministan na kasar Spain ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martnni ga wani dan majalisar kasar daga yankin Catalonia, Gabrel Rovian yana wanda ya tuhume shi da cewa, yana huldar kasuwanci da Isra’ila,alhali tana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi.

Kafafen watsa labarun Spain sun ce wannan shi ne karon farko da firma ministan kasar ya bayyana abinda Isra’ila take yi da cewa kisan kiyasn kare dangi ne.

HKI ta fusata akan furucin da Fira ministan Spain tare da kiran jakadan kasar  domin nuna masa rashin amincewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran : Hare-haren da Isra’ila ta kai kan Yemen babban laifin yaki ne
  • Rokar Kasuwanci Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 6 Zuwa Sararin Samaniya
  • Shuwagabanin Larabawa Sun Yi Alkawalin Sake Gina Gaza, Suna Kuma Kokarin Tsagaita Wuta Da Farko
  • Adadin shahidai a yakin Gaza ya kai 53,119 tun daga Oktoba 2023
  • Isra’ila ta yi barazanar kashe shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen
  •  Fira Ministan Spain: Ba Za Mu Yi Mu’amala Da Isra’ila  Mai Kisan Kiyash
  • Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-hare A Kasar Yemen
  • Sojojin Yemen Suna Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Babban Filin Jirgin Ben Gurion Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Human Rights Watch : Katange Gaza mataki ne na share al’umma