Trump ya ce ya yi tattaunawa mai armashi da Putin
Published: 20th, May 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin na cewa tattaunawar ta yi amfani.
Rasha a shirye take ta yi aiki tare da Ukraine a kan wata yarjejeniya “game da samar da zaman lafiya a nan gaba.”
“Rasha da Ukraine za su fara tattaunawa nan take domin tsagaita bude wuta,” in ji Trump.
A cewar wata majiya kusa da tattaunawar da ke gudana, shugaban fadar White House ya tuntubi Volodymyr Zelensky “na ‘yan mintoci kadan” kafin kiran Putin.
“Daidaita” dangantaka, musayar fursunoni, Iran da Gabas ta Tsakiya na daga cikin batutuwan da aka tattauna.
Mr. Putin ya yaba da shawarwarin da ake yi tsakanin Washington da Tehran kan shirin nukiliyar Iran da aka faro ta hanyar shiga tsakani na Oman.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Kwana 60 Da Hamas – Trump
“Ba za su samu tayin da ya fi wannan ba abu zai ƙara muni idan suka ƙi.”
Har yanzu babu martani daga jami’an Isra’ila kan iƙirarin Trump ba.
Tattaunawar neman tsagaita wuta ta tsaya cak tun watanni da suka gabata saboda rashin jituwa kan matakin da za a ɗauka bayan an daina faɗa.
Isra’ila tana son ta ci gaba da samun damar kai farmaki idan ta ga dama, amma Hamas tana so a daina faɗa gaba ɗaya.
Ana sa ran Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai kai ziyara fadar White House a mako mai zuwa.
Trump ya ce zai yi magana da Netanyahu domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin.
A farkon shekarar nan, wani ƙoƙari na tsagaita wuta ya rushe a watan Maris bayan Isra’ila ta kai wani farmaki ba tare da sanarwa ba a Gaza wanda rahotanni suka ce ya hallaka fiye da mutane 300.
Daga baya Netanyahu ya kare farmakin, inda ya bayyana cewa Hamas ta ƙi sakin fursunon Isra’ila da ke hannunta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp