Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Hanyar Warware Takaddamar Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Published: 30th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Hanyar cimma yarjejeniya ta ta’allaka ne ta kan teburin tattaunawa, ba ta hanyar kafafen yada labarai ba.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya fada a jiya Alhamis cewa: Kafafen yada labarai na yada jita-jita game da yarjejeniyar da ake shirin kullawa tsakanin Iran da Amurka.
Araqchi ya ci gaba da yin tsokaci a shafinsa na Twitter a dandalin Twitter, inda ya ce: “Muna shakkar cewa an kai wannan matakin.”
Ya kara da cewa: “Hanyar yarjejeniya tana bi ta kan teburin tattaunawa ne, ba ta hanyar kafafen yada labarai ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA