Gasar Wasanni Ta Kasa Wata Hanya Ce Ta Hada Kan Matasan Nijeriya– Obasanjo
Published: 30th, May 2025 GMT
“Ina isar da wannan sakon ba wai a matsayina na tsohon shugaban kasa ba, har ma a matsayina na dan jihar Ogun cike da alfahari, na kasance tare da ku a lokacin bikin bude gasar, na kalli wasannin a cikin dakina, kuma hakika wasannin sun nuna cewa ba wai kawai wasanni ba ne, alama ce ta hadin kai, baje kolin hazaka, da kuma kishin kasa.
“Daga karshe Obasanjo ya jinjinawa jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya, da kuma kananan kungiyoyin da aka gayyata bisa jajircewarsu, inda ya kara da cewa, kwamitocin da suka shirya gasar, abokan hadin gwiwa, da masu aikin sa kai na hukumar wasanni ta kasa sun cancanci a yaba musu saboda mayar da wannan mafarkin da ya zama gaskiya.” In ji Obasanjo
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Bikin BIRTV2025 A Beijing
Yau Laraba, aka kaddamar da bikin nune-nunen harkokin rediyo da fina-finai da talabijin na kasa da kasa na Beijing karo na 32 ko kuma BIRTV2025 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wanda kamfanin CBIC na kasar Sin ya dauki nauyin shiryawa, bisa jagorancin babbar hukumar kula da harkokin rediyo da talabijin ta kasa gami da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasa wato CMG.
Bikin na BIRTV2025 yana kokarin kafa wata gada don inganta mu’amala tsakanin kasa da kasa ta hanyar gudanar da harkokin kasa da kasa, ciki har da taron sanin makamar aiki don inganta kwarewar kafafen yada labaran Sin da Afirka, wanda zai mayar da hankali kan irin labaran da suka kamata a watsa, gami da hanyoyin watsa su, tare kuma da lalubo sabbin hanyoyin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin masana’antun talabijin da rediyo.
Bikin BIRTV2025 na bana wanda za’a rufe shi a ranar 26 ga wata, ya samu halartar kamfanoni sama da 500 daga kasashe da yankuna fiye da 20, wadanda suke nuna sabbin nasarori da fasahohin da suke da su a sana’o’in da suka shafi rediyo da fina-finai da talabijin da kuma intanet. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp