HausaTv:
2025-05-29@17:20:47 GMT

HKI Ta Kai Sabbin Hare-Hare Kan Tashar Jiragen Sama Na Birnin San’a

Published: 28th, May 2025 GMT

Majiyoyin labarai a kasar Yemen sun bayyana cewa HKI ta kai hare-hare a kan tashar Jiragen sama a birnin San’aa inda a wannan karon suka lalata hanyar tashin jiragen sama a tashar.

Tashar talabijan ta Al-manar ta kasar Lebanon ta kanalto majiyar HKI tana tabbatar da wannan labarin.

Tashar radio ta HKI ta nakalto ministan yakin HKI Yasra’il Katz yana tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hare-haren ta sama sun wargaza wani bangare na tashar jiragen sama na birnin, sannan ya lalata jirgin sama tilo wanda ya rage a tasahr jiragen.

Hakama tasha ta 12 ta HKI ta nakalto Katz yana cewa jiragen yaki fiye da 10 ne suka yi aikin hare-hare a kan tashar jirage na Sa’aa.

Kafin haka dai sojojin kasar Yemen a jiya Talata ma sun cilla makamai masu linzami samfurin Bilistic zuwa kan  tashar jiragen sama na Bengerion don tallafawa mutanen Gaza wadanda HKI take kashewa da yunwa da kuma wuta ta ko ina.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: tashar jiragen sama

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Ta Kammala Samar Da Fasfo Sama Da 200,000 Da Suka Yi Jinkiri

Kan batun gyaran gidajen yari kuwa, ministan ya nuna damuwa kan halin da gidan gyaran hali ke ciki, inda ya bayyana cewa fiye da fursunoni 4,000 na tsare ne saboda gazawarsu na biyan tara kamar Naira 50,000.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja
  •  Yemen: Wuce Gona Da Irin HKI Ba Zai Sauya Mana Ra’ayi Akan Ci Gaba Da Taimaka Wa Gaza Ba
  • Hadin Gwiwar Sin Da Yankin Turai Na Kara Kawo Haske Ga Tattalin Arzikin Duniya
  • Babu Wata Sauran Mafaka Ga ‘Yan Ta’adda, In Ji Shugaban Rundunar Sojin Sama
  • Gaza : EU ba ta gamsu da sabon tsarin raba agaji na Amurka da Isra’ila ba  
  • Gwamna Uba Sani Ya Kammala Titin Unguwar Su El-Rufai
  • Gwamnati Ta Kammala Samar Da Fasfo Sama Da 200,000 Da Suka Yi Jinkiri
  • Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Wa Yankunan Gaza Hare-hare
  • Tare Da Taimakon Kasar China Za A Bude Masana’antun  Sarrafa Sanadarin Lithium A Nigerria