Kudin Shigar Masana’antar Manhajojin Sin Ya Karu Da 10.8% A Watanni Hudu Na Farkon Bana
Published: 30th, May 2025 GMT
Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar, sun nuna daga watan Janairu zuwa watan Afirilun bana, masana’antun samar da manhajoji da ayyukan ba da hidimomin fasahohin sadarwa na Sin sun bunkasa lami lafiya.
Alkaluman sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Afrilun bana, jimillar kudin shiga da masana’antar ta samu, ta haura yuan tiriliyan 4.
Har ila yau, jimillar kudin shigar masana’antun fitar da kayayyakin manhajojin ta kai dalar Amurka biliyan 17.26, adadin da ya karu da kashi 3.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Samar Da Karin Guraben Aikin Yi Miliyan 6.95 A Rabin Farko Na Bana
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara.
Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a yau Talata, inda ya ce a watan Yuni, yawan wadanda ba su da aiki a birane ya tsaya kan kaso 5 bisa dari, watau bai sauya ba daga yadda ya kasance shekara 1 da ya wuce.
Kasar Sin na da burin adadin marasa aikin yi ya tsaya kan kaso 5.5 a bana, tare da burin samar da guraben aikin yi sama da miliyan 12. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp