Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Gana Da Ministan Cikin Gida Da Gwamnonim Lardunan Iran
Published: 29th, May 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya gana da ministan harkokin cikin gida da kuma gwamnonin Larduna, inda ya basu shawarar amfanin da kekyawar yanayin da kasar take ciki don ciyar da kasar Gaba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana cewa, a halin yanzu kasar Iran bata fuskantan watai annoba kamar CoviD19, ko matsalar tsaro a cikin gida da sauran wanda zai hanasu aiki.
Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa kasar Iran a halin yanzu bata fuskantar wata matsala, don haka ya bukaci Gwamnonin lardun su yi amfani da wannan damar don amfani da matasan kasar wadanda suka yi karatu don bukasa tattalin arzikin kasar tare da amfani da dimbin arzikin da All..ya horewa kasar.
Kafin haka dai ministan harkokin cikin gida Eskandar Mumini ya gabatar da jawabi inda yake halin da ake cikin a ayyukan ci gaban da gwamnonin suke yi a duk fadin kasar ya kuma bayyana ire-iren ci gaban da aka samu.
Jagoran a wani wuri ya fadawa gwamnonin kan cewa suna iya amfani da kungiyoyin raya kasashen wadanda Iran take da su don kalla yarjeniyoyi da wadannan kasashen saboda ci gaban kasar Iran. Yace kungiyoyi kamar shanhai, da ECO da sauran su zasu iya taimakawa don kawo ci gaban tattalin arzikin kasar.
Sannan daga karshe jagoran ya bukaci gwamnanin su rika ciga mutane suka tambayansu matsaloli duk da cewa wani lokacin sukan hadu da wadanda zasu fada masu maganganu marasa dadi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Iya Samun Masu Samar Da Kayayyaki Iri-Iri Cikin Awa Daya A Kasar Sin
“Ba kawai girma tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin yake da shi ba, har ma ya hade dukkanin fannoni, tare da amsawa da sauri kwarai da gaske.”
“Daga kulla kwangila zuwa samun wurin gudanarwar ayyuka bai wuce watanni 3 ba, lamarin da ya ba mu mamaki sosai!”
A ranar 20 ga wata, an rufe bikin baje kolin samar da kayayyaki na kasa da kasa karo na uku a birnin Beijing. A yayin bikin na wannan karo, kamfanonin kasashen ketare da suka hada da Honeywell, da Louis Dreyfus, da Corning, da kuma Wacker Chemie AG da dai sauransu, sun jinjinawa tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin mai inganci. Sun ce, za su ci gaba da raya ayyukansu a kasar Sin, tare da hada kai da kasar Sin da ma sauran baki ’yan kasuwa wajen kyautata tsarin samar da kayayyaki na duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp