Kokarin Minista Tuggar Na Mayar Da Hijirar Masana Daga Nijeriya Zuwa Kasashen Waje Alhairi
Published: 31st, May 2025 GMT
Wannan shi ne babban abin alfahari da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ke jagoranta. A yayin tattaunawar manyan jami’an biyu a Berlin tare da ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul, Tuggar ya nuna bajinta. “Ba manufar Nijeriya bace ta fitar da mutane zuwa wasu kasashen waje ba, sai don nuna gwanayenta,” in ji shi, tare da sake sanya haske a manufinta.
A cikin shekarun baya-bayan nan, yawan al’ummar Nijeriya sun kasance ana sanya su a matsayin wadanda ke cikin rikici, miliyoyin matasa marasa aikin yi, masu karatun digiri, da kwararru an nuna musu halin ko-in-kula.
Amma Tuggar, gogaggen jami’in diflomasiyya kuma mai tunani na Afirka, yana ganin abin da mutane da yawa ke watsi da shi dama ce. Ana ganin sama da mutum miliyan 220 da muke da su a yau ana hasashen za su kai miliyan 400 nan da shekarar 2050, don haka Nijeriya ba kawai mai daukar nauyin al’umma bace, ita ce ma’adanin jari-hujja baki daya.
Sabanin haka, Jamus da yawancin Tarayyar Turai suna tsufa da wuri. Tattalin arzikinsu na karuwa, amma yawansu yana raguwa
Kwararrun ma’aikata suna cikin karancin wadata. Vangaren kiwon lafiya ya tabarbare. Masana’antu suna bukatar a karfafe su da kwarewar dijital.
To a nan akwa al’amari mai ban sha’awa: Nijeriya na da hazaka. Turai kuma na da bukata. Amma maimakon a yi asarar wannan wannan hadin gwiwa ta hanyar yanke kauna da yin hijira ba bisa ka’ida ba, Tuggar ya ba da shawarar yin doka, da tsarin hadin gwiwa, wacce za a rika yin hijrar akan tsari.
Wadephul, a nasa bangaren, wannan shawara ba wai ta kasance karbabbiya bace, ai bayan haka abar sha’ace a bayyane
A nasa jawabin, ya jaddada ingancin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Jamus a fannonin da suka hada da kasuwanci zuwa makamashi, da kuma yadda ake tafiyar da ayyuka na hazaka. “Akwai manyan damammaki a hadin gwiwa cikin ma’adanai masu mahimmanci, canjin makamashi, da hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu,” in ji shi.
Jamus ba ta sanya Nijeriya cikin masu ba da taimako ga masu karba, ko mai taimako ga marasa galihu. Madadin haka, wannan hadin gwiwa ne da zai zama na masu daidaita kasashen da za su daidata bukatun juna da mutunta juna. Tuggar da Wadephul sun binciko hanyoyin zurfafa alaka ta hanyar koyar da sana’o’i, inganta kwarewa, da kirkirar hanyoyin kaura da ke mutunta ikon mallaka da samun dama.
Hadin gwiwar makamashi tsakanin Jamus da Nijeriya, wanda aka fara a 2008 kuma aka karfafa shi a 2021 tare da kafa ofishin hydrogen a Abuja, wani abin koyi ne na yadda kasashen biyu za su iya samar da darajar kayan. Yanzu dai, makasudin yin haka shi ne a sake dawo da irin wannan hadin gwiwa, karfafawa matasa, da sanya hannun jari na kasashen biyu.
A cikin manufofin waje na Tuggar, ba gwaninta bace a rika fita da kaya ta hanyar bazata ba, domin kadara ta kasa. Ya fahimci cewa idan kaura ba ta da tsari, to lallai kasashe sun yi hasara. Amma idan aka yi da kyakkwar niyya kuma ana yin mubaya’a, al’ummomi kasashe za su shigo ciki.
’Yan Najeriya kwararrun da ke aiki a Berlin, Hamburg, Munich, ko Frankfurt ba wai kawai suna cike gibin aiki bane, suna gina gadoji na kasashen waje, aika kudi, samun sabbin kwarewa, da fadada darajar Nijeriya a duniya.
Wannan ba maganar hijira ba ce kawai; wannan shi ne dabarun diflomasiyya.
Wannan tsarin ya kalubalanci ra’ayin da aka dade ana yi wanda Afirka ba ta da wani abin da za ta iya bayarwa. Akasin haka, Afirka, da Nijeriya musamman a shirye suke domin kerawa gami da ba wa duniya abin da ba ta da shi ko take rasawa.
Ayyukan Tuggar a Berlin sun fi ba da fifiko kan kiraye-kirayen girmamawa na bangarorin biyu, da suka kasance wani bangare na hangen nesa wajen sake mayar da Nijeriya a matsayin mai kwarin gwiwa, mai kwarewa wajen taka muhimmiyar rawa a fagen duniya. Har ila yau ya gana da ‘yan majalisar dokokin Jamus, da manyan jami’an raya kasa, da Farfesa Lanz Rolla, wanda shi ne mai hangen nesan da ya kafa taron tattaunawa na duniya na Berlin.
Dangane da jagorancinsa da kuma yadda Nijeriya ke tasowa, an gayyaci Tuggar a hukumance don yin jawabi a taron 2025 na Tattaunawar Duniya ta Berlin. Wannan gayyata kakkarfar alama ce.
Kuma hakan ya tabbatar da rawar da Nijeriya ta taka wajen tsara tattaunawar duniya game da mulki, da dorewa, da kuma yin hijira.
Shekaru da yawa, an yi magana game da Afirka a cikin da’irar duniya. Tuggar yana son Nijeriya ta kasance daya daga cikin masu fada a ji kuma masu jagoranci.
Lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya a gida da waje za su daina kallon hijira a matsayin abin takaici. Ba koyaushe ne hijrar take zama tsrewa ake ba,. Wani lokaci, ana ficewa ne domin fadada ilimi. Wani lokaci, masu hijrar ba batu ne na watsar da kasarsu ba, a’a suna fita ne domin ciyar da ita kasar gaba.
Dole ne mu gina tsarin da zai ba matasa ‘yan Nijeriya kayan aiki ba kawai don yin gasa a duniya ba sai don yin nasara da alfahari, daukar su tare da girmamawa, da kuma danganta nasarar kansu ga ci gaban kasa.
Dan Nijeriya mazaunin kasar waje ai ba zama dan kasa ba. Kadara ce kawai ta ketare.
Don yin wannan aikin, dole ne gwamnati ta saka hannun jari a fannin ilimi, fasahar dijital, da horar da sana’o’i. Dole ne kuma ta sake fasalin ayyukan diflomasiyya don tallafa wa hanyoyin kaura na doka da kuma kare ‘yan kasa a kasashen waje daga cin zarafi da nuna wariya.
Amma bayan gwamnati, dole ne kowane dan Najeriya ya sake gyara tunaninsa. “Japa” ba shi ne abin kunya ba. A hannun shugabanni masu hangen nesa kamar Tuggar, ya zama dabara dabara ta hawa abin hawa mai mahimmanci ga kasa.
Kada mu yi la’akari da bin hanya daya. Mu horar da ingantattun tunani, mu samar da ginshikai masu karfi, domin gina Nijeriya a duniya wanda zai amfanar da kowa.
Nijeriya ba ta yi asarar mutanenta ba. Tana amfanuwa ta karkashin kasa.
Kuma yayin da wannan sabon babi ya bayyana-mai tushe cikin mutunci, da tsarin diflomasiyya – har yanzu muna iya gano cewa jiragen da a da suka kwashe mafarkinmu suna dawowa, ba kawai tare da fasinjoji ba, har ma da kyakkyawar manufa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tuggar kasashen waje hadin gwiwa da Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana cewa aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, a karshen kogin Yarlung Zangbo, aiki ne dake bisa ikon mallakar kasar Sin, kuma Sin din tana raya aikin don gaggauta samar da makamashi mai tsabta, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wurin, da kuma tinkarar sauyin yanayi.
Guo ya ce, kasar Sin ta mai da hankali, da sauke nauyin dake wuyanta na amfani da albarkatun kogin da ya ratsa bangarenta da ma kasashen waje, kana tana da fasahohin gina tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa. An tsara aikin ne a kan karshen kogin Yarlung Zangbo bisa ma’aunin Sin mai nasaba da aiki, da gudanar da aikin tare da kiyaye muhalli, da magance aikin a muhimman wuraren halittu don tabbatar da tsarin yanayin wanzuwar halittu. An gina tashar don magance bala’i a kan kogin, ta yadda aikin ba zai yi wata illa ga yankin karshen kogin ba.
Guo Jiakun ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashen dake kan karshen kogin a fannonin sanar da yanayin kogin, da magance bala’i, da yaki da bala’i da sauransu, da kuma yin mu’amala da kasashen don ci gaba da yin hadin gwiwa da su, da kuma kawo moriya ga jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp